希伯來書 10 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

希伯來書 10:1-39

永遠的贖罪祭

1律法只是將來美事的一個投影,並非本體的真像,所以年復一年的獻祭不能使前來敬拜的人純全。 2否則,獻祭的事早已終止了,因為敬拜的人若獻一次祭就能徹底得到潔淨,他們就不再覺得有罪了。 3然而,每年獻祭的事都使人想起自己的罪來, 4因為公牛和山羊的血根本不能除去人的罪。

5所以,基督來到世上的時候曾說:

「上帝啊,祭物和供物非你所悅,

你為我預備了身體。

6你並非喜愛燔祭和贖罪祭。

7於是我說,

『上帝啊,我來是要遵行你的旨意,

我的事都記在聖經上了。』」

8基督首先說:「祭物、供物、燔祭和贖罪祭都不是你想要的,也不是你喜悅的。」這些都是依照律法獻上的。 9然後祂又說:「我來是要遵行你的旨意。」這樣,祂廢除了前者,為要設立後者。 10上帝的旨意是:耶穌基督只一次獻上自己的身體,便使我們永遠聖潔了。

11祭司都要天天站著供職,一次次地獻上同樣的祭物,只是這些祭物根本不能除罪。 12而基督一次獻上自己成為永遠的贖罪祭後,就坐在上帝的右邊, 13等待祂的仇敵成為祂的腳凳。 14祂憑自己的一次犧牲,使那些得以聖潔的人永遠純全。

15聖靈也向我們做見證,說:

16「主說,那些日子以後,

我將與他們立這樣的約,

我要把我的律例放在他們心中,

寫在他們腦中。

17我要忘記他們的過犯和罪惡。」

18既然過犯和罪惡已經得到赦免,就不需要再為罪獻祭了。

堅忍到底

19-20弟兄姊妹,耶穌已用寶血為我們開闢了一條又新又活的路,使我們可以穿過幔子,就是祂的身體,坦然進入至聖所。 21並且,我們有一位大祭司管理上帝的家, 22祂潔淨了我們被罪困擾的良心,用清水洗淨了我們的身體。因此,我們要信心十足、真誠地到上帝面前。 23我們要堅定不移地持守我們所認定的盼望,因為賜應許的那位是信實的。 24我們要想辦法彼此相顧,激發愛心,勉勵行善。 25不要停止聚會,像那些停止慣了的人,要互相鼓勵,特別是你們知道主再來的日子近了。

26因為我們知道了真理以後,若仍然故意犯罪,就再沒有贖罪祭了, 27只有可怕的審判和燒滅敵對者的烈火等候我們。 28人違犯摩西的律法,經兩三個人指證後,尚且被毫不留情地處死, 29更何況人踐踏上帝的兒子,輕看那使人聖潔的立約之血,又藐視賜人恩典的聖靈?這等人該受多麼重的刑罰啊! 30我們知道上帝說過:「伸冤在我,我必報應。」祂又說:「主要審判祂的百姓。」 31落在永活上帝的手中是可怕的!

32你們要回想當初的日子,那時你們蒙了光照以後,忍受了各種苦難的煎熬。 33有時候,你們在眾目睽睽之下被辱駡,受迫害;有時候,你們和遭受這樣苦難的人同舟共濟。 34你們體恤那些坐牢的人,即使你們的家業被搶奪,仍然甘心忍受,因為你們知道自己有更美的、永遠長存的家業。 35所以切勿失去勇敢的心,因為勇敢的心會給你們帶來大賞賜。 36你們需要堅忍到底,這樣你們遵行了上帝的旨意後,便可以得到祂的應許。

37因爲「將要來臨的那位很快要來了,絕不遲延。 38屬我的義人必靠信心而活。他若畏縮退後,我必不喜悅他。」 39但我們都不是退後走向滅亡的人,而是因為有信心而靈魂得救的人。

Hausa Contemporary Bible

Ibraniyawa 10:1-39

Hadayar Kiristi sau ɗaya tak

1Dokar, inuwa ce kawai ta kyawawan abubuwa masu zuwa, wannan inuwar ba ita ce ainihin abubuwan ba ne. Saboda haka ba za tă taɓa mai da masu matsowa kusa don yin sujada cikakku ta wurin irin hadayun da ake maimaitawa ba fasawa shekara-shekara ba. 2Da a ce za tă iya, da ba su daina miƙa hadayu ba? Ai, da an riga an tsabtacce masu yin sujada sau ɗaya tak, da kuma ba za su ƙara damuwa da zunubansu ba. 3Amma waɗancan hadayu abin tunawa da zunubai ne na kowace shekara, 4domin ba zai taɓa yiwuwa jinin bijimai da na awaki yă kawar da zunubai ba.

