New International Version

John 12:1-50

Jesus Anointed at Bethany

1Six days before the Passover, Jesus came to Bethany, where Lazarus lived, whom Jesus had raised from the dead. 2Here a dinner was given in Jesus’ honor. Martha served, while Lazarus was among those reclining at the table with him. 3Then Mary took about a pint12:3 Or about 0.5 liter of pure nard, an expensive perfume; she poured it on Jesus’ feet and wiped his feet with her hair. And the house was filled with the fragrance of the perfume.

4But one of his disciples, Judas Iscariot, who was later to betray him, objected, 5“Why wasn’t this perfume sold and the money given to the poor? It was worth a year’s wages.12:5 Greek three hundred denarii6He did not say this because he cared about the poor but because he was a thief; as keeper of the money bag, he used to help himself to what was put into it.

7“Leave her alone,” Jesus replied. “It was intended that she should save this perfume for the day of my burial. 8You will always have the poor among you,12:8 See Deut. 15:11. but you will not always have me.”

9Meanwhile a large crowd of Jews found out that Jesus was there and came, not only because of him but also to see Lazarus, whom he had raised from the dead. 10So the chief priests made plans to kill Lazarus as well, 11for on account of him many of the Jews were going over to Jesus and believing in him.

Jesus Comes to Jerusalem as King

12The next day the great crowd that had come for the festival heard that Jesus was on his way to Jerusalem. 13They took palm branches and went out to meet him, shouting,

“Hosanna!12:13 A Hebrew expression meaning “Save!” which became an exclamation of praise

“Blessed is he who comes in the name of the Lord!”12:13 Psalm 118:25,26

“Blessed is the king of Israel!”

14Jesus found a young donkey and sat on it, as it is written:

15“Do not be afraid, Daughter Zion;

see, your king is coming,

seated on a donkey’s colt.”12:15 Zech. 9:9

16At first his disciples did not understand all this. Only after Jesus was glorified did they realize that these things had been written about him and that these things had been done to him.

17Now the crowd that was with him when he called Lazarus from the tomb and raised him from the dead continued to spread the word. 18Many people, because they had heard that he had performed this sign, went out to meet him. 19So the Pharisees said to one another, “See, this is getting us nowhere. Look how the whole world has gone after him!”

Jesus Predicts His Death

20Now there were some Greeks among those who went up to worship at the festival. 21They came to Philip, who was from Bethsaida in Galilee, with a request. “Sir,” they said, “we would like to see Jesus.” 22Philip went to tell Andrew; Andrew and Philip in turn told Jesus.

23Jesus replied, “The hour has come for the Son of Man to be glorified. 24Very truly I tell you, unless a kernel of wheat falls to the ground and dies, it remains only a single seed. But if it dies, it produces many seeds. 25Anyone who loves their life will lose it, while anyone who hates their life in this world will keep it for eternal life. 26Whoever serves me must follow me; and where I am, my servant also will be. My Father will honor the one who serves me.

27“Now my soul is troubled, and what shall I say? ‘Father, save me from this hour’? No, it was for this very reason I came to this hour. 28Father, glorify your name!”

Then a voice came from heaven, “I have glorified it, and will glorify it again.” 29The crowd that was there and heard it said it had thundered; others said an angel had spoken to him.

30Jesus said, “This voice was for your benefit, not mine. 31Now is the time for judgment on this world; now the prince of this world will be driven out. 32And I, when I am lifted up12:32 The Greek for lifted up also means exalted. from the earth, will draw all people to myself.” 33He said this to show the kind of death he was going to die.

34The crowd spoke up, “We have heard from the Law that the Messiah will remain forever, so how can you say, ‘The Son of Man must be lifted up’? Who is this ‘Son of Man’?”

35Then Jesus told them, “You are going to have the light just a little while longer. Walk while you have the light, before darkness overtakes you. Whoever walks in the dark does not know where they are going. 36Believe in the light while you have the light, so that you may become children of light.” When he had finished speaking, Jesus left and hid himself from them.

Belief and Unbelief Among the Jews

37Even after Jesus had performed so many signs in their presence, they still would not believe in him. 38This was to fulfill the word of Isaiah the prophet:

“Lord, who has believed our message

and to whom has the arm of the Lord been revealed?”12:38 Isaiah 53:1

39For this reason they could not believe, because, as Isaiah says elsewhere:

40“He has blinded their eyes

and hardened their hearts,

so they can neither see with their eyes,

nor understand with their hearts,

nor turn—and I would heal them.”12:40 Isaiah 6:10

41Isaiah said this because he saw Jesus’ glory and spoke about him.

