New International Version

Hebrews 11:1-40

Faith in Action

1Now faith is confidence in what we hope for and assurance about what we do not see. 2This is what the ancients were commended for.

3By faith we understand that the universe was formed at God’s command, so that what is seen was not made out of what was visible.

4By faith Abel brought God a better offering than Cain did. By faith he was commended as righteous, when God spoke well of his offerings. And by faith Abel still speaks, even though he is dead.

5By faith Enoch was taken from this life, so that he did not experience death: “He could not be found, because God had taken him away.”11:5 Gen. 5:24 For before he was taken, he was commended as one who pleased God. 6And without faith it is impossible to please God, because anyone who comes to him must believe that he exists and that he rewards those who earnestly seek him.

7By faith Noah, when warned about things not yet seen, in holy fear built an ark to save his family. By his faith he condemned the world and became heir of the righteousness that is in keeping with faith.

8By faith Abraham, when called to go to a place he would later receive as his inheritance, obeyed and went, even though he did not know where he was going. 9By faith he made his home in the promised land like a stranger in a foreign country; he lived in tents, as did Isaac and Jacob, who were heirs with him of the same promise. 10For he was looking forward to the city with foundations, whose architect and builder is God. 11And by faith even Sarah, who was past childbearing age, was enabled to bear children because she11:11 Or By faith Abraham, even though he was too old to have children—and Sarah herself was not able to conceive—was enabled to become a father because he considered him faithful who had made the promise. 12And so from this one man, and he as good as dead, came descendants as numerous as the stars in the sky and as countless as the sand on the seashore.

13All these people were still living by faith when they died. They did not receive the things promised; they only saw them and welcomed them from a distance, admitting that they were foreigners and strangers on earth. 14People who say such things show that they are looking for a country of their own. 15If they had been thinking of the country they had left, they would have had opportunity to return. 16Instead, they were longing for a better country—a heavenly one. Therefore God is not ashamed to be called their God, for he has prepared a city for them.

17By faith Abraham, when God tested him, offered Isaac as a sacrifice. He who had embraced the promises was about to sacrifice his one and only son, 18even though God had said to him, “It is through Isaac that your offspring will be reckoned.”11:18 Gen. 21:12 19Abraham reasoned that God could even raise the dead, and so in a manner of speaking he did receive Isaac back from death.

20By faith Isaac blessed Jacob and Esau in regard to their future.

21By faith Jacob, when he was dying, blessed each of Joseph’s sons, and worshiped as he leaned on the top of his staff.

22By faith Joseph, when his end was near, spoke about the exodus of the Israelites from Egypt and gave instructions concerning the burial of his bones.

23By faith Moses’ parents hid him for three months after he was born, because they saw he was no ordinary child, and they were not afraid of the king’s edict.

24By faith Moses, when he had grown up, refused to be known as the son of Pharaoh’s daughter. 25He chose to be mistreated along with the people of God rather than to enjoy the fleeting pleasures of sin. 26He regarded disgrace for the sake of Christ as of greater value than the treasures of Egypt, because he was looking ahead to his reward. 27By faith he left Egypt, not fearing the king’s anger; he persevered because he saw him who is invisible. 28By faith he kept the Passover and the application of blood, so that the destroyer of the firstborn would not touch the firstborn of Israel.

29By faith the people passed through the Red Sea as on dry land; but when the Egyptians tried to do so, they were drowned.

30By faith the walls of Jericho fell, after the army had marched around them for seven days.

31By faith the prostitute Rahab, because she welcomed the spies, was not killed with those who were disobedient.11:31 Or unbelieving

32And what more shall I say? I do not have time to tell about Gideon, Barak, Samson and Jephthah, about David and Samuel and the prophets, 33who through faith conquered kingdoms, administered justice, and gained what was promised; who shut the mouths of lions, 34quenched the fury of the flames, and escaped the edge of the sword; whose weakness was turned to strength; and who became powerful in battle and routed foreign armies. 35Women received back their dead, raised to life again. There were others who were tortured, refusing to be released so that they might gain an even better resurrection. 36Some faced jeers and flogging, and even chains and imprisonment. 37They were put to death by stoning;11:37 Some early manuscripts stoning; they were put to the test; they were sawed in two; they were killed by the sword. They went about in sheepskins and goatskins, destitute, persecuted and mistreated— 38the world was not worthy of them. They wandered in deserts and mountains, living in caves and in holes in the ground.

