Titu 2 – CRO & HCB

Knijga O Kristu

Titu 2:1-15

Promicati zdravo učenje

1Ali ti poučavaj životu koji je u skladu sa zdravim učenjem. 2Pouči starije muškarce da budu trijezni i razboriti te zdravi u vjeri, ljubavi i strpljivosti.

3Pouči starije žene da se ponašaju pobožno i predano. Ne smiju ogovarati i neka ne robuju prevelikom vinu. Radije neka budu učiteljice dobra. 4Neka odgajaju mlađe žene da žive mirno, da ljube svoje muževe i djecu, 5da budu razborite i čista srca, da marljivo rade u svojim domovima, da budu dobre i poslušne muževima kako drugi zbog njih ne bi vrijeđali Božju riječ.

6Mladiće također potiči da budu razumni. 7Sam im budi uzor čineći dobra djela. Poučavaj zdravo i ozbiljno. 8Neka ti učenje bude tako zdravo da se tvoji protivnici posrame jer nemaju što loše reći.

9Robovi se u svemu moraju pokoravati svojim gospodarima i truditi se da im ugode. Ne smiju im proturječiti 10niti ih potkradati, nego se moraju pokazati pouzdanima. Tako će učenje o Bogu, našem Spasitelju, učiniti privlačnim u svakom pogledu.

11Objavljena je Božja milost koja donosi spasenje svim ljudima. 12Odgojila nas je da se odreknemo bezbožnog života i grešnih svjetovnih požuda te da u ovome svijetu živimo uzdržljivo, pravedno i pobožno 13iščekujući blaženu nadu: da se veliki Bog, naš Spasitelj Isus Krist, pojavi u slavi. 14On je dao sebe umjesto nas da nas oslobodi od svakoga grijeha, da nas očisti i da budemo njegov izabrani narod koji revno čini dobra djela.

15To poučavaj i opominji ljude da tako čine. Kori ih kad je to potrebno jer imaš tu vlast. Nemoj da te tko prezire!

Hausa Contemporary Bible

Titus 2:1-15

Abin da ya kamata a koyarwa wa ƙungiyoyi dabam-dabam

1Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa. 2Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri.

3Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. 4Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu, 5su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah.

6Haka kuma, ka ƙarfafa samari su zama masu kamunkai. 7Cikin kowane abu ka zama musu misali mai kyau ta wurin aikata abin da yake nagari. A cikin koyarwarka ka nuna mutunci da ƙwazo 8da kuma sahihanci cikin maganar da ba za a iya kushewa ba, domin masu gāba da kai su ji kunya, su kuma rasa wani mugun abin da za su faɗa game da mu.

9Ka koya wa bayi su yi wa iyayengijinsu biyayya cikin kowane abu, su yi ƙoƙari su gamshe su, kada su mayar musu da magana, 10kada kuma su yi musu sata, sai dai su nuna za a iya amince da su sosai, don ta kowace hanya su sa koyarwa game da Allah Mai Cetonmu ta zama abin ɗaukan hankali.

11Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane. 12Yana koya mana mu ce, “A’a” ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani, 13yayinda muke sauraron begenmu mai albarka bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi, 14wanda ya ba da kansa dominmu don yă fanshe mu daga dukan mugunta yă kuma tsarkake wa kansa mutanen da suke nasa, waɗanda suke marmarin yin abin da yake nagari.

15Waɗannan kam, su ne abubuwan da ya kamata ka koyar, ka ƙarfafa ka kuma tsawata da dukan iko. Kada ka yarda wani yă rena ka.