42Yet at the same time many even among the leaders believed in him. But because of the Pharisees they would not openly acknowledge their faith for fear they would be put out of the synagogue; 43for they loved human praise more than praise from God.

44Then Jesus cried out, “Whoever believes in me does not believe in me only, but in the one who sent me. 45The one who looks at me is seeing the one who sent me. 46I have come into the world as a light, so that no one who believes in me should stay in darkness.

47“If anyone hears my words but does not keep them, I do not judge that person. For I did not come to judge the world, but to save the world. 48There is a judge for the one who rejects me and does not accept my words; the very words I have spoken will condemn them at the last day. 49For I did not speak on my own, but the Father who sent me commanded me to say all that I have spoken. 50I know that his command leads to eternal life. So whatever I say is just what the Father has told me to say.”

Hausa Contemporary Bible

Yohanna 12:1-50

An shafe Yesu da mai a Betani

(Mattiyu 26.6-13; Markus 14.3-9)

1Kwana shida kafin Bikin Ƙetarewa, sai Yesu ya iso Betani, inda Lazarus yake, wanda Yesu ya tā da daga matattu. 2A nan aka shirya abincin yamma don girmama Yesu. Marta ta ce yi hidima, Lazarus kuma yana ɗaya cikin waɗanda suke ci tare shi. 3Sai Maryamu ta ɗauki wajen awo guda na nardi zalla, turare mai tsada; ta zuba a ƙafafun Yesu ta kuma goge ƙafafunsa da gashinta. Gidan duk ya cika da ƙanshin turaren.

4Amma ɗaya daga cikin almajiransa, Yahuda Iskariyot, wanda daga baya zai bashe shi, bai amince ba ya ce, 5“Don me ba a sayar da turaren nan aka kuma ba da kuɗin ga matalauta ba? Ai, kuɗin ya kai albashin shekara guda.” 6Ya yi wannan magana ba don ya kula da matalauta ba ne, sai dai don shi ɓarawo ne. Da yake shi ne mai ajiya jakar kuɗin, yakan taimaki kansa da abin da aka sa a ciki.

7Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta, an nufa ta ajiye wannan turaren don ranar jana’izata. 8Kullum za ku kasance da matalauta, amma ba kullum za ku kasance tare da ni ba.”

9Ana cikin haka sai babban taron Yahudawa suka sami labari Yesu yana can suka kuwa zo, ba kawai don shi ba amma don su kuma ga Lazarus, wanda ya tā da daga matattu. 10Saboda haka manyan firistoci suka ƙulla su kashe Lazarus shi ma, 11gama dalilinsa Yahudawa da yawa suna komawa ga Yesu suna kuma ba da gaskiya gare shi.

Shiga mai nasara

(Mattiyu 21.1-11; Markus 11.1-11; Luka 19.28-40)

12Kashegari babban taron da suka zo Bikin suka sami labari cewa Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima. 13Sai suka ɗaɗɗauko rassan dabino suka fiffita taryensa, suna ɗaga murya suna cewa,

“Hosanna!”

“Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!”12.13 Zab 118.25,26

“Mai albarka ne Sarkin Isra’ila!”

14Yesu ya sami ɗan jaki, ya hau, kamar yadda yake a rubuce cewa,

15“Kada ki ji tsoro, ya Diyar Sihiyona;

duba, ga sarkinki yana zuwa,

zaune a kan aholaki jaki.”12.15 Zak 9.9

16Da fari almajiransa ba su gane dukan wannan ba. Sai bayan da aka ɗaukaka Yesu, sa’an nan suka gane cewa an rubuta waɗannan abubuwa game da shi ne, har ma suka yi masa waɗannan abubuwa.

17Taron da suke tare da shi a sa’ad da ya kira Lazarus daga kabari ya kuma tā da shi daga matattu suka yi ta baza labarin. 18Mutane da yawa kuwa suka fita taryensa, saboda sun ji labarin abin banmamakin da ya yi. 19Saboda haka Farisiyawa suka ce wa juna, “Duba, wannan ba ya kai mu ko’ina. Ga shi, duk duniya tana bin sa!”

