加拉太書 4 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

加拉太書 4:1-31

兒子與奴僕

1然而,產業繼承人還年幼時,雖然身為產業的主人,實際上和奴僕沒有分別。 2他一樣要受監護人和管家的約束,一直到他父親指定他繼承產業的日子為止。 3我們也一樣,當我們還是孩童的時候,我們受世界基本規條的轄制。 4然而,時候一到,上帝就差遣自己的兒子藉著一位女子降生,並受律法的約束, 5為要救贖一切受律法約束的人,使我們成為祂的兒女。

6我們4·6 我們」希臘文是「你們」。既然成為兒女,上帝就差遣祂兒子的靈進入我們的心裡,使我們可以稱呼上帝為「阿爸,父親」。 7由此可見,你們從今以後不再是奴僕,而是兒女。既然身為兒女,就可以靠著上帝成為產業繼承人。

保羅對加拉太人的關懷

8從前,你們不認識上帝,做那些假神的奴隸。 9現在,你們既然認識了上帝,或者更應該說是上帝認識了你們,為什麼還要回到那些無意義的基本規條之下,甘願再做它們的奴隸呢? 10為什麼還拘守什麼日子、月分、節期和年分呢? 11我真擔心我在你們身上的一番心血都枉費了!

12弟兄姊妹,我勸你們現在要像我一樣,因為我已經像你們一樣。你們向來沒有虧待過我。 13你們知道,當初是因為我生病才首次有機會向你們傳福音。 14那時,你們雖然因為我生病而受累,卻沒有輕視我、嫌棄我,反而接待我,就像接待上帝的天使,接待基督耶穌一樣。 15我可以為你們作證,如果可能的話,你們那時就是把眼睛剜出來給我,也心甘情願。你們當初的喜樂哪裡去了? 16現在我因為告訴你們真理,就成了你們的仇人嗎?

17那些人非常熱心地對待你們,其實他們心懷不軌,想要離間我們的關係,使你們熱心地對待他們。 18有人熱心待你們當然很好,但總要動機純正、始終如一,不應該只是我和你們在一起時才熱心待你們。 19孩子們,為了你們,我像一位母親再次經歷生產的痛苦,一直到基督的生命在你們裡面成形。 20我恨不得立刻趕到你們身邊,換種口氣說話,因為我為你們焦慮不安。

夏甲與撒拉的例子

21你們這些甘受律法約束的人啊!告訴我,你們沒聽過律法怎麼說嗎? 22律法書上說:亞伯拉罕有兩個兒子,一個是婢女生的,一個是主母生的。 23婢女的兒子是按著人的意願生的,主母的兒子是按著上帝的應許生的。 24這些事都有更深的含義,兩個婦人是指兩個約。夏甲代表頒佈於西奈山的約,她所生的孩子是奴僕。 25夏甲指的是阿拉伯西奈山,相當於現今的耶路撒冷,她和她的兒女都是奴僕。 26那天上的耶路撒冷則是自由的,是我們的母親。 27因為聖經上說:

「不生育、未生養的婦人啊,

要快樂;

未曾生產的女子啊,

要高聲歡呼,

因為沒有丈夫的比有丈夫的兒女更多。」

28弟兄姊妹,你們都像以撒一樣是照著上帝的應許出生的。 29當時,那按著人的意願生的兒子迫害那靠著聖靈生的兒子,現在的情況也和當時一樣。 30但聖經上怎麼說呢?聖經上說:「趕走婢女和她的兒子,因為婢女的兒子不能與主母的兒子一同承受產業。」 31弟兄姊妹,這樣看來,我們不是婢女的兒女,而是主母的兒女。

Hausa Contemporary Bible

Galatiyawa 4:1-31

1Abin da nake nufi shi ne, muddin magāji yana ɗan yaro ne tukuna, babu bambanci tsakaninsa da bawa, ko da yake shi ne da mallakar kome. 2Yana ƙarƙashin iyayen goyonsa da masu riƙon amana har yă zuwa cikar lokacin da mahaifinsa ya sa. 3Haka yake, sa’ad da muke ’yan yara, mun kasance cikin bauta a ƙarƙashin ƙa’idodin duniya. 4Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka, 5domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya. 6Da yake ku ’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, “Abba,4.6 Arameyik na Mahaifi Uba.” 7Saboda haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.

