提摩太後書 1 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

提摩太後書 1:1-18

1保羅奉上帝的旨意,按照在基督耶穌裡所應許的生命作基督耶穌的使徒, 2寫信給我親愛的兒子提摩太

願父上帝和我們的主基督耶穌的恩典、憐憫和平安臨到你!

勉勵忠心事奉

3我日夜不停地為你禱告,對我效法祖先用清潔的良心事奉的上帝充滿了感恩。 4每逢想起你流淚的情形,我就渴望見你,好使我的心充滿喜樂。 5我記得你那真誠無偽的信心。你外祖母羅以和你母親友妮基首先有了這信心,我深信你也有。 6因此我提醒你,要把上帝在我把手按在你身上時賜給你的恩賜充分發揮出來。 7因為上帝賜給我們的不是懦弱的心,而是剛強、仁愛、自律的心。

8所以,你不要羞於為我們的主做見證,也不要以我這為主被囚的人為恥,要靠著上帝的能力和我一同為福音受苦。 9上帝拯救了我們,並呼召我們過聖潔的生活,不是因為我們的行為,而是出於祂的旨意和恩典。早在萬古以前,祂就在基督耶穌裡把這恩典賜給我們了, 10如今藉著我們救主基督耶穌的降世顯明了出來。基督已經消滅了死亡,藉著福音將不朽的生命彰顯了出來。

11我為了這福音受委派做傳道人、使徒和教師。 12我因此而遭受這些苦難,但我不以為恥,因為我知道我所信的是誰,也深信祂能保守祂所託付我的1·12 祂所託付我的」又可翻譯為「我所信託祂的」。,一直到那日1·12 那日」指保羅站在基督面前交帳的日子。13你要以在基督耶穌裡的信心和愛心,把從我這裡聽到的正確教導當作典範遵守, 14要靠著住在我們裡面的聖靈牢牢守住交託給你的美善之道。

15你知道幾乎所有亞細亞的人都離棄了我,其中包括腓吉路黑摩其尼16願主憐憫阿尼色弗一家人,他常常鼓勵我,不以我被囚禁為恥。 17他在羅馬的時候千方百計尋訪我的下落,直到找著我為止。 18你很清楚,他從前在以弗所怎樣在各個方面服侍我。願主再來時格外地憐憫他。

Hausa Contemporary Bible

2 Timoti 1:1-18

1Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, bisa ga alkawarin rai wanda yake cikin Kiristi Yesu,

2Zuwa ga Timoti, ƙaunataccen ɗana.

Alheri, jinƙai da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai.

Godiya

3Na gode wa Allah wanda nake bauta wa, kamar yadda kakanni-kakannina suka yi da lamiri mai tsabta, yadda kullum dare da rana ina tuna da ku a cikin addu’o’ina. 4Sa’ad da na tuna da hawayenka, nakan yi marmarin ganinka, don in cika da farin ciki. 5An tunashe ni da sahihiyar bangaskiyarka, wadda a farko ta kasance a cikin kakarka Loyis da kuma mahaifiyarka Yunis yanzu kuwa na tabbata tana cikinka.

Ƙarfafawa don zaman aminci

6Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwan nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗibiya maka hannuwana. 7Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai. 8Saboda haka kada ka ji kunyar ba da shaida game da Ubangijinmu, ko kuwa ka ji kunyata, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi. Sai dai ka haɗa kai tare da ni cikin shan wahala saboda bishara ta wurin ikon Allah, 9wanda ya cece mu ya kuma kira mu ga rayuwar tsarki ba saboda wani abin da muka yi ba sai dai saboda nufinsa da kuma alherinsa. An ba mu wannan alheri cikin Kiristi Yesu tun fil azal, 10amma yanzu an bayyana ta ta wurin bayyanuwar Mai Cetonmu, Kiristi Yesu, wanda ya hallaka mutuwa ya kuma kawo rai da rashin mutuwa a sarari ta wurin bishara. 11A wannan bishara ce, aka naɗa ni mai shela da manzo da kuma malami. 12Shi ya sa nake shan wahalar da nake sha. Duk da haka ba na jin kunya, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata cewa yana iya kiyaye abin da na danƙa masa1.12 Ko kuwa abin da aka danƙa mini amana don wancan rana.

13Abin da ka ji daga gare ni, ka kiyaye shi kamar tsarin sahihiyar koyarwa, cikin bangaskiya da ƙauna cikin Kiristi Yesu. 14Ka kiyaye kyakkyawar ajiyan nan da aka danƙa maka amana, ka lura da ita da taimakon Ruhu Mai Tsarki wanda yake raye a cikinmu.

15Ka san cewa kowa a lardin Asiya ya juya mini baya, har da Figelus da Hermogenes.

16Bari Ubangiji yă yi wa iyalin Onesiforus jinƙai, domin sau da dama yakan wartsakar da ni, bai kuma ji kunyar sarƙoƙina ba. 17A maimakon haka ma, sa’ad da yake a Roma, ya neme ni ido a rufe sai da ya same ni. 18Bari Ubangiji yă sa yă sami jinƙai daga Ubangiji a wancan ranar! Ka sani sarai yadda ya taimake ni a hanyoyi dabam-dabam a Afisa.