Yesu ya yi maganar mutuwarsa

20To, akwai waɗansu Hellenawa a cikin waɗanda suka haura don su yi sujada a Bikin. 21Suka zo wurin Filibus, wanda yake daga Betsaida ta Galili, da roƙo. Suka ce, “Ranka yă daɗe, muna so mu ga Yesu.” 22Sai Filibus ya je ya gaya wa Andarawus, Andarawus da kuma Filibus suka gaya wa Yesu.

23Yesu ya amsa ya ce, “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum. 24Gaskiya nake gaya muku, sai ƙwayar alkama ta fāɗi ƙasa ta mutu, in ba haka ba za tă kasance ƙwaya ɗaya tak. Amma in ta mutu, za tă ba da ’ya’ya da yawa. 25Duk mai ƙaunar ransa, zai rasa shi, duk mai ƙin ransa a wannan duniya, zai kiyaye shi har yă zuwa rai madawwami. 26Duk wanda zai bauta mini dole yă bi ni, inda kuma nake, a can bawana zai kasance. Ubana zai girmama wanda yake bauta mini.

27“Yanzu kuwa na damu, amma me zan ce? ‘Uba, ka cece ni daga wannan sa’a’? A’a, ai, saboda wannan dalili ne musamman na zo. 28Uba, ka ɗaukaka sunanka!”

Sai wata murya ta fito daga sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi.” 29Taron da suke a wurin suka ji, suka ce an yi tsawa; waɗansu kuwa suka ce mala’ika ne ya yi masa magana.

30Yesu ya ce, “An yi wannan muryar saboda amfaninku ne, ba don nawa ba. 31Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari’a, yanzu ne za a tumɓuke mai mulkin duniyan nan. 32Amma ni, sa’ad da aka ɗaga ni daga ƙasa, zan ja dukan mutane gare ni.” 33Ya faɗa haka ne don yă nuna irin mutuwar da zai yi.

34Sai taron suka ce, “Ahab, Dokarmu ta gaya mana cewa, Kiristi zai kasance har abada, to, yaya za ka ce, ‘Dole ne a ɗaga Ɗan Mutum?’ Wane ne wannan ‘Ɗan Mutum’?”

35Sai Yesu ya ce musu, “Haske zai kasance da ku na ɗan lokaci. Ku yi tafiya yayinda hasken yana nan tare da ku, kada duhu yă cim muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda za shi ba. 36Ku dogara ga hasken yayinda kuke da shi, don ku zama ’ya’yan haske.” Da Yesu ya gama magana, sai ya tafi ya ɓuya daga gare su.

Yahudawa sun ci gaba da rashin bangaskiya

37Ko bayan Yesu ya yi dukan waɗannan abubuwan banmamaki a gabansu, duk da haka ba su gaskata da shi ba. 38Wannan ya faru ne, don a cika maganar annabi Ishaya cewa,

“Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu,

ga wa kuma aka bayyana hannun ikon Ubangiji?”12.38 Ish 53.1

39Saboda haka ba su iya gaskatawa ba, domin, kamar yadda Ishaya ya faɗa a wani wuri cewa,

40“Ya makantar da idanunsu

ya kuma taurare zukatansu,

don kada su gani da idanunsu,

ko su fahimta a zukatansu,

ko kuwa su juyo, har in warkar da su.”12.40 Ish 6.10

41Ishaya ya faɗi haka ne, saboda ya hangi ɗaukakar Yesu, ya kuwa yi magana a kansa.

42Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi. Amma saboda Farisiyawa ba su furta bangaskiyarsu ba, don tsoron kada a kore su daga majami’a; 43gama sun fi son yabon mutane, fiye da yabon Allah.

44Sa’an nan Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Duk wanda ya gaskata da ni, ba ni yake gaskatawa ba, amma ga wanda ya aiko ni ne. 45Duk mai dubana, yana duban wanda ya aiko ni ne. 46Na zo cikin duniya a kan ni haske ne, don duk wanda ya gaskata da ni, kada yă zauna a cikin duhu.

47“Duk mai jin kalmomina bai kuwa kiyaye su ba, ba ni ba ne nake shari’anta shi. Gama ban zo domin in yi wa duniya shari’a ba, sai dai domin in cece ta. 48Akwai mai hukunci saboda wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi kalmomina ba; wannan maganar da na faɗa ita ce za tă hukunta shi a rana ta ƙarshe. 49Gama ba don kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ne ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa da kuma yadda zan faɗe shi. 50Na san cewa umarninsa yana kai ga rai madawwami. Saboda haka duk abin da na faɗa na faɗe shi ne kamar dai yadda Uba ya ce in faɗa.”