使徒行傳 8 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

使徒行傳 8:1-40

教會受迫害

1當時,掃羅也贊成殺死司提凡。從那天起,耶路撒冷的教會開始遭到極大的迫害。除了使徒之外,門徒都分散到猶太撒瑪利亞各地。 2有些虔誠人將司提凡埋葬了,為他大聲痛哭。

3掃羅卻在摧毀教會,他挨家挨戶搜尋,把男女信徒抓進監裡。

腓利傳揚福音

4但那些逃往各地的信徒逃到哪裡,就將福音傳到哪裡。 5腓利來到撒瑪利亞城宣講基督。 6城裡的人耳聞目睹他所行的神蹟,都聚精會神地聽他講道。 7當時有許多人被污鬼附身,那些污鬼大聲喊叫著被趕了出來。還有不少癱子和瘸子也被醫好了。 8城裡洋溢著歡樂的氣氛。

術士歸主

9有個名叫西門的術士,向來妄自尊大,曾用邪術使撒瑪利亞人驚奇不已。 10無論貴賤,眾人都聽從他,稱他為「上帝的大能者」。 11他們聽從他,因為他長期用邪術迷惑他們。 12後來,他們相信了腓利所傳關於上帝的國度和耶穌基督的福音,男男女女都接受了洗禮。 13西門本人也信了基督,接受了洗禮,並常常追隨腓利左右。腓利所行的神蹟奇事令他非常驚奇。

14耶路撒冷的使徒聽說撒瑪利亞人接受了上帝的道,就派彼得約翰去那裡。 15二人到了,為那些信徒禱告,好讓他們領受聖靈, 16因為他們只是奉耶穌的名受了洗,聖靈還沒有降在他們身上。 17使徒把手按在他們身上,他們就領受了聖靈。

18西門看見使徒把手一按在人身上,就有聖靈賜下來,便拿錢給使徒, 19說:「請把這能力也給我吧,以便我把手按在誰身上,就使誰領受聖靈。」

20彼得責備他說:「你和你的錢都一同毀滅吧!因為你以為可以用錢買上帝的恩賜! 21你在上帝面前心術不正,休想在我們的事工上有份。 22你要悔改,離棄邪惡,向主禱告,或許主會赦免你心中的邪念。 23我看得出你正因為嫉妒而心裡充滿了苦澀,被罪惡捆綁。」

24西門說:「請為我求求主,免得我遭受你們所說的刑罰。」

25彼得約翰為主做見證,傳講主的道。之後,他們啟程回耶路撒冷,沿途又在撒瑪利亞各村莊傳揚福音。

太監歸主

26有一天,主的天使對腓利說:「起來,向南走,往耶路撒冷通往迦薩的路去。」那條路很荒涼。 27腓利立刻動身,結果在那條路上遇見一個衣索匹亞的太監。他是衣索匹亞女王甘大基手下的重臣,負責管理國庫。他剛從耶路撒冷參加敬拜回來, 28正坐在車上誦讀以賽亞先知的書。 29聖靈吩咐腓利:「趕上去,貼近那輛馬車!」

30腓利跑上前,聽見太監在誦讀以賽亞先知的書,就問:「你明白所讀的經文嗎?」

31他說:「沒有人為我解釋,我怎能明白呢?」他就請腓利上車和他一起坐。 32他剛才念的那段經文是:

「祂默然不語,

像被人牽去宰殺的羔羊,

又如在剪毛人手下一聲不吭的綿羊。

33祂忍受恥辱,

無人為祂主持公道,

誰能明白那個世代呢?

因為祂的生命竟然被奪去。」

34太監問腓利:「請問先知是在說誰?在說他自己還是在說別人?」 35腓利就從這段經文入手向他傳耶穌的福音。 36他們往前走的時候,經過一處有水的地方,太監說:「你看,這裡有水,我可以在這裡接受洗禮嗎?」 37腓利說:「只要你全心相信,當然可以。」太監說:「我相信耶穌基督是上帝的兒子!」

38於是,太監吩咐停車,二人一同下到水裡,腓利為他施洗。 39他們從水裡上來時,主的靈把腓利帶走了。太監看不見腓利了,就繼續前行,滿心歡喜。 40後來,腓利出現在亞鎖都。他走遍那裡,在各城各鄉傳揚福音,直到凱撒利亞

Hausa Contemporary Bible

Ayyukan Manzanni 8:1-40

1Shawulu kuwa yana can, yana tabbatar da mutuwarsa.

Tsanantawa da warwatsewar ikkilisiya

A wannan rana wani babban tsanani ya auka wa ikkilisiyar da take a Urushalima, sai duka suka warwatsu ko’ina a Yahudiya da Samariya, manzanni kaɗai ne suka rage. 2Mutane masu tsoron Allah suka binne Istifanus suka kuma yi makoki ƙwarai dominsa. 3Amma Shawulu ya fara hallaka ikkilisiya. Yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata yana jefa su cikin kurkuku.

Filibus a Samariya

4Waɗanda aka wartsar suka yi ta wa’azin maganar a duk inda suka tafi. 5Filibus ya gangara zuwa wani birni a Samariya ya kuma yi shelar Kiristi a can. 6Sa’ad da taron mutane suka ji Filibus suka kuma ga abubuwan banmamakin da ya yi, sai duk suka mai da hankali sosai ga abin da ya faɗa. 7Mugayen ruhohi suka fiffito suna kururuwa daga cikin mutane da yawa, shanyayyu da guragu masu yawa suka sami warkarwa. 8Saboda haka aka yi farin ciki ƙwarai a birnin.

