Gen. 2 – NIV & HCB

New International Version

Gen. 2:1-25

1Thus the heavens and the earth were completed in all their vast array.

2By the seventh day God had finished the work he had been doing; so on the seventh day he rested from all his work. 3Then God blessed the seventh day and made it holy, because on it he rested from all the work of creating that he had done.

Adam and Eve

4This is the account of the heavens and the earth when they were created, when the Lord God made the earth and the heavens.

5Now no shrub had yet appeared on the earth2:5 Or land; also in verse 6 and no plant had yet sprung up, for the Lord God had not sent rain on the earth and there was no one to work the ground, 6but streams2:6 Or mist came up from the earth and watered the whole surface of the ground. 7Then the Lord God formed a man2:7 The Hebrew for man (adam) sounds like and may be related to the Hebrew for ground (adamah); it is also the name Adam (see verse 20). from the dust of the ground and breathed into his nostrils the breath of life, and the man became a living being.

8Now the Lord God had planted a garden in the east, in Eden; and there he put the man he had formed. 9The Lord God made all kinds of trees grow out of the ground—trees that were pleasing to the eye and good for food. In the middle of the garden were the tree of life and the tree of the knowledge of good and evil.

10A river watering the garden flowed from Eden; from there it was separated into four headwaters. 11The name of the first is the Pishon; it winds through the entire land of Havilah, where there is gold. 12(The gold of that land is good; aromatic resin2:12 Or good; pearls and onyx are also there.) 13The name of the second river is the Gihon; it winds through the entire land of Cush.2:13 Possibly southeast Mesopotamia 14The name of the third river is the Tigris; it runs along the east side of Ashur. And the fourth river is the Euphrates.

15The Lord God took the man and put him in the Garden of Eden to work it and take care of it. 16And the Lord God commanded the man, “You are free to eat from any tree in the garden; 17but you must not eat from the tree of the knowledge of good and evil, for when you eat from it you will certainly die.”

18The Lord God said, “It is not good for the man to be alone. I will make a helper suitable for him.”

19Now the Lord God had formed out of the ground all the wild animals and all the birds in the sky. He brought them to the man to see what he would name them; and whatever the man called each living creature, that was its name. 20So the man gave names to all the livestock, the birds in the sky and all the wild animals.

But for Adam2:20 Or the man no suitable helper was found. 21So the Lord God caused the man to fall into a deep sleep; and while he was sleeping, he took one of the man’s ribs2:21 Or took part of the man’s side and then closed up the place with flesh. 22Then the Lord God made a woman from the rib2:22 Or part he had taken out of the man, and he brought her to the man.

23The man said,

“This is now bone of my bones

and flesh of my flesh;

she shall be called ‘woman,’

for she was taken out of man.”

24That is why a man leaves his father and mother and is united to his wife, and they become one flesh.

25Adam and his wife were both naked, and they felt no shame.

Hausa Contemporary Bible

Farawa 2:1-25

1Ta haka aka gama yin sammai da duniya da dukan abubuwan da suke cikinsu.

2Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa. 3Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi.

Adamu da Hawwa’u

4Wannan shi ne asalin tarihin sammai da duniya sa’ad da aka halicce su.

Sa’ad da Ubangiji Allah ya yi duniya da sammai, 5babu tsiro a duniya kuma ganyaye ba su tsira a busasshiyar ƙasa ko ba, gama Ubangiji Allah bai aiko da ruwan sama a kan duniya ba tukuna, babu kuma wani mutumin da zai nome ƙasar, 6amma dai rafuffuka suna ɓullo da ruwa daga ƙasa suna jiƙe ko’ina a fāɗin ƙasa. 7Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.

8To, fa, Ubangiji Allah ya yi lambu a gabas, a Eden, a can kuwa ya sa mutumin da ya yi. 9Ubangiji Allah ya kuma sa kowane irin itace ya tsira daga ƙasa, itace mai kyan gani, mai amfani kuma don abinci. A tsakiyar lambun kuwa akwai itacen rai da kuma itacen sanin abin da yake da kyau da abin da yake mugu.

10Akwai wani kogi mai ba da ruwa ga lambun wanda ya gangaro daga Eden, daga nan ya rarrabu, ya zama koguna huɗu. 11Sunan kogi na fari, Fishon. Shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya. 12(Zinariyar wannan ƙasa kuwa tana da kyau, akwai kuma kayan ƙanshi da duwatsun da ake kira onis a can ma.) 13Sunan kogi na biyu, Gihon. Shi ne ya malala kewaye da ƙasar Kush.2.13 Mai yiwuwa kudu maso gabas na Mesofotamiya ne 14Sunan kogi na uku Tigris. Wannan ne ya malala ya bi ta gefen gabashin Asshur. Kogi na huɗu kuwa shi ne Yuferites.

15Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi. 16Ubangiji Allah ya umarci mutumin ya ce, “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace a cikin lambun, 17amma kada ka ci daga itacen sanin abin da yake mai kyau da abin da yake mugu, gama a ranar da ka ci shi, lalle za ka mutu.”

18Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”

19To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don yă ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan. 20Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye.

Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba. 21Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama. 22Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.

23Sai mutumin ya ce,

“Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana

nama kuma na namana.

Za a ce da ita ‘mace,’

gama an ciro ta daga namiji.”

24Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

25Mutumin da matarsa, dukansu biyu tsirara suke, ba su kuwa ji kunya ba.