New International Version

Romans 4:1-25

Abraham Justified by Faith

1What then shall we say that Abraham, our forefather according to the flesh, discovered in this matter? 2If, in fact, Abraham was justified by works, he had something to boast about—but not before God. 3What does Scripture say? “Abraham believed God, and it was credited to him as righteousness.”4:3 Gen. 15:6; also in verse 22

4Now to the one who works, wages are not credited as a gift but as an obligation. 5However, to the one who does not work but trusts God who justifies the ungodly, their faith is credited as righteousness. 6David says the same thing when he speaks of the blessedness of the one to whom God credits righteousness apart from works:

7“Blessed are those

whose transgressions are forgiven,

whose sins are covered.

8Blessed is the one

whose sin the Lord will never count against them.”4:8 Psalm 32:1,2

9Is this blessedness only for the circumcised, or also for the uncircumcised? We have been saying that Abraham’s faith was credited to him as righteousness. 10Under what circumstances was it credited? Was it after he was circumcised, or before? It was not after, but before! 11And he received circumcision as a sign, a seal of the righteousness that he had by faith while he was still uncircumcised. So then, he is the father of all who believe but have not been circumcised, in order that righteousness might be credited to them. 12And he is then also the father of the circumcised who not only are circumcised but who also follow in the footsteps of the faith that our father Abraham had before he was circumcised.

13It was not through the law that Abraham and his offspring received the promise that he would be heir of the world, but through the righteousness that comes by faith. 14For if those who depend on the law are heirs, faith means nothing and the promise is worthless, 15because the law brings wrath. And where there is no law there is no transgression.

16Therefore, the promise comes by faith, so that it may be by grace and may be guaranteed to all Abraham’s offspring—not only to those who are of the law but also to those who have the faith of Abraham. He is the father of us all. 17As it is written: “I have made you a father of many nations.”4:17 Gen. 17:5 He is our father in the sight of God, in whom he believed—the God who gives life to the dead and calls into being things that were not.

18Against all hope, Abraham in hope believed and so became the father of many nations, just as it had been said to him, “So shall your offspring be.”4:18 Gen. 15:5 19Without weakening in his faith, he faced the fact that his body was as good as dead—since he was about a hundred years old—and that Sarah’s womb was also dead. 20Yet he did not waver through unbelief regarding the promise of God, but was strengthened in his faith and gave glory to God, 21being fully persuaded that God had power to do what he had promised. 22This is why “it was credited to him as righteousness.” 23The words “it was credited to him” were written not for him alone, 24but also for us, to whom God will credit righteousness—for us who believe in him who raised Jesus our Lord from the dead. 25He was delivered over to death for our sins and was raised to life for our justification.

Hausa Contemporary Bible

Romawa 4:1-25

Adalcin Ibrahim ta wurin bangaskiya

1To, me za mu ce Ibrahim kakan kakanninmu ya gani game da wannan batu? 2In fa da gaske ne Ibrahim ya sami kuɓuta ta wurin ayyuka, yana da abin da zai yin taƙama da shi ke nan, amma ba a gaban Allah ba. 3Me Nassin ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne a gare shi.”4.3 Fit 15.6; haka da ma a aya 22

4To, sa’ad da mutum ya yi aiki, ba a lissafta ladan aikinsa a matsayin kyauta, sai dai a matsayin hakkinsa. 5Amma fa, game da mutumin da ba ya aiki sai dai dogara ga Allah wanda yake kuɓutar da masu mugunta, akan lissafta bangaskiyarsa a matsayin adalci ne. 6Dawuda ya faɗi haka sa’ad da ya yi magana game da albarkar da aka yi wa mutumin da Allah ya lissafta adalci a gare shi, ba don yă yi ayyuka ba.

7“Masu albarka ne

waɗanda aka gafarta laifofinsu,

waɗanda aka kuma rufe zunubansu.

8Mai albarka ne mutumin

da Ubangiji ba zai taɓa lissafta zunubansa ba.”4.8 Zab 32.2

9Shin, wannan albarkar a kan masu kaciya ne kawai, ko kuwa har da marasa kaciya ma? Mun sha faɗi cewa an lissafta bangaskiyar Ibrahim adalci ne a gare shi. 10A kan wane hali ne aka lissafta masa? Bayan da aka yi masa kaciya ne, ko kuwa kafin kaciyar? Ba bayan an yi masa kaciya ba ne, amma kafin a yi masa kaciya! 11Ya kuma karɓi alamar kaciya, hatimin adalcin da yake da shi ta wurin bangaskiya tun yana marar kaciya. Saboda haka fa, ya zama mahaifin dukan waɗanda suka gaskata domin su ma a lasafta su masu adalci ne, ba tare da an yi musu kaciya ba. 12Ya kuma zama mahaifin masu kaciya waɗanda ba kaciya kaɗai suke da ita ba amma har ma suna bin gurbin bangaskiyar da mahaifinmu Ibrahim yake da ita kafin aka yi masa kaciya.

13Ba ta wurin doka ce Ibrahim da zuriyarsa suka sami alkawarin cewa zai zama magājin duniya ba, amma sai dai ta wurin adalcin da yake zuwa ta wurin bangaskiya. 14Gama da a ce masu kiyaye doka ne magāda, ai, da bangaskiya ba ta da amfani, alkawarin kuma ya zama banza, 15domin doka tana jawo fushi ne. Kuma inda babu doka babu keta umarni ke nan.

16Saboda haka, alkawari yakan zo ta wurin bangaskiya ne, domin yă zama ta wurin alheri, don a tabbatar wa dukan zuriyar Ibrahim ba kawai ga waɗanda suke na doka ba amma har ma ga waɗanda suke na bangaskiyar Ibrahim. Shi ne kuwa mahaifinmu duka. 17Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na mai da kai uban al’ummai masu yawa.”4.17 Far 17.5 Shi ubanmu ne a gaban Allah, wanda a cikinsa ya gaskata, Allahn da yake ba da rai ga matattu, yake kuma kiran abubuwan da ba su kasance ba su zama kamar sun kasance.

18Saɓanin dukan bege, Ibrahim cikin bege ya gaskata, haka kuwa ya zama uban al’ummai masu yawa, kamar yadda aka riga aka faɗa masa cewa, “Haka zuriyarka za tă zama.”4.18 Far 15.5 19Ba tare da ya bar bangaskiyarsa ta yi rauni ba, ya fuskanci gaskiyan nan mai cewa jikinsa mai tsufa matacce ne, da yake yana da shekara wajen ɗari, mahaifar Saratu kuma matacciya ce. 20Duk da haka bai yi shakka ta wurin rashin bangaskiya game da alkawarin Allah ba, sai ma ya ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa, ya kuma ɗaukaka Allah, 21yana kuma da cikakken tabbaci cewa Allah yana da iko yă cika abin da ya yi alkawari. 22Shi ya sa, “aka lissafta adalci a gare shi.” 23Kalmomin nan, “aka lissafta a gare shi” ba a rubuta su saboda shi kaɗai ba ne, 24amma saboda mu ma, mu da Allah zai lissafta adalci, mu da muka ba da gaskiya gare shi da ya tashe Yesu Ubangijinmu daga matattu. 25An miƙa shi ga mutuwa saboda zunubanmu, aka kuma tashe shi zuwa rai saboda Allah zai same mu marasa laifi.