Siman mai sihiri

9To, akwai wani mutum mai suna Siman wanda ya kwana biyu yana yin sihiri a birnin har ya ba wa duk mutanen Samariya mamaki. Ya kuma yi taƙama cewa shi wani mai girma ne, 10dukan mutane kuwa, manyan da ƙanana, suka mai da hankali gare shi suka kuma ce, “Mutumin nan shi ne ikon Allah da aka sani a matsayin Iko Mai Girma” 11Suka bi shi domin ya daɗe yana ba su mamaki da sihirinsa. 12Amma da suka gaskata da Filibus sa’ad da yake wa’azin labari mai daɗi na mulkin Allah da kuma sunan Yesu Kiristi, sai aka yi musu baftisma, maza da mata. 13Siman kansa ya gaskata aka kuma yi masa baftisma. Ya kuma bi Filibus ko’ina, yana mamakin manyan alamu da ayyukan banmamakin da ya gani.

14Sa’ad da manzannin da suke a Urushalima suka ji cewa Samariya ta karɓi maganar Allah, sai suka aika musu da Bitrus da Yohanna. 15Da suka iso, sai suka yi musu addu’a domin su karɓi Ruhu Mai Tsarki, 16domin Ruhu Mai Tsarki bai riga ya sauka wa waninsu ba tukuna, an dai yi musu baftisma ne kawai a cikin sunan Ubangiji Yesu. 17Sa’an nan Bitrus da Yohanna suka ɗibiya hannuwansu a kansu, suka kuwa karɓi Ruhu Mai Tsarki.

18Sa’ad da Siman ya ga cewa ana ba da Ruhu ta wurin ɗibiya hannuwan manzannin, sai ya miƙa musu kuɗi, 19ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iyawa don kowa na ɗibiya wa hannuwana yă karɓi Ruhu Mai Tsarki.”

20Bitrus ya amsa ya ce, “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi! 21Ba ruwanka da wannan hidimar, domin zuciyarka ba daidai take a gaban Allah ba. 22Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi addu’a ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka. 23Gama na lura kana cike da ɗacin rai kana kuma daure cikin zunubi.”

24Sai Siman ya amsa ya ce, “Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda ni don kada ko ɗaya daga cikin abin da ka faɗa ya same ni.”

25Sa’ad da suka yi shaidar suka kuma yi shelar maganar Ubangiji, sai Bitrus da Yohanna suka koma Urushalima, suna wa’azin bishara a ƙauyukan Samariya masu yawa.

Filibus da mutumin Itiyofiya

26To wani mala’ikan Ubangiji ya ce wa Filibus, “Ka yi kudu zuwa hanyar, hanyar hamada, da ta gangara daga Urushalima zuwa Gaza.” 27Saboda haka ya kama hanya, a kan hanyarsa kuwa sai ya sadu da wani mutumin Itiyofiya, wanda yake bābā, hafsa mai muhimmanci wanda yake lura da dukan ma’ajin Kandas (wanda yake nufin “sarauniyar mutanen Itiyofiya”). Mutumin nan ya tafi Urushalima ne domin yin sujada, 28a kan hanyarsa ta komawa gida kuwa yana zaune bisan keken yaƙinsa yana karatun littafin annabin Ishaya. 29Sai Ruhu ya ce wa Filibus, “Matsa wurin kekunan yaƙin nan ka yi kusa da ita.”

30Sai Filibus ya ruga zuwa wajen keken yaƙin ya kuma ji mutumin yana karatun littafin annabin Ishaya. Filibus ya yi tambaya ya ce, “Ka fahimci abin da kake karantawa?”

31Sai ya ce, “Ina fa zan iya, in ba dai wani ya fassara mini ba?” Saboda haka sai ya gayyaci Filibus yă hau yă zauna tare da shi.

32Bābān yana karanta wannan Nassin,

“An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka,

kuma kamar ɗan rago a hannun mai askin gashinsa yake shiru,

haka kuwa bai buɗe bakinsa ba.

33A cikin wulaƙacinsa aka hana masa gaskiya.

Wa zai iya yin zancen zuriyarsa?

Gama an ɗauke ransa daga duniya.”8.33 Ish 53.7,8

34Sai bābān ya tambayi Filibus ya ce, “Ka gaya mini, ina roƙonka, annabin yana magana a kan wane ne, kansa ne, ko kuwa wani dabam?” 35Sa’an nan Filibus ya fara da wannan Nassi ɗin ya kuma faɗa masa labari mai daɗi game da Yesu.

36Yayinda suke cikin tafiya a kan hanya, sai suka iso wani wurin ruwa bābān nan ya ce, “Duba, ga ruwa. Me zai hana a yi mini baftisma?”8.36 Waɗansu rubuce-rubucen hannu da da ba su daɗe ba suna da baftisma? 37 Filibus ya ce, “In ka gaskata da dukan zuciyarka, za ka iya.” Bābān ya ce, “Na gaskata cewa Yesu Kiristi shi ne Ɗan Allah.” 38Ya kuwa ba da umarni a tsai da keken yaƙin. Sa’an nan da Filibus da bābān suka gangara zuwa cikin ruwan Filibus kuwa ya yi masa baftisma. 39Sa’ad da suka fita daga cikin ruwan, sai Ruhun Ubangiji ya fyauce Filibus, bābān kuwa bai ƙara ganinsa ba, amma ya ci gaba da tafiyarsa yana farin ciki. 40Filibus kuwa ya fito a Azotus, ya yi ta zagawa, yana wa’azin bishara a dukan garuruwan sai da ya kai Kaisariya.