39These were all commended for their faith, yet none of them received what had been promised, 40since God had planned something better for us so that only together with us would they be made perfect.

Hausa Contemporary Bible

Ibraniyawa 11:1-40

Ta wurin bangaskiya

1Bangaskiya ita ce kasance tabbacin abin da muke bege a kai da kuma tabbatar da abin da ba mu gani ba. 2Abin da aka yabi kakanni na dā a kai ke nan.

3Ta wurin bangaskiya ne muka fahimci cewa an halicci duniya bisa ga umarnin Allah, saboda an halicce abin da ake gani daga abin da ba a gani.

4Ta wurin bangaskiya Habila ya miƙa wa Allah hadayar da ta fi wadda Kayinu ya miƙa. Ta wurin bangaskiya aka yabe shi cewa shi mai adalci ne, sa’ad da Allah ya yi magana mai kyau game da bayarwarsa. Ta wurin bangaskiya kuma har yanzu yana magana, ko da yake ya riga ya mutu.

5Ta wurin bangaskiya ne aka ɗauki Enok daga wannan rayuwa, ta haka bai ɗanɗana mutuwa ba; ba a kuwa same shi ba, domin Allah ya ɗauke shi. Gama kafin a ɗauke shi, an yabe shi a kan ya gamshi Allah. 6In ba tare da bangaskiya ba kuwa, ba ya yiwuwa a gamshi Allah, domin duk mai zuwa wurin Allah dole yă gaskata cewa yana nan, kuma shi ne yakan sāka wa waɗanda suke nemansa da gaske.

7Ta wurin bangaskiya Nuhu, sa’ad da aka yi masa gargaɗi a kan abubuwan da ba a gani ba tukuna, a cikin tsoro mai tsarki ya sassaƙa jirgi don ceton iyalinsa. Ta wurin bangaskiyarsa ya hukunta duniya ya kuma zama magājin adalcin da ake samu ta wurin bangaskiya.

8Ta wurin bangaskiya ne Ibrahim, sa’ad da aka kira shi ya fita zuwa wata ƙasar da zai karɓi gādo daga baya, ya kuwa yi biyayya ya tafi, ko da yake bai san inda za shi ba. 9Ta wurin bangaskiya ya yi zama a ƙasar da aka yi masa alkawari kamar baƙo a baƙuwar ƙasa; ya zauna a tentuna, haka ma Ishaku da Yaƙub, waɗanda su ma magādan alkawarin nan ne tare da shi. 10Gama yana zuba ido ga birnin nan mai tushe, wanda mai zānen gininsa da kuma mai gininsa Allah ne. 11Ta wurin bangaskiya Ibrahim, ko da yake shekarunsa sun wuce, Saratu kanta kuma bakararriya ce ya iya zama mahaifi domin ya11.11 Ko kuwa Ta wurin bangaskiya Saratu ma, wadda shekarunta sun wuce, ta iya haifi ’ya’ya domin ta amince cewa shi wanda ya yi alkawarin mai aminci ne. 12Saboda haka, daga mutum ɗaya, wanda dā shi ma da matacce kusan ɗaya ne, zuriya masu yawa suka fito kamar taurari a sararin sama da kuma kamar yashin da ba a iya ƙirgawa a bakin teku.

13Duk mutanen nan suna cikin bangaskiya sa’ad da suka mutu. Ba su kuwa karɓi abubuwan da aka yi alkawari ba; sun dai hango su suka kuma marabce su daga nesa. Suka kuma amince cewa su baƙi ne, bare kuma a duniya. 14Mutane masu faɗin irin abubuwan nan sun nuna cewa suna neman ƙasar da take tasu. 15Da a ce suna tunanin ƙasar da suka bari a baya, da sun riga sun sami damar komawa. 16A maimako, suna marmarin wata ƙasa mafi kyau, ta sama. Saboda haka Allah ba ya kunya a kira shi Allahnsu, domin ya riga ya shirya musu birni.

