哥林多前書 16 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

哥林多前書 16:1-24

捐助聖徒

1至於捐款幫助聖徒這件事,你們可以照我吩咐加拉太各教會的方法辦理。 2每逢週日,各人應按照自己的收入抽出一部分留起來,免得我到的時候才現湊。 3我到了以後,會差遣你們委託的人帶著推薦信把你們的捐款送到耶路撒冷4如果我也需要去的話,他們可以跟我一起去。

保羅的計劃

5我正打算從馬其頓經過,過了馬其頓,我就去探望你們。 6我也許會和你們住一段時期,甚至在你們那裡過冬。之後,我無論去什麼地方,你們都可以給我送行。 7我不想只是現在順道探望你們,主若許可,我盼望能夠和你們同住一段時期。 8我會在以弗所停留到五旬節, 9因為大門為我敞開了,工作很有成效,不過反對我的人也很多。

10提摩太到了以後,你們要好好接待他,讓他在你們那裡安心,因為他和我一樣,都是在為主做工。 11所以誰也不許輕視他。你們要幫助他平安地回到我這裡,我正在等候他和弟兄們同來。 12至於亞波羅弟兄,我雖然再三勸他和弟兄們去你們那裡,但他目前還不願啟行。不過他有機會就會去。

勸勉與問候

13你們要警醒,在信仰上堅定不移,做勇敢剛強的人。 14無論做什麼事,都要有愛心。

15弟兄姊妹,你們都知道司提法納一家在亞該亞是最早信主的16·15 最早信主的」希臘文是「最早的果子」。,也知道他們怎樣盡心竭力地服侍聖徒。 16你們要順服這樣的人,也要順服所有同心努力服侍的人。 17我很高興司提法納福徒拿都亞該古來我這裡,因為你們幫不到我的地方,他們都補足了。 18他們使我和你們心裡都感到十分欣慰,你們要敬重這樣的人。

19亞細亞的各教會問候你們。亞居拉百基拉夫婦和常在他們家裡聚會的信徒,奉主的名衷心地向你們問安。 20全體弟兄姊妹都問候你們。你們要以聖潔的吻彼此問候。

21保羅親筆問候你們。

22如果有人不愛主,這人可咒可詛!主啊,我願你來!

23願主耶穌基督的恩典與你們同在! 24我在基督耶穌裡愛你們所有的人。阿們!

Hausa Contemporary Bible

1 Korintiyawa 16:1-24

Bayarwa saboda mutanen Allah

1To, game da tara kuɗi domin taimakon mutanen Allah, ku yi abin da na gaya wa ikkilisiyoyin Galatiyawa. 2A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba. 3In kuwa na iso sai in ba da wasiƙun gabatarwa ga mutanen da kuka amince da su, in kuma aike su da taimakonku zuwa Urushalima. 4In kuma ya dace in tafi, to, sai su tafi tare da ni.

Roƙona

5Bayan na zazzaga Makidoniya, zan zo wurinku, domin zan ratsa ta Makidoniya. 6Wataƙila zan ɗan jima a wajenku, ko ma in ci damina a can, domin ku yi mini rakiya a tafiyata, duk inda za ni. 7Ba na so in gan ku yanzu in wuce kawai, ina fata zan yi ’yan kwanaki tare da ku, in Ubangiji ya yarda. 8Sai dai zan kasance a Afisa har lokacin Fentekos, 9domin an buɗe mini wata hanya mai fāɗi don aiki mai amfani, ko da yake akwai mutane da yawa masu gāba da ni.

10In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi. 11Kada fa wani yă ƙi karɓansa. Ku sallame shi lafiya, domin yă koma wurina. Ina duban hanyarsa tare da ’yan’uwa.

12Batun ɗan’uwanmu Afollos kuwa, na roƙe shi sosai yă zo wurinku tare da ’yan’uwa. Bai so zuwa yanzu ba, amma zai zo in ya sami zarafi.

13Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi. 14Ku yi kome da ƙauna.

15Kun san cewa iyalin gidan Istifanas ne suka fara tuba a Akayya. Sun kuma ba da kansu ga yi wa tsarkaka hidima. Ina roƙonku ’yan’uwa, 16ku ba da kanku ga irin waɗannan, ga kuma kowa da ya haɗa hannu a aikin, yana kuma faman a cikinsa. 17Na yi farin ciki da isowar Istifanas, Fortunatus da Akaikus, domin sun biya bukatar da ba ku iya biya ba. 18Gama sun wartsake ruhuna da kuma naku. Ya kamata ku girmama irin waɗannan mutane.

Gaisuwa ta ƙarshe

19Ikkilisiyoyin da suke a lardin Asiya suna gaisuwa.

Akwila da Firiskila suna gaishe ku sosai cikin Ubangiji, haka ma ikkilisiyar da takan taru a gidansu.

20Dukan ’yan’uwa a nan suna gaisuwa.

Ku gai da juna da sumba mai tsarki.

21Ni, Bulus nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna.

22Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji, la’ana ta zauna a kansa. Zo, ya Ubangiji16.22 Da Arameyik kalman nan Zo, ya Ubangiji ita ce Maranata.!

23Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da ku.

24Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙaunata cikin Kiristi Yesu. Amin.16.24 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā ba su da Amin.