The Fellowship Offering
1“ ‘If your offering is a fellowship offering, and you offer an animal from the herd, whether male or female, you are to present before the Lord an animal without defect. 2You are to lay your hand on the head of your offering and slaughter it at the entrance to the tent of meeting. Then Aaron’s sons the priests shall splash the blood against the sides of the altar. 3From the fellowship offering you are to bring a food offering to the Lord: the internal organs and all the fat that is connected to them, 4both kidneys with the fat on them near the loins, and the long lobe of the liver, which you will remove with the kidneys. 5Then Aaron’s sons are to burn it on the altar on top of the burnt offering that is lying on the burning wood; it is a food offering, an aroma pleasing to the Lord.
6“ ‘If you offer an animal from the flock as a fellowship offering to the Lord, you are to offer a male or female without defect. 7If you offer a lamb, you are to present it before the Lord, 8lay your hand on its head and slaughter it in front of the tent of meeting. Then Aaron’s sons shall splash its blood against the sides of the altar. 9From the fellowship offering you are to bring a food offering to the Lord: its fat, the entire fat tail cut off close to the backbone, the internal organs and all the fat that is connected to them, 10both kidneys with the fat on them near the loins, and the long lobe of the liver, which you will remove with the kidneys. 11The priest shall burn them on the altar as a food offering presented to the Lord.
12“ ‘If your offering is a goat, you are to present it before the Lord, 13lay your hand on its head and slaughter it in front of the tent of meeting. Then Aaron’s sons shall splash its blood against the sides of the altar. 14From what you offer you are to present this food offering to the Lord: the internal organs and all the fat that is connected to them, 15both kidneys with the fat on them near the loins, and the long lobe of the liver, which you will remove with the kidneys. 16The priest shall burn them on the altar as a food offering, a pleasing aroma. All the fat is the Lord’s.
17“ ‘This is a lasting ordinance for the generations to come, wherever you live: You must not eat any fat or any blood.’ ”
Hadaya ta salama
1“ ‘In hadayar wani mutum, hadaya ta salama ce,3.1 Al’adance; hadaya ta zumunci; haka ma a ayoyi 3, 6 da 9. ya kuma miƙa ’yar dabba daga garke, ko namiji ko ta mace ce, sai yă miƙa dabbar da ba ta da lahani a gaban Ubangiji. 2Yă kuma ɗibiya hannunsa bisa kan hadayarsa, yă yanka ta a mashigin Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna waɗanda suke firistoci za su yayyafa jinin a kan bagade a kowane gefe. 3Daga hadaya ta zumuncin da zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta; wato, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki ko kuwa da sun shafe su, 4da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji. 5’Ya’yan Haruna za su ƙone shi a kan bagade a bisa hadaya ta ƙonawa wadda take a kan itacen da yake cin wuta, kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
6“ ‘In ya miƙa dabba ce daga garke a matsayin hadaya ta salama ga Ubangiji, zai miƙa namiji ko ta mace marar lahani. 7In ya miƙa ɗan rago ne, zai kawo shi a gaban Ubangiji. 8Zai ɗibiya hannu a kan hadayarsa, yă yanka shi a gaban Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza za su yayyafa jinin dabbar a kowane gefe na bagade. 9Daga hadaya ta zumuncin zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, kitsen, ƙibabbiya wutsiyar gaba ɗaya da ya yanka gab da ƙashin gadon baya, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki, ko kuwa da suka shafe su, 10da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji. 11Firist zai ƙone su a kan bagade kamar hadayar abinci, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
12“ ‘In yana miƙa akuya ce, zai kawo ta a gaban Ubangiji. 13Zai ɗibiya hannunsa a kanta yă kuma yanka ta a gaban Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza za su yayyafa jininta a kowane gefe na bagade. 14Daga abin da zai miƙa sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, dukan kitsen da ya rufe kayan cikin, ko kuwa da suka shafe su, 15da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji. 16Firist zai ƙone su a kan bagade kamar abinci, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi. Dukan kitsen na Ubangiji ne.
17“ ‘Wannan dawwammamiyar farilla ce ga tsararraki masu zuwa, a inda za ku zauna. Ba za ku ci wani kitse ko wani jini ba.’ ”