New International Version

Romans 11:1-36

The Remnant of Israel

1I ask then: Did God reject his people? By no means! I am an Israelite myself, a descendant of Abraham, from the tribe of Benjamin. 2God did not reject his people, whom he foreknew. Don’t you know what Scripture says in the passage about Elijah—how he appealed to God against Israel: 3“Lord, they have killed your prophets and torn down your altars; I am the only one left, and they are trying to kill me”11:3 1 Kings 19:10,14? 4And what was God’s answer to him? “I have reserved for myself seven thousand who have not bowed the knee to Baal.”11:4 1 Kings 19:18 5So too, at the present time there is a remnant chosen by grace. 6And if by grace, then it cannot be based on works; if it were, grace would no longer be grace.

7What then? What the people of Israel sought so earnestly they did not obtain. The elect among them did, but the others were hardened, 8as it is written:

“God gave them a spirit of stupor,

eyes that could not see

and ears that could not hear,

to this very day.”11:8 Deut. 29:4; Isaiah 29:10

9And David says:

“May their table become a snare and a trap,

a stumbling block and a retribution for them.

10May their eyes be darkened so they cannot see,

and their backs be bent forever.”11:10 Psalm 69:22,23

Ingrafted Branches

11Again I ask: Did they stumble so as to fall beyond recovery? Not at all! Rather, because of their transgression, salvation has come to the Gentiles to make Israel envious. 12But if their transgression means riches for the world, and their loss means riches for the Gentiles, how much greater riches will their full inclusion bring!

13I am talking to you Gentiles. Inasmuch as I am the apostle to the Gentiles, I take pride in my ministry 14in the hope that I may somehow arouse my own people to envy and save some of them. 15For if their rejection brought reconciliation to the world, what will their acceptance be but life from the dead? 16If the part of the dough offered as firstfruits is holy, then the whole batch is holy; if the root is holy, so are the branches.

17If some of the branches have been broken off, and you, though a wild olive shoot, have been grafted in among the others and now share in the nourishing sap from the olive root, 18do not consider yourself to be superior to those other branches. If you do, consider this: You do not support the root, but the root supports you. 19You will say then, “Branches were broken off so that I could be grafted in.” 20Granted. But they were broken off because of unbelief, and you stand by faith. Do not be arrogant, but tremble. 21For if God did not spare the natural branches, he will not spare you either.

22Consider therefore the kindness and sternness of God: sternness to those who fell, but kindness to you, provided that you continue in his kindness. Otherwise, you also will be cut off. 23And if they do not persist in unbelief, they will be grafted in, for God is able to graft them in again. 24After all, if you were cut out of an olive tree that is wild by nature, and contrary to nature were grafted into a cultivated olive tree, how much more readily will these, the natural branches, be grafted into their own olive tree!

All Israel Will Be Saved

25I do not want you to be ignorant of this mystery, brothers and sisters, so that you may not be conceited: Israel has experienced a hardening in part until the full number of the Gentiles has come in, 26and in this way11:26 Or and so all Israel will be saved. As it is written:

“The deliverer will come from Zion;

he will turn godlessness away from Jacob.

27And this is11:27 Or will be my covenant with them

when I take away their sins.”11:27 Isaiah 59:20,21; 27:9 (see Septuagint); Jer. 31:33,34

28As far as the gospel is concerned, they are enemies for your sake; but as far as election is concerned, they are loved on account of the patriarchs, 29for God’s gifts and his call are irrevocable. 30Just as you who were at one time disobedient to God have now received mercy as a result of their disobedience, 31so they too have now become disobedient in order that they too may now11:31 Some manuscripts do not have now. receive mercy as a result of God’s mercy to you. 32For God has bound everyone over to disobedience so that he may have mercy on them all.

Doxology

33Oh, the depth of the riches of the wisdom and11:33 Or riches and the wisdom and the knowledge of God!

How unsearchable his judgments,

and his paths beyond tracing out!

34“Who has known the mind of the Lord?

Or who has been his counselor?”11:34 Isaiah 40:13

35“Who has ever given to God,

that God should repay them?”11:35 Job 41:11

36For from him and through him and for him are all things.

To him be the glory forever! Amen.

Hausa Contemporary Bible

Romawa 11:1-36

Ragowar Isra’ila

1To, ina da tambaya. Allah ya ƙi mutanensa ne? Sam, ko kaɗan! Ni mutumin Isra’ila ne kaina, zuriyar Ibrahim kuwa, daga kabilar Benyamin. 2Allah bai ƙi mutanensa da ya rigya sani ba. Ba ku san abin da Nassi ya faɗa game da Iliya ba, yadda ya kawo kuka ga Allah a kan Isra’ila ya ce, 3“Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka suka kuma rurrushe bagadanka; ni kaɗai na ragu, suna kuma neman raina”11.3 1Sar 19.10,14? 4Wace amsa ce Allah ya ba shi? “Na keɓe wa kaina dubu bakwai waɗanda ba su yi wa Ba’al sujada ba.”11.4 1Sar 19.18 5Haka ma, a wannan zamani akwai ragowar da aka zaɓa ta wurin alheri. 6In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga ayyuka ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.

