New International Version

John 16:1-33

1“All this I have told you so that you will not fall away. 2They will put you out of the synagogue; in fact, the time is coming when anyone who kills you will think they are offering a service to God. 3They will do such things because they have not known the Father or me. 4I have told you this, so that when their time comes you will remember that I warned you about them. I did not tell you this from the beginning because I was with you, 5but now I am going to him who sent me. None of you asks me, ‘Where are you going?’ 6Rather, you are filled with grief because I have said these things. 7But very truly I tell you, it is for your good that I am going away. Unless I go away, the Advocate will not come to you; but if I go, I will send him to you. 8When he comes, he will prove the world to be in the wrong about sin and righteousness and judgment: 9about sin, because people do not believe in me; 10about righteousness, because I am going to the Father, where you can see me no longer; 11and about judgment, because the prince of this world now stands condemned.

12“I have much more to say to you, more than you can now bear. 13But when he, the Spirit of truth, comes, he will guide you into all the truth. He will not speak on his own; he will speak only what he hears, and he will tell you what is yet to come. 14He will glorify me because it is from me that he will receive what he will make known to you. 15All that belongs to the Father is mine. That is why I said the Spirit will receive from me what he will make known to you.”

The Disciples’ Grief Will Turn to Joy

16Jesus went on to say, “In a little while you will see me no more, and then after a little while you will see me.”

17At this, some of his disciples said to one another, “What does he mean by saying, ‘In a little while you will see me no more, and then after a little while you will see me,’ and ‘Because I am going to the Father’?” 18They kept asking, “What does he mean by ‘a little while’? We don’t understand what he is saying.”

19Jesus saw that they wanted to ask him about this, so he said to them, “Are you asking one another what I meant when I said, ‘In a little while you will see me no more, and then after a little while you will see me’? 20Very truly I tell you, you will weep and mourn while the world rejoices. You will grieve, but your grief will turn to joy. 21A woman giving birth to a child has pain because her time has come; but when her baby is born she forgets the anguish because of her joy that a child is born into the world. 22So with you: Now is your time of grief, but I will see you again and you will rejoice, and no one will take away your joy. 23In that day you will no longer ask me anything. Very truly I tell you, my Father will give you whatever you ask in my name. 24Until now you have not asked for anything in my name. Ask and you will receive, and your joy will be complete.

25“Though I have been speaking figuratively, a time is coming when I will no longer use this kind of language but will tell you plainly about my Father. 26In that day you will ask in my name. I am not saying that I will ask the Father on your behalf. 27No, the Father himself loves you because you have loved me and have believed that I came from God. 28I came from the Father and entered the world; now I am leaving the world and going back to the Father.”

29Then Jesus’ disciples said, “Now you are speaking clearly and without figures of speech. 30Now we can see that you know all things and that you do not even need to have anyone ask you questions. This makes us believe that you came from God.”

31“Do you now believe?” Jesus replied. 32“A time is coming and in fact has come when you will be scattered, each to your own home. You will leave me all alone. Yet I am not alone, for my Father is with me.

33“I have told you these things, so that in me you may have peace. In this world you will have trouble. But take heart! I have overcome the world.”

Hausa Contemporary Bible

Yohanna 16:1-33

1“Na faɗa muku wannan duka, domin kada ku bauɗe. 2Za su kore ku daga majami’a; lalle, lokaci yana zuwa da duk wanda ya kashe ku, zai ɗauka yana yin wa Allah hidima ne. 3Za su yi waɗannan abubuwa ne domin ba su san Uba ko ni ba. 4Na faɗa muku wannan, domin in lokacin ya yi, ku tuna na gargaɗe ku. Ban faɗa muku wannan tun da fari ba domin ina tare da ku.

