New International Version

John 21:1-25

Jesus and the Miraculous Catch of Fish

1Afterward Jesus appeared again to his disciples, by the Sea of Galilee.21:1 Greek Tiberias It happened this way: 2Simon Peter, Thomas (also known as Didymus21:2 Thomas (Aramaic) and Didymus (Greek) both mean twin.), Nathanael from Cana in Galilee, the sons of Zebedee, and two other disciples were together. 3“I’m going out to fish,” Simon Peter told them, and they said, “We’ll go with you.” So they went out and got into the boat, but that night they caught nothing.

4Early in the morning, Jesus stood on the shore, but the disciples did not realize that it was Jesus.

5He called out to them, “Friends, haven’t you any fish?”

“No,” they answered.

6He said, “Throw your net on the right side of the boat and you will find some.” When they did, they were unable to haul the net in because of the large number of fish.

7Then the disciple whom Jesus loved said to Peter, “It is the Lord!” As soon as Simon Peter heard him say, “It is the Lord,” he wrapped his outer garment around him (for he had taken it off) and jumped into the water. 8The other disciples followed in the boat, towing the net full of fish, for they were not far from shore, about a hundred yards.21:8 Or about 90 meters 9When they landed, they saw a fire of burning coals there with fish on it, and some bread.

10Jesus said to them, “Bring some of the fish you have just caught.” 11So Simon Peter climbed back into the boat and dragged the net ashore. It was full of large fish, 153, but even with so many the net was not torn. 12Jesus said to them, “Come and have breakfast.” None of the disciples dared ask him, “Who are you?” They knew it was the Lord. 13Jesus came, took the bread and gave it to them, and did the same with the fish. 14This was now the third time Jesus appeared to his disciples after he was raised from the dead.

Jesus Reinstates Peter

15When they had finished eating, Jesus said to Simon Peter, “Simon son of John, do you love me more than these?”

“Yes, Lord,” he said, “you know that I love you.”

Jesus said, “Feed my lambs.”

16Again Jesus said, “Simon son of John, do you love me?”

He answered, “Yes, Lord, you know that I love you.”

Jesus said, “Take care of my sheep.”

17The third time he said to him, “Simon son of John, do you love me?”

Peter was hurt because Jesus asked him the third time, “Do you love me?” He said, “Lord, you know all things; you know that I love you.”

Jesus said, “Feed my sheep. 18Very truly I tell you, when you were younger you dressed yourself and went where you wanted; but when you are old you will stretch out your hands, and someone else will dress you and lead you where you do not want to go.” 19Jesus said this to indicate the kind of death by which Peter would glorify God. Then he said to him, “Follow me!”

20Peter turned and saw that the disciple whom Jesus loved was following them. (This was the one who had leaned back against Jesus at the supper and had said, “Lord, who is going to betray you?”) 21When Peter saw him, he asked, “Lord, what about him?”

22Jesus answered, “If I want him to remain alive until I return, what is that to you? You must follow me.” 23Because of this, the rumor spread among the believers that this disciple would not die. But Jesus did not say that he would not die; he only said, “If I want him to remain alive until I return, what is that to you?”

24This is the disciple who testifies to these things and who wrote them down. We know that his testimony is true.

25Jesus did many other things as well. If every one of them were written down, I suppose that even the whole world would not have room for the books that would be written.

Hausa Contemporary Bible

Yohanna 21:1-25

Yesu da kamun kifin banmamaki

1Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya.21.1 Wato, Tekun Galili Ga yadda ya faru. 2Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili, ’ya’yan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare. 3Sai Siman Bitrus ya ce musu, “Za ni kamun kifi,” suka ce, “Za mu tafi tare da kai.” Saboda haka suka fita suka shiga jirgin ruwa, amma a daren nan ba su kama kome ba.

4Da sassafe, sai ga Yesu tsaye a gaci, amma almajiran ba su gane cewa Yesu ne ba.

5Sai ya ce musu, “Abokai, kuna da kifi kuwa?”

Suka amsa suka ce, “A’a.”

6Ya ce musu, “Ku jefa abin kamun kifinku dama da jirgin ruwan, za ku samu.” Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo abin kamun kifin saboda yawan kifi.

7Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan. 8Sauran almajiran kuwa suka bi shi cikin jirgin ruwan, janye da abin kamun kifin cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, wajen yadi ɗari ne. 9Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma ’yan burodi.

10Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.” 11Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo abin kamun kifin gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan abin kamun kifin bai tsintsinke ba. 12Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Ba wani daga cikin almajiran da ya yi karambanin tambayarsa, “Wane ne kai?” Sun san cewa Ubangiji ne. 13Yesu ya zo, ya ɗauki burodin ya ba su, haka kuma kifin. 14Wannan fa shi ne sau na uku da Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa bayan an tashe shi daga matattu.

Yesu ya sāke tabbatar da Bitrus

15Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?”

Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.”

Yesu ya ce, “Ciyar da ’ya’yan tumakina.”

16Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?”

Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.”

Yesu ya ce, “Lura da tumakina.”

17Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?”

Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.”

Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina. 18Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.” 19Yesu ya faɗi wannan ne, don yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yă ɗaukaka Allah. Sa’an nan ya ce masa, “Bi ni!”

20Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu sa’ad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”) 21Da Bitrus ya gan shi sai ya ce, “Ubangiji, wannan fa?”

22Yesu ya amsa ya ce, “Idan na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai bi ni.” 23Saboda wannan, jita-jita ta bazu a cikin ’yan’uwa cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma fa Yesu bai ce ba zai mutu ba; shi dai ya ce, “In na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki?”

24Wannan shi ne almajirin da ya ba da shaida a kan waɗannan abubuwa ya kuma rubuta su. Mun san cewa shaidarsa gaskiya ce.

25Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za tă sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.