17Ta wurin bangaskiya Ibrahim, sa’ad da Allah ya gwada shi, sai ya miƙa Ishaku hadaya. Shi da ya karɓi alkawaran ya yi shirin miƙa makaɗaicin ɗansa, 18ko da yake Allah ya ce masa, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.”11.18 Far 21.12 19Ibrahim ya yi tunani cewa Allah yana iya tā da matattu, a misalce kuwa, ya sāke karɓan Ishaku daga matattu.

20Ta wurin bangaskiya ne Ishaku ya albarkaci Yaƙub da Isuwa game da nan gabansu.

21Ta wurin bangaskiya ne Yaƙub, sa’ad da yake bakin mutuwa, ya albarkaci kowane ɗan Yusuf, ya kuma yi sujada yayinda yake jingine a kan sandansa.

22Ta wurin bangaskiya ne Yusuf, sa’ad da kwanakinsa suka yi kusan ƙarewa, ya yi magana game da fitowar Isra’ilawa daga Masar ya kuma ba da umarni game da ƙasusuwansa.

23Ta wurin bangaskiya ne iyayen Musa suka ɓoye shi har wata uku bayan haihuwarsa, domin sun ga cewa shi ba kamar sauran yara ba ne, ba su kuwa ji tsoron umarnin sarki ba.

24Ta wurin bangaskiya ne Musa, sa’ad da ya yi girma, ya ƙi a kira shi ɗan diyar Fir’auna. 25Ya zaɓa yă sha wahala tare da mutanen Allah, maimakon yă ji daɗin sha’awace-sha’awacen zunubi na ɗan lokaci. 26Ya ɗauki wulaƙancin da yake sha saboda Kiristi ya fi dukiyar Masar daraja, domin ya sa ido ga ladansa. 27Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, ba tare da jin tsoron fushin sarki ba; ya kuwa jure domin ya ga wannan wanda ba a iya gani. 28Ta wurin bangaskiya ya kiyaye Bikin Ƙetarewa ya kuma yayyafa jini, domin kada mai hallakar ’ya’yan fari yă taɓa ’ya’yan fari na Isra’ila.

29Ta wurin bangaskiya ne mutane suka bi ta cikin Jan Teku, sai ka ce a kan busasshiyar ƙasa; amma da Masarawa suka yi ƙoƙari su yi haka, sai aka nutsar da su.

30Ta wurin bangaskiya ne katangar Yeriko ta rushe, bayan mutane suka yi ta kewaye ta har kwana bakwai.

31Ta wurin bangaskiya ne ba a kashe Rahab karuwan nan, ta tare da marasa biyayya ba don ta marabci ’yan leƙan asiri.

32Me kuma zan faɗa? Ba ni da lokacin da zan ba da labari a kan Gideyon, Barak, Samson, Yefta, Dawuda, Sama’ila, da kuma annabawa, 33waɗanda ta wurin bangaskiya ne suka ci nasara a kan mulkoki, suka aikata adalci, suka kuma sami abin da aka yi alkawari; waɗanda suka rurrufe bakunan zakoki, 34suka kashe harshen wuta, suka kuma tsere wa kaifin takobi; waɗanda aka mai da rashin ƙarfinsu ya zama ƙarfi; waɗanda suka yi jaruntaka wajen yaƙi suka kuma fatattaki mayaƙan waɗansu ƙasashe. 35Mata suka karɓi ƙaunatattunsu da aka sāke tasar daga matattu. Aka azabtar da yawancin mutanen nan, amma suka ƙi a sake su, domin sun tabbata za su sami lada mafi kyau sa’ad da aka tā da matattu. 36Waɗansu suka sha ba’a da bulala, har da dauri da sarƙa, da kuma jefa su cikin kurkuku. 37Aka jajjefe su da duwatsu; aka raba su biyu da zarto; aka kashe su da takobi. Suka yi ta yawo saye da fatun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, suka sha tsanani da kuma wulaƙanci 38duniya ba tă ma cancanci su zauna a cikinta ba. Suka yi ta yawo a cikin hamada da a kan duwatsu, da cikin kogwanni da kuma cikin ramummuka.

39Waɗannan duka an yabe su saboda bangaskiyarsu, duk da haka babu waninsu da ya sami abin da aka yi alkawari. 40Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau. Kuma bai so su kai ga maƙasudin bangaskiyarsu ba sai tare da mu.