Aikin Ruhu Mai Tsarki

5“Yanzu zan tafi wurin wanda ya aiko ni, duk da haka ba waninku da ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’ 6Saboda na faɗa waɗannan abubuwa ga shi kun cika da baƙin ciki. 7Amma gaskiya nake gaya muku. Don amfaninku ne zan tafi. Sai ko na tafi, in ba haka ba Mai Taimakon nan ba zai zo muku ba. Amma in na tafi, zan aiko shi gare ku. 8Sa’ad da ya zo kuwa, zai kā da duniya a kan zunubi da adalci da kuma hukunci, 9a kan zunubi, domin mutane ba su gaskata da ni ba; 10a kan adalci, domin zan tafi wurin Uba, inda ba za ku ƙara ganina ba; 11a kan hukunci kuma, domin an yanke hukunci a kan mai mulkin duniyan nan.

12“Ina da sauran abubuwa da yawa da zan faɗa muku, amma ba za ku iya ɗauka a yanzu ba. 13Amma sa’ad da shi, Ruhun gaskiya ya zo, zai bi da ku zuwa ga dukan gaskiya. Ba zai yi magana don kansa ba; zai faɗi abin da ya ji ne kaɗai, zai kuma faɗa muku abin da bai faru ba tukuna. 14Zai kawo ɗaukaka gare ni ta wurin ɗaukan abin da yake nawa, ya bayyana muku. 15Duk abin da yake na Uba nawa ne. Shi ya sa na ce, ‘Ruhun zai ɗauko daga abin da yake nawa, yă bayyana muku.’ ”

Baƙin cikin almajirai zai koma farin ciki

16Yesu ya ci gaba da cewa, “Jim kaɗan, ba za ku ƙara ganina ba, sa’an nan bayan an jima kaɗan kuma, za ku gan ni.”

17A nan fa sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da cewa, ‘Jim kaɗan ba za ku ƙara ganina ba, kuma bayan an jima kaɗan, za ku gan ni,’ da kuma, ‘Domin zan tafi wurin Uba’?” 18Suka yi ta tambaya, “Me yake nufi da ‘jim kaɗan’? Ba mu fahimci abin da yake faɗi ba.”

19Yesu ya gane suna so su tambaye shi game da wannan, sai ya ce musu, “Kuna tambayar juna game da abin da nake nufi da na ce, ‘Jim kaɗan ba za ku ƙara ganina ba, da kuma bayan an jima kaɗan, za ku gan ni’? 20Gaskiya nake gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, yayinda duniya take murna. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki. 21Macen da za tă haihu takan yi naƙuda domin lokacinta ya yi; amma sa’ad da ta haihu, sai ta manta da wahalar domin farin ciki an haifi jariri a duniya. 22Haka ku ma, yanzu ne lokacin baƙin cikinku, amma zan sāke ganinku za ku kuma yi farin ciki, ba kuwa wanda zai ɗauke muku farin cikinku. 23A ranan nan, ba za ku sāke tambaya ta kome ba. Gaskiya nake gaya muku, Ubana zai ba ku kome da kuka roƙa cikin sunana. 24Har yanzu dai ba ku roƙi kome cikin sunana ba. Ku roƙa za ku kuwa samu, farin cikinku kuwa zai zama cikakke.

25“Ko da yake ina magana da misalai, lokaci yana zuwa da ba zan ƙara yin magana da misalai ba, sai dai in faɗa muku a fili game da Ubana. 26A ranan nan, za ku roƙa a cikin sunana. Ban ce zan roƙi Uba a madadinku ba. 27Ai, shi Uban kansa yana ƙaunarku domin kun ƙaunace ni kun kuma gaskata cewa daga Allah na fito. 28Na fito daga wurin Uba, na kuma shigo duniya, yanzu kuwa zan bar duniya in koma wurin Uba.”

29Sai almajiran Yesu suka ce, “Haba, yanzu ne fa kake magana a sarari ba tare da misalai ba. 30Yanzu mun gane cewa ka san kome ba sai wani ya tambaye ka ba. Wannan ya sa muka gaskata ka fito daga Allah.”

31Yesu ya amsa ya ce, “A ƙarshe kun gaskata! 32Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansa. Za ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka ba ni kaɗai ba ne, gama Ubana yana tare da ni.

33“Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”