The Arrangement of the Tribal Camps
1The Lord said to Moses and Aaron: 2“The Israelites are to camp around the tent of meeting some distance from it, each of them under their standard and holding the banners of their family.”
3On the east, toward the sunrise, the divisions of the camp of Judah are to encamp under their standard. The leader of the people of Judah is Nahshon son of Amminadab. 4His division numbers 74,600.
5The tribe of Issachar will camp next to them. The leader of the people of Issachar is Nethanel son of Zuar. 6His division numbers 54,400.
7The tribe of Zebulun will be next. The leader of the people of Zebulun is Eliab son of Helon. 8His division numbers 57,400.
9All the men assigned to the camp of Judah, according to their divisions, number 186,400. They will set out first.
10On the south will be the divisions of the camp of Reuben under their standard. The leader of the people of Reuben is Elizur son of Shedeur. 11His division numbers 46,500.
12The tribe of Simeon will camp next to them. The leader of the people of Simeon is Shelumiel son of Zurishaddai. 13His division numbers 59,300.
14The tribe of Gad will be next. The leader of the people of Gad is Eliasaph son of Deuel.2:14 Many manuscripts of the Masoretic Text, Samaritan Pentateuch and Vulgate (see also 1:14); most manuscripts of the Masoretic Text Reuel 15His division numbers 45,650.
16All the men assigned to the camp of Reuben, according to their divisions, number 151,450. They will set out second.
17Then the tent of meeting and the camp of the Levites will set out in the middle of the camps. They will set out in the same order as they encamp, each in their own place under their standard.
18On the west will be the divisions of the camp of Ephraim under their standard. The leader of the people of Ephraim is Elishama son of Ammihud. 19His division numbers 40,500.
20The tribe of Manasseh will be next to them. The leader of the people of Manasseh is Gamaliel son of Pedahzur. 21His division numbers 32,200.
22The tribe of Benjamin will be next. The leader of the people of Benjamin is Abidan son of Gideoni. 23His division numbers 35,400.
24All the men assigned to the camp of Ephraim, according to their divisions, number 108,100. They will set out third.
25On the north will be the divisions of the camp of Dan under their standard. The leader of the people of Dan is Ahiezer son of Ammishaddai. 26His division numbers 62,700.
27The tribe of Asher will camp next to them. The leader of the people of Asher is Pagiel son of Okran. 28His division numbers 41,500.
29The tribe of Naphtali will be next. The leader of the people of Naphtali is Ahira son of Enan. 30His division numbers 53,400.
31All the men assigned to the camp of Dan number 157,600. They will set out last, under their standards.
32These are the Israelites, counted according to their families. All the men in the camps, by their divisions, number 603,550. 33The Levites, however, were not counted along with the other Israelites, as the Lord commanded Moses.
34So the Israelites did everything the Lord commanded Moses; that is the way they encamped under their standards, and that is the way they set out, each of them with their clan and family.
Tsari yadda kabilu za su zauna a sansani
1Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, 2“Duk sa’ad da Isra’ilawa suka yi sansani, kowane mutum zai sauka a inda tutar ƙungiyar kabilarsa take. Sansanin zai kasance a kewaye da Tentin Sujada.”
3Kabilar Yahuda za su yi sansani bisa ga ƙa’idarsu a gabas, wajen fitowar rana. Shugaban mutanen Yahuda kuwa shi ne Nashon ɗan Amminadab. 4Yawan mutanen sashensa 74,600 ne.
5Kabilar Issakar za su yi sansani biye da su. Shugabansu shi ne Netanel ɗan Zuwar. 6Yawan mutanen sashensa 54,400 ne.
7Kabilar Zebulun za su yi sansani biye da su. Shugabansu shi ne Eliyab ɗan Helon. 8Yawan mutanen sashensa 57,400 ne.
9Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Yahuda bisa ga sashensu sun kai 186,400. Su ne za su ja gaba.
10A kudu, a nan ne sashe sansanin mutanen Ruben a ƙarƙashin ƙa’idarsu, za su yi sansani. Shugaban mutanen Ruben shi ne Elizur ɗan Shedeyur. 11Yawan mutanen sashensa 46,500 ne.
12Kabilar Simeyon za su yi sansani biye da su. Shugaban mutanensa shi ne Shelumiyel ɗan Zurishaddai. 13Yawan mutanen sashensa 59,300 ne.
14Kabilar Gad za su zama na biye. Shugaban mutanensa shi ne Eliyasaf ɗan Reyuwel. 15Yawan mutanen sashensa 45,650 ne.
16Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Ruben, bisa ga sashensu sun kai 151,450. Su ne za su zama na biyu in za a tashi.
17Sa’an nan Lawiyawa ɗauke da Tentin Sujada za su kasance a tsakiyar sansani sa’ad da aka tashi tafiya. Za su kama hanya kamar yadda aka dokace su su zauna a sansani, kowa a wurinsa a ƙarƙashin ƙa’idarsu.
18Ta wajen yamma kuma sashen Efraim za su yi sansani a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Shugaban mutanensa, shi ne Elishama ɗan Ammihud. 19Yawan mutanen sashensa 40,500 ne.
20Kabilar Manasse ce za tă zama ta biye. Shugabansu shi ne Gamaliyel ɗan Fedazur. 21Yawan mutanen sashensa 32,200 ne.
22Na biye da su su ne mutanen Benyamin. Shugaban mutanensu kuwa Abidan ɗan Gideyoni. 23Yawan mutanen sashensa 35,400 ne.
24Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Efraim, bisa ga sashensu su kai 108,100 ne. Su ne za su zama na uku sa’ad da za a tashi.
25A arewa za a sami sashen sansanin Dan, a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Shugabansu shi ne Ahiyezer ɗan Ammishaddai. 26Yawan mutanen sashensa 62,700 ne.
27Kabilar Asher ce za tă zama ta biye. Shugabansu shi ne Fagiyel ɗan Okran. 28Yawan mutanen sashensa 41,500 ne.
29Kabilar Naftali za su zama na biye da su. Shugaban mutanen kuwa shi ne Ahira ɗan Enan. 30Yawan mutanen sashensa 53,400 ne
31Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Efraim, bisa ga sashensu su kai 157,600. Su ne za su zama na ƙarshe, ƙarƙashin ƙa’idarsu.
32Waɗannan su ne Isra’ilawan da aka a ƙidaya bisa ga iyalansu. Dukansu da suke a sansani, mutane 603,550 ne. 33Ba a dai ƙidaya Lawiyawa tare da sauran Isra’ilawa ba yadda Ubangiji ya umarci Musa.
34Saboda haka Isra’ilawa suka yi duk ko mene ne da Ubangiji ya umarci Musa. Ta haka ne suka yi sansani a ƙarƙashin ƙa’idarsu kowanne tare da kabilarsa da danginsa.