5Saboda haka, sa’ad da Kiristi ya shigo duniya ya ce,

“Hadaya da sadaka kam ba ka so,

sai dai ka tanadar mini jiki;

6hadayun ƙonawa da kuma hadayun zunubi ba ka ji daɗin.

7Sai na ce, ‘Ga ni nan, a rubuce yake cikin naɗaɗɗen littafi

na zo in aikata nufinka, ya Allah.’ ”10.7 Zab 40.6-8 (dubi Seftuwajin)

8Da farko ya ce, “Hadayu da sadakoki, hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka so, ba ka kuwa jin daɗinsu” (ko da yake doka ta bukaci a yi su). 9Sa’an nan ya ce, “Ga ni nan, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon domin yă kafa na biyun. 10Kuma bisa ga wannan nufi, aka mai da mu masu tsarki ta wurin miƙa hadayar jikin Yesu Kiristi sau ɗaya tak.

11Kowace rana kowane firist yakan tsaya yin hidimar ibadarsa; sau da sau yakan miƙa hadayu iri ɗaya, waɗanda ba za su taɓa kawar da zunubai ba. 12Amma da Kiristi ya miƙa hadaya ɗaya ta dukan lokaci saboda zunubai, sai ya zauna a hannun dama na Allah. 13Tun daga lokacin nan yana jira a mai da abokan gābansa matashin ƙafafunsa, 14gama ta wurin hadayan nan guda ɗaya ya kammala har abada waɗanda ake tsarkake.

15Ruhu Mai Tsarki ma ya yi mana shaida game da wannan. Da farko ya ce,

16“Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su

bayan wannan lokaci,

in ji Ubangiji.

Zan sa dokokina a cikin zukatansu,

in kuma rubuta su a kan zukatansu.”10.16 Irm 31.33

17Sai ya ƙara da cewa,

“Zunubansu da kurakuransu

ba zan ƙara tunawa da su ba.”10.17 Irm 31.34

18In an gafarta zunubai, babu sauran bukatar miƙa hadaya.

Kira don a adana bangaskiya

19Saboda haka, ’yan’uwa, da yake muna da wannan tabbaci na shiga Wuri Mafi Tsarki ta wurin jinin Yesu, 20ta wurin sabuwa, rayayyiyar hanya kuma wadda aka buɗe mana ta labulen nan, wato, jikinsa, 21da yake kuma muna da babban firist mai mulkin gidan Allah, 22bari mu matso kusa da Allah da zuciya mai gaskiya da kuma cikakken tabbaci mai zuwa ta wurin bangaskiya. Bari mu bar zukatan da tsabta, lamirinmu babu mugunta, da kuma jikunanmu a wanke da ruwa. 23Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne. 24Bari kuma mu yi tunani a kan yadda za mu gargaɗe juna ga ƙauna da kuma ayyuka nagari. 25Kada mu daina taruwa kamar yadda waɗansu suka saba, sai dai mu ƙarfafa juna, tun ba ma da kuka ga Ranan nan tana kusatowa ba.

26Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya. 27A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za tă cinye abokan gāban Allah. 28Duk wanda ya ƙi ya kiyaye dokar Musa akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidar mutum biyu ko uku. 29Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani zai dace da mutumin da ya nuna rashin bangirma ga Ɗan Allah, wanda ya yi banza da jinin nan na alkawarin da ya tsarkake shi, wanda kuma ya zargi Ruhun alheri? 30Gama mun san shi, wannan wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce; zan rama,”10.30 M Sh 32.35 da kuma, “Ubangiji zai yi wa mutanensa hukunci.”10.30 M Sh 32.36; Zab 135.14 31Abu mai matuƙar bantsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai rai.

32Ku tuna da kwanakin nan da suka wuce bayan kun sami haske, sa’ad da kuka tsaya daram a tsananin shan wahala. 33Wani lokaci a fili an tsananta muku aka kuma zage ku aka kuma tsananta muku; a wani lokaci kuma kuka tsaya tare da waɗanda aka yi musu haka. 34Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau. 35Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace.

36Kuna bukata ku jimre don sa’ad da kuka aikata nufin Allah, za ku karɓi abin da ya yi alkawari. 37Gama,

“A cikin ɗan lokaci kaɗan,

mai zuwan nan zai zo

ba kuwa zai yi jinkiri ba.

38Amma,

“Mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya.

In kuwa ya ja da baya,

ba zan ji daɗinsa ba.”10.38 Hab 2.3,4

39Amma mu ba na waɗanda suke ja da baya, su kuma hallaka ba ne, amma na waɗanda suka gaskata, suka kuma sami ceto ne.