New International Version

John 17:1-26

Jesus Prays to Be Glorified

1After Jesus said this, he looked toward heaven and prayed:

“Father, the hour has come. Glorify your Son, that your Son may glorify you. 2For you granted him authority over all people that he might give eternal life to all those you have given him. 3Now this is eternal life: that they know you, the only true God, and Jesus Christ, whom you have sent. 4I have brought you glory on earth by finishing the work you gave me to do. 5And now, Father, glorify me in your presence with the glory I had with you before the world began.

Jesus Prays for His Disciples

6“I have revealed you17:6 Greek your name to those whom you gave me out of the world. They were yours; you gave them to me and they have obeyed your word. 7Now they know that everything you have given me comes from you. 8For I gave them the words you gave me and they accepted them. They knew with certainty that I came from you, and they believed that you sent me. 9I pray for them. I am not praying for the world, but for those you have given me, for they are yours. 10All I have is yours, and all you have is mine. And glory has come to me through them. 11I will remain in the world no longer, but they are still in the world, and I am coming to you. Holy Father, protect them by the power of17:11 Or Father, keep them faithful to your name, the name you gave me, so that they may be one as we are one. 12While I was with them, I protected them and kept them safe by17:12 Or kept them faithful to that name you gave me. None has been lost except the one doomed to destruction so that Scripture would be fulfilled.

13“I am coming to you now, but I say these things while I am still in the world, so that they may have the full measure of my joy within them. 14I have given them your word and the world has hated them, for they are not of the world any more than I am of the world. 15My prayer is not that you take them out of the world but that you protect them from the evil one. 16They are not of the world, even as I am not of it. 17Sanctify them by17:17 Or them to live in accordance with the truth; your word is truth. 18As you sent me into the world, I have sent them into the world. 19For them I sanctify myself, that they too may be truly sanctified.

Jesus Prays for All Believers

20“My prayer is not for them alone. I pray also for those who will believe in me through their message, 21that all of them may be one, Father, just as you are in me and I am in you. May they also be in us so that the world may believe that you have sent me. 22I have given them the glory that you gave me, that they may be one as we are one— 23I in them and you in me—so that they may be brought to complete unity. Then the world will know that you sent me and have loved them even as you have loved me.

24“Father, I want those you have given me to be with me where I am, and to see my glory, the glory you have given me because you loved me before the creation of the world.

25“Righteous Father, though the world does not know you, I know you, and they know that you have sent me. 26I have made you17:26 Greek your name known to them, and will continue to make you known in order that the love you have for me may be in them and that I myself may be in them.”

Hausa Contemporary Bible

Yohanna 17:1-26

Yesu ya yi addu’a

1Bayan da Yesu ya faɗi wannan, sai ya dubi sama ya yi addu’a ya ce,

“Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka, don Ɗanka yă ɗaukaka ka. 2Gama ka ba shi iko bisa dukan mutane domin yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi. 3Rai madawwami kuwa shi ne, su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko. 4Na ɗaukaka ka a duniya ta wurin gama aikin da ka ba ni. 5Yanzu ya Uba, ka ɗaukaka ni a gabanka da ɗaukakar da dā nake da ita tun kafin a kafa duniya.

Yesu ya yi addu’a saboda almajiransa

6“Na bayyana ka ga waɗanda ka ba ni a duniya. Su naka ne; kai ka ba ni su sun kuma yi biyayya da maganarka. 7Yanzu sun san cewa duk abin da ka ba ni daga gare ka ya fito. 8Na ba su kalmomin da ka ba ni sun kuwa karɓa. Sun san tabbatacce daga wurinka na fito. Sun kuma gaskata kai ka aiko ni. 9Ina addu’a dominsu. Ba domin duniya nake addu’a ba, amma domin waɗanda ka ba ni, gama su naka ne. 10Duk abin da nake da shi naka ne, kuma duk abin da kake da shi nawa ne. Na kuwa sami ɗaukaka ta wurinsu. 11Ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai Tsarki, ka kiyaye su ta wurin ikon sunanka, sunan da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya. 12Yayinda nake tare da su, na kāre su na kuma kiyaye su ta wurin sunan nan da ka ba ni. Ba ko ɗayan da ya ɓace, sai dai wannan da aka ƙaddara zuwa ga hallaka don Nassi yă cika.

13“Yanzu ina zuwa wurinka, sai dai na faɗi waɗannan abubuwa ne tun ina a duniya domin farin ciki yă zama cikakke a cikinsu. 14Na gaya musu maganarka duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne yadda ni ma ba na duniya ba ne. 15Ba addu’ata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan. 16Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 17Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya. 18Kamar yadda ka aiko ni cikin duniya, haka ni ma na aike su cikin duniya. 19Saboda su ne na tsarkake kaina, domin su ma a tsarkake su da gaske.

Yesu ya yi addu’a saboda dukan masu bi

20“Addu’ata ba saboda masu bina kaɗai ba ne. Ina addu’a kuma saboda waɗanda za su gaskata da ni ta wurin maganarsu. 21Ina so dukansu su zama ɗaya, ya Uba, kamar yadda kake a cikina, ni kuwa a cikinka. Haka su ma bari su zauna cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa kai ka aiko ni. 22Na ba su ɗaukakar da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya. 23Ni a cikinsu kai kuma a cikina. Bari su kasance da cikakken haɗinkai, domin duniya ta san cewa kai ka aiko ni. Ka kuwa ƙaunace su yadda ka ƙaunace ni.

24“Uba, ina so waɗanda ka ba ni su kasance tare da ni a inda nake, su kuma ga ɗaukakata, ɗaukakar da ka ba ni domin kana ƙaunata kafin halittar duniya.

25“Ya Uba Mai Adalci, ko da yake duniya ba tă san ka ba, ni na san ka, sun kuma san kai ka aiko ni. 26Na bayyana ka a gare su, zan kuma ci gaba da bayyana ka domin ƙaunar da ka yi mini ta kasance a cikinsu ni ma in kasance a cikinsu.”