約翰一書 5 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

約翰一書 5:1-21

勝過世界的人

1每一個信耶穌是基督的人,都是從上帝生的。凡愛生他之上帝的,也愛上帝所生的。 2當我們愛上帝,遵行祂的命令時,便知道自己也愛祂的兒女。 3因為我們遵行上帝的命令就是愛上帝,祂的命令並不難遵守。 4因為凡是從上帝生的人都能勝過世界,使我們得勝的是我們的信心。 5誰能勝過世界呢?不就是那些信耶穌是上帝的兒子的人嗎?

上帝的見證

6耶穌基督是藉著水和血來的。祂不單是藉著水來的,也是藉著水和血來的,並且有聖靈為祂做見證,聖靈就是真理。 7這樣,做見證的共有三樣: 8聖靈、水和血。這三者是一致的。 9我們既然接受人的見證,就更該接受上帝的見證,因為上帝為祂的兒子作了見證。 10信上帝兒子的人心裡有這見證,不信上帝的人等於把上帝當作撒謊的,因為他不信上帝為祂兒子做的見證。 11這見證就是:上帝已經把永恆的生命賜給我們,這生命在祂兒子裡面。 12人有上帝的兒子,就有這生命;沒有上帝的兒子,就沒有這生命。

永恆的生命

13我把這些事寫給你們這些信上帝兒子之名的人,是要你們知道自己有永生。 14我們若按著上帝的旨意祈求,祂必垂聽,這是我們對上帝的信心。 15我們既然知道上帝垂聽我們一切的祈求,就知道我們能得到所求的。

16若有人看見信徒犯了不至於死的罪,就當為他禱告,上帝必將生命賜給他。有的罪會導致死亡,我並不是說你們要為這樣的罪禱告。 17一切不義的事都是罪,但有的罪不會導致死亡。

18我們知道從上帝生的不會繼續犯罪,因為上帝的兒子保護他,那惡者無法害他。 19我們知道自己屬於上帝,全世界都在那惡者手中。

20我們知道上帝的兒子已經來了,並且賜給了我們悟性,使我們能認識真神。我們在真神裡面,就是在祂兒子耶穌基督裡面。祂是真神,也是永生。

21孩子們啊,你們要遠離偶像!

Hausa Contemporary Bible

1 Yohanna 5:1-21

Bangaskiya cikin Ɗan Allah

1Kowa ya gaskata cewa Yesu shi ne Kiristi, shi haifaffe na Allah ne, kuma duk mai ƙaunar mahaifi kuwa, yakan ƙaunaci ɗansa ma. 2Ga yadda muka san cewa muna ƙaunar ’ya’yan Allah. Muna yin haka ta wurin ƙaunar Allah da kuma aikata umarnansa. 3Ƙaunar Allah ita ce, a yi biyayya da umarnansa. Umarnansa kuwa ba masu nauyi ba ne; 4domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya. 5Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.

6Ga wanda ya zo ta wurin ruwa da jini, wato, Yesu Kiristi. Bai zo ta wurin ruwa kaɗai ba, sai dai ta wurin ruwa da kuma jini. Ruhu ne kuwa yake ba da shaida, gama Ruhu shi ne gaskiya. 7Akwai shaidu uku, wato, 8Ruhu,5.7,8 Rubuce-rubucen hannu na baya-bayan nan na Bulget shaida a sama: Uba, Kalma da kuma Ruhu Mai Tsarki, waɗannan uku kuwa ɗaya ne. 8 Akwai kuma uku da suka ba da shaida a duniya, wannan: Ruhu (babu kalman nan a rubuce-rubucen hannu na Girik kafin karni na goma sha shida) da ruwa, da kuma jini; waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce. 9Tun da yake mukan yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa. 10Duk wanda ya gaskata da Ɗan Allah, yana da shaidan nan a zuciyarsa. Duk wanda bai gaskata da Allah ba kuwa ya mai da shi maƙaryaci, domin bai gaskata shaidar da Allah ya bayar game da Ɗansa ba. 11Wannan kuwa ita ce shaidar; cewa Allah ya ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa. 12Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai; wanda kuwa ba shi da Ɗan Allah, ba shi da rai.

Ƙarshen magana

13Ina rubuta waɗannan abubuwa gare ku, ku da kuka gaskata sunan Ɗan Allah domin ku san kuna da rai madawwami. 14Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi sa’ad da muke zuwa a gaban Allah, gama mun san cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu. 15In kuwa muka san cewa yana sauraranmu, ko mene ne muka roƙa, mun sani, mun riga mun sami abin da muka roƙa daga gare shi ke nan.

16Kowa ya ga ɗan’uwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai yă yi masa addu’a. Ta dalilin mai addu’an nan kuwa, Allah zai ba da rai ga mai yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yakan kai ga mutuwa. Ban ce a yi addu’a domin wannan ba. 17Duk rashin adalci, zunubi ne, amma akwai waɗansu zunuban da ba sa kai ga mutuwa.

18Mun san cewa kowane haifaffe na Allah ba ya cin gaba da yin zunubi; kasancewarsa haifaffe na Allah ita takan kāre shi, mugun kuwa ba zai iya cuce shi ba. 19Mun san cewa mu ’ya’yan Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun. 20Mun san cewa Ɗan Allah ya zo duniya, ya kuma ba mu ganewa domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna cikinsa, shi da yake Allah na gaskiya wato, cikin Ɗansa Yesu Kiristi. Shi ne Allah na gaskiya da kuma rai na har abada.

21’Ya’yana ƙaunatattu, ku yi nesa da gumaka.