Leviticus 2 – NIV & HCB

New International Version

Leviticus 2:1-16

The Grain Offering

1“ ‘When anyone brings a grain offering to the Lord, their offering is to be of the finest flour. They are to pour olive oil on it, put incense on it 2and take it to Aaron’s sons the priests. The priest shall take a handful of the flour and oil, together with all the incense, and burn this as a memorial2:2 Or representative; also in verses 9 and 16 portion on the altar, a food offering, an aroma pleasing to the Lord. 3The rest of the grain offering belongs to Aaron and his sons; it is a most holy part of the food offerings presented to the Lord.

4“ ‘If you bring a grain offering baked in an oven, it is to consist of the finest flour: either thick loaves made without yeast and with olive oil mixed in or thin loaves made without yeast and brushed with olive oil. 5If your grain offering is prepared on a griddle, it is to be made of the finest flour mixed with oil, and without yeast. 6Crumble it and pour oil on it; it is a grain offering. 7If your grain offering is cooked in a pan, it is to be made of the finest flour and some olive oil. 8Bring the grain offering made of these things to the Lord; present it to the priest, who shall take it to the altar. 9He shall take out the memorial portion from the grain offering and burn it on the altar as a food offering, an aroma pleasing to the Lord. 10The rest of the grain offering belongs to Aaron and his sons; it is a most holy part of the food offerings presented to the Lord.

11“ ‘Every grain offering you bring to the Lord must be made without yeast, for you are not to burn any yeast or honey in a food offering presented to the Lord. 12You may bring them to the Lord as an offering of the firstfruits, but they are not to be offered on the altar as a pleasing aroma. 13Season all your grain offerings with salt. Do not leave the salt of the covenant of your God out of your grain offerings; add salt to all your offerings.

14“ ‘If you bring a grain offering of firstfruits to the Lord, offer crushed heads of new grain roasted in the fire. 15Put oil and incense on it; it is a grain offering. 16The priest shall burn the memorial portion of the crushed grain and the oil, together with all the incense, as a food offering presented to the Lord.

Hausa Contemporary Bible

Firistoci 2:1-16

Hadaya ta hatsi

1“ ‘Sa’ad da wani ya kawo hadaya ta gari ga Ubangiji, hadayarsa za tă zama gari mai laushi ne. Zai zuba mai a kai, yă sa turare a kansa 2yă kai wa ’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci. Firist zai ɗiba gari mai laushin a tafin hannu da kuma man, tare da dukan turaren, yă ƙone wannan a sashen tunawa a kan bagade, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 3Sauran hadaya ta garin zai zama na Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta.

4“ ‘In kuka kawo toyayyen hadayar gari da aka yi daga matoya, zai ƙunshi gari mai laushi, toyayye ba tare da yisti ba, gauraye kuma da mai, ko kuwa ƙosai da aka yi ba tare da yisti ba, aka kuma kwaɓa da mai. 5In an toya hadaya ta garinku a kasko, sai a yi shi da gari mai laushi haɗe da mai, ba kuwa da yisti ba. 6A gutsuttsura shi, a zuba mai a kansa, hadaya ce ta hatsi. 7In hadayarku ta hatsin da aka dafa ne a tukunya, sai a yi shi da gari mai laushi da kuma mai. 8A kawo hatsin da aka yi da waɗannan abubuwa ga Ubangiji; a ba wa firist wanda zai ɗauka yă kai bagade. 9Zai fid da sashen tunawa daga hadaya ta gari, yă ƙone shi a kan bagade kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 10Sauran hadaya ta garin za tă zama ta Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayun da aka yi ga Ubangiji ta wuta.

11“ ‘Kowace hadaya ta garin da kuka kawo ga Ubangiji, dole a yi shi ba tare da yisti ba, gama ba za ku ƙone wani yisti, ko zuma a cikin hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta ba. 12Za ku iya kawo su ga Ubangiji kamar hadaya ta ’ya’yan fari, amma ba za a miƙa su a bagade kamar turare mai ƙanshi ba. 13A sa gishiri a dukan hadayunku na hatsi. Kada a rasa sa gishirin alkawari na Allahnku a hadayunku na hatsi, a sa gishiri a dukan hadayunku.

14“ ‘In kuka kawo hadaya ta gari na ’ya’yan fari ga Ubangiji, sai ku miƙa ɓarzajjen kawunan sabon hatsin da aka gasa a wuta. 15A sa mai da turare a kansa, hadaya ce ta hatsi. 16Firist zai ƙone sashe na ɓarzajjen hatsin da kuma mai, tare da turare don tunawa, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.