7To, sai me? Abin da Isra’ila suka nema da himma ba su samu ba, amma zaɓaɓɓun suka samu. Sauran suka taurare, 8kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Allah ya ba su ruhun ruɗewa,

idanu don su kāsa gani,

da kuma kunnuwa don su kāsa ji,

har yă zuwa yau.”11.8 M Sh 29.4; Ish 29.10

9Dawuda kuma ya ce,

“Bari teburin cin abincinsu yă zama musu tarko,

sanadin fāɗuwa da dutsen sa tuntuɓe da kuma ramuwa a kansu.

10Bari idanunsu su duhunta don kada su iya gani,

bayansu kuma yă tanƙware har abada.”11.10 Zab 69.22,23

Rassan aure

11Har yanzu ina da tambaya. Sun yi tuntuɓe har ya kai ga fāɗuwar da ba za su iya tashi ba ne? Sam, ko kaɗan! A maimako, saboda laifinsu ne ceto ya zo ga Al’ummai don a sa mutanen Isra’ila su ji kishi. 12Amma in laifinsu yana nufin albarka ga duniya, hasararsu kuma albarka ga Al’ummai, ina misalin yalwar da albarkunsu za su kawo!

13Ina magana da ku ne fa Al’ummai. Tun da yake ni manzo ne ga Al’ummai, ina taƙama da aikin nan nawa, 14da fata zan rura kabilata a ta kowace hanya su ji kishi har ma yă sa in ceci waɗansunsu. 15Gama in ƙinsu da aka yi ya zama sulhu ga duniya, me karɓarsu za tă zama in ba rai daga matattu ba? 16In sashen da aka miƙa a matsayin nunan fari tsattsarka ne, to, sauran ma tsattsarka ne; in saiwar tsattsarka ce, to, sauran rassan ma tsattsarka ne.

17In an sassare waɗansu rassa, kai kuwa da kake kai zaitun jeji, aka ɗauke ka aka kuma yi muku aure, a yanzu kuwa kana shan ni’imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan, 18kada ka yi taƙama cewa ka fi waɗancan rassan da aka sassare. In kuwa ka yi haka, to, ka yi la’akari da wannan. Ba kai ne kake taimakon saiwar ba, saiwar ce take taimakonka. 19To, kana iya cewa, “An sassare rassan ne don a ɗaura aure da ni.” 20Haka yake. Amma an sassare su ne saboda rashin bangaskiya, kai kuma kana tsaye ta wurin bangaskiya. Kada ka yi taƙama, sai dai ka ji tsoro. 21Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba.

22Ka lura fa da alheri da kuma tsananin Allah, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, amma alheri a gare ka, da fata za ka ci gaba cikin alherinsa. In ba haka ba, kai ma za a sare ka. 23In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su. 24Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?

Dukan Isra’ila za su tsira

25Ba na so ku kasance cikin rashin sani game da wannan asirin ’yan’uwa, domin kada ku ɗaga kai. Isra’ila sun ɗanɗana sashe na taurarewa har sai da shigowar Al’ummai masu yawa ya cika. 26Ta haka kuwa za a ceci dukan Isra’ila, kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Mai ceto zai zo daga Sihiyona;

zai kawar da rashin bin Allah daga Yaƙub.

27Wannan kuwa shi ne alkawarina da su

sa’ad da na ɗauke musu zunubansu.”11.27 Ish 59.20,21; Ish 27.9; Irm 31.33,34

28Game da zancen nan na bishara kuwa, su abokan gāba ne saboda ku; amma game da zaɓen kuwa, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu, 29gama kyautar Allah da kiransa ba a sokewa. 30Kamar yadda a dā can ku da kuke marasa biyayya ga Allah kuka sami jinƙai yanzu ta dalilin rashin biyayyarsu, 31haka su ma suka zama marasa biyayya a yanzu domin su ma su sami jinƙai ta dalilin jinƙan da Allah ya yi muku. 32Gama Allah ya daure dukan mutane ga rashin biyayya don yă nuna jinƙai ga kowa.

Ɗaukakawa

33Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace!

Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike,

hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!

34“Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?

Ko kuwa yă ba shi shawara?”11.34 Ish 40.13

35“Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu,

da Allah zai sāka masa?”11.35 Ayu 41.11

36Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance.

Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.