Damuwar Bulus domin Galatiyawa

8Dā da ba ku san Allah ba, ku bayi ne ga waɗanda a ainihi ba alloli ba ne. 9Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma a ce Allah ya san ku, yaya kuke sāke komawa ga ƙa’idodin duniya marasa ƙarfi, abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu ne? 10Kuna kiyaye ranaku da watanni da lokuta da shekaru na musamman! 11Kai, kun ba ni tsoro, don ya zama kamar duk wahalar da na yi a kanku banza ne!

12Ina roƙonku ’yan’uwa, ku zama kamar ni, gama na zama kamar ku. Ba ku yi mini wani laifi ba. 13Kun san rashin lafiyar da na yi, shi ne ya yi mini hanyar da na kawo muku bishara da farko. 14Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce mala’ikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa. 15Me ya faru da dukan farin cikinku? Na tabbata, a lokacin, da mai yiwuwa ne da kun ciccire idanunku kun ba ni. 16Yanzu na zama abokin gābanku don na faɗa muku gaskiya ke nan?

17Waɗancan mutane suna neman su rinjaye ku da ƙwazo, amma ba da kyakkyawar aniya ba. Abin da suke so shi ne su raba ku da mu, saboda ƙwazonku yă koma gare su. 18Yana da kyau ku kasance da irin wannan niyya idan da nufi mai kyau ne, ku kuma kasance a haka koyaushe ba sai ina tare da ku ba. 19Ya ku ’ya’yana ƙaunatattu, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har sai Kiristi ya kahu a cikinku. 20Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canja muryata mana! Gama na damu ƙwarai saboda ku!

Saratu da Hagar

21Ku gaya mini, ku da kuke so ku zauna a ƙarƙashin Doka, ba ku san abin da Doka ta ce ba ne? 22Gama a rubuce yake cewa Ibrahim yana da ’ya’ya biyu maza, ɗaya ta wurin mace ’yar aikin gidansa, ɗaya kuma ta wurin ainihin matarsa. 23Ɗansa na wajen mace ’yar aikin gidansa ya zo bisa ga ƙa’idar jiki ne; amma ɗansa na wajen ainihin matarsa ya zo a sakamakon alkawarin ne.

24Za a iya ɗaukan waɗannan al’amura a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawura biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar ’ya’yan da za su zama bayi. Hagar ke nan. 25Hagar tana a matsayin Dutsen Sinai a Arabiya tana kuma kwatancin birnin Urushalima na yanzu, gama ita baiwa ce tare da ’ya’yanta. 26Amma Urushalimar da take sama ’yantacciya ce, ita ce kuma mahaifiyarmu. 27Gama a rubuce yake cewa,

“Ki yi farin ciki, ya ke bakararriya,

wadda ba ta haihuwa

ki ɓarke da murna, ki kuma tā da murya,

ke da ba kya naƙuda;

domin da yawa ne ’ya’yan macen da aka yashe,

fiye da na mai miji.”4.27 Ish 54.1

28To, ku ’yan’uwa, ku ’ya’yan alkawari ne kamar Ishaku. 29A wancan lokaci, wannan ɗa wanda aka haifa ta wurin ƙa’idar jiki ya tsananta wa wanda aka haifa ta ikon Ruhu. Haka ma yake har yanzu. 30Amma me Nassi ya ce? Nassi ya ce, “Kori macen nan ’yar aikin gida da ɗanta don ɗan mace ’yar aikin gida ba zai taɓa raba gādo tare da ɗa na ainihin matarka ba.”4.30 Far 21.10 31Saboda haka, ’yan’uwa, mu ba ’ya’yan mace ’yar aikin gida ba ne, amma na ainihin matan gidan ne.