New International Version

Romans 12:1-21

A Living Sacrifice

1Therefore, I urge you, brothers and sisters, in view of God’s mercy, to offer your bodies as a living sacrifice, holy and pleasing to God—this is your true and proper worship. 2Do not conform to the pattern of this world, but be transformed by the renewing of your mind. Then you will be able to test and approve what God’s will is—his good, pleasing and perfect will.

Humble Service in the Body of Christ

3For by the grace given me I say to every one of you: Do not think of yourself more highly than you ought, but rather think of yourself with sober judgment, in accordance with the faith God has distributed to each of you. 4For just as each of us has one body with many members, and these members do not all have the same function, 5so in Christ we, though many, form one body, and each member belongs to all the others. 6We have different gifts, according to the grace given to each of us. If your gift is prophesying, then prophesy in accordance with your12:6 Or the faith; 7if it is serving, then serve; if it is teaching, then teach; 8if it is to encourage, then give encouragement; if it is giving, then give generously; if it is to lead,12:8 Or to provide for others do it diligently; if it is to show mercy, do it cheerfully.

Love in Action

9Love must be sincere. Hate what is evil; cling to what is good. 10Be devoted to one another in love. Honor one another above yourselves. 11Never be lacking in zeal, but keep your spiritual fervor, serving the Lord. 12Be joyful in hope, patient in affliction, faithful in prayer. 13Share with the Lord’s people who are in need. Practice hospitality.

14Bless those who persecute you; bless and do not curse. 15Rejoice with those who rejoice; mourn with those who mourn. 16Live in harmony with one another. Do not be proud, but be willing to associate with people of low position.12:16 Or willing to do menial work Do not be conceited.

17Do not repay anyone evil for evil. Be careful to do what is right in the eyes of everyone. 18If it is possible, as far as it depends on you, live at peace with everyone. 19Do not take revenge, my dear friends, but leave room for God’s wrath, for it is written: “It is mine to avenge; I will repay,”12:19 Deut. 32:35 says the Lord. 20On the contrary:

“If your enemy is hungry, feed him;

if he is thirsty, give him something to drink.

In doing this, you will heap burning coals on his head.”12:20 Prov. 25:21,22

21Do not be overcome by evil, but overcome evil with good.

Hausa Contemporary Bible

Romawa 12:1-21

Hadayu masu rai

1Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. 2Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

3Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada yă ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yă auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa. 4Kamar dai yadda kowannenmu yake da jiki ɗaya da gaɓoɓi da yawa, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba, 5haka ma a cikin Kiristi mu da muke da yawa mun zama jiki ɗaya, kuma kowace gaɓar ɗan’uwan sauran ne. 6Muna da baye-baye dabam-dabam, gwargwadon alherin da aka yi mana. In baiwar mutum ta yin annabci ce, sai yă yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarsa. 7In ta hidima ce; sai yă yi hidima. In kuma ta koyarwa ce, sai yă koyar; 8in ta ƙarfafawa ce, sai yă ƙarfafa; in kuma ta ba da taimako ce don biyan bukatun waɗansu, sai yă yi haka hannu sake; in ta shugabanci ce, sai yă yi shugabanci da himma; in ta nuna jinƙai ce, sai yă yi haka da fara’a.

Ƙauna

9Dole ƙauna tă zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu; ku manne wa abin da yake nagari. 10Ku ba da kanku ga juna cikin ƙauna irin ta ’yan’uwa. Kowa yă yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa. 11Kada ku zama marasa himma, sai dai masu himma a ruhaniyarku, kuna bauta wa Ubangiji. 12Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a. 13Ku taimaki mutanen Allah masu bukata. Ku zama masu karɓan baƙi.

14Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku la’anta. 15Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka. 16Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna girman kai, sai ma ku riƙa cuɗanya da talakawa. Kada ku zama masu ɗaga kai.

17Idan kowa ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne. 18Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa. 19Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,”12.19 M Sh 32.35 in ji Ubangiji. 20A maimakon haka,

“In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi;

in yana jin ƙishirwa, ka ba shi ruwan sha.

Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta a kansa.”12.20 K Mag 25.21,22

21Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta.