启示录 5 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

启示录 5:1-14

羔羊与封印的书卷

1接着,我看见坐在宝座上的那位右手拿着一卷内外写着字、用七个印封住的书。 2有一位大力天使高声问道:“谁有资格揭开那七个封印,打开那卷书?” 3可是,天上、地上、甚至地底下都没有人有资格揭开并阅读那卷书。 4我见无人有资格揭开并阅读那卷书,便放声大哭。 5有一位长老对我说:“不要哭。你看,犹大支派的狮子、大卫的根已经得胜了!祂能揭开那七个封印,打开那卷书。”

6我又看到宝座、四个活物和众长老之间站着一只好像是被宰杀过的羔羊。祂身上的七只角和七只眼睛代表奉差遣到普天下去的上帝的七灵。 7那羔羊走上前去,从坐在宝座上的那位右手中接过书卷。 8祂拿过书卷后,四个活物和二十四位长老就俯伏在羔羊面前,各拿着竖琴和盛满了香的金香炉。那些香就是众圣徒的祈祷。 9他们唱着一首新歌:

“你配拿书卷并揭开封印,

因你曾被杀,

用你的血从各部落、各语言族群、各民族、各国家,

将人买赎回来归给上帝。

10你又使他们成为上帝的国度和祭司,

他们要在地上执掌王权。”

11我看见宝座、四个活物和众长老的周围有千千万万的天使,又听见他们高声呼喊: 12“那被杀的羔羊配得权柄、财富、智慧、能力、尊贵、荣耀和颂赞!”

13我又听到天上、地上、地底下和海洋中一切被造之物同声说:“愿颂赞、尊贵、荣耀和权柄都归于坐在宝座上的那位和羔羊,直到永永远远!” 14四个活物就说:“阿们!”众长老也俯伏敬拜。

Hausa Contemporary Bible

Ruʼuya ta Yohanna 5:1-14

Naɗaɗɗen littafi da kuma Ɗan Ragon

1Sa’an nan na ga a hannun damar wannan wanda yake zaune a kursiyin naɗaɗɗen littafi da rubutu a ciki da wajensa an kuma hatimce shi da hatimai bakwai. 2Na kuma ga wani babban mala’ika yana shela da babbar murya cewa, “Wa ya cancanta yă ɓalle hatiman nan yă kuma buɗe naɗaɗɗen littafin?” 3Amma ba wani a sama ko a ƙasa ko a ƙarƙashin ƙasan da ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin ko ma yă duba cikinsa. 4Na yi ta kuka domin ba a iya samun wanda ya cancanta yă buɗe naɗaɗɗen littafin ko yă duba cikinsa ba. 5Sai ɗaya daga cikin dattawan ya ce mini, “Kada ka yi kuka! Duba, Zakin kabilar Yahuda, da kuma Tushen Dawuda ya ci nasara. Ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin da hatimansa bakwai.”

6Sa’an nan na ga Ɗan Rago, yana kamar an yanka, tsaye a tsakiyar kursiyin, halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan an sun kewaye shi. Yana da ƙahoni bakwai da idanu bakwai, waɗanda suke ruhohi bakwai na Allah da aka aika cikin dukan duniya. 7Ya zo ya karɓi naɗaɗɗen littafin daga hannun dama na wannan wanda yake zaune a kursiyin. 8Bayan ya karɓa, sai halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi ƙasa a gaban Ɗan Ragon. Kowannensu yana da garaya kuma suna riƙe da kaskon zinariya cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka. 9Suka rera sabuwar waƙa,

“Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin

ka kuma buɗe hatimansa,

domin an kashe ka,

da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah,

daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma.

10Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima,

kuma za su yi mulki a duniya.”

11Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. 12Da babbar murya suka rera,

“Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe,

don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi

da girma da ɗaukaka da kuma yabo!”

13Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa,

“Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon

yabo da girma da ɗaukaka da iko,

sun tabbata har abada abadin!”

14Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.