Setting Up the Tabernacle
1Then the Lord said to Moses: 2“Set up the tabernacle, the tent of meeting, on the first day of the first month. 3Place the ark of the covenant law in it and shield the ark with the curtain. 4Bring in the table and set out what belongs on it. Then bring in the lampstand and set up its lamps. 5Place the gold altar of incense in front of the ark of the covenant law and put the curtain at the entrance to the tabernacle.
6“Place the altar of burnt offering in front of the entrance to the tabernacle, the tent of meeting; 7place the basin between the tent of meeting and the altar and put water in it. 8Set up the courtyard around it and put the curtain at the entrance to the courtyard.
9“Take the anointing oil and anoint the tabernacle and everything in it; consecrate it and all its furnishings, and it will be holy. 10Then anoint the altar of burnt offering and all its utensils; consecrate the altar, and it will be most holy. 11Anoint the basin and its stand and consecrate them.
12“Bring Aaron and his sons to the entrance to the tent of meeting and wash them with water. 13Then dress Aaron in the sacred garments, anoint him and consecrate him so he may serve me as priest. 14Bring his sons and dress them in tunics. 15Anoint them just as you anointed their father, so they may serve me as priests. Their anointing will be to a priesthood that will continue throughout their generations.” 16Moses did everything just as the Lord commanded him.
17So the tabernacle was set up on the first day of the first month in the second year. 18When Moses set up the tabernacle, he put the bases in place, erected the frames, inserted the crossbars and set up the posts. 19Then he spread the tent over the tabernacle and put the covering over the tent, as the Lord commanded him.
20He took the tablets of the covenant law and placed them in the ark, attached the poles to the ark and put the atonement cover over it. 21Then he brought the ark into the tabernacle and hung the shielding curtain and shielded the ark of the covenant law, as the Lord commanded him.
22Moses placed the table in the tent of meeting on the north side of the tabernacle outside the curtain 23and set out the bread on it before the Lord, as the Lord commanded him.
24He placed the lampstand in the tent of meeting opposite the table on the south side of the tabernacle 25and set up the lamps before the Lord, as the Lord commanded him.
26Moses placed the gold altar in the tent of meeting in front of the curtain 27and burned fragrant incense on it, as the Lord commanded him.
28Then he put up the curtain at the entrance to the tabernacle. 29He set the altar of burnt offering near the entrance to the tabernacle, the tent of meeting, and offered on it burnt offerings and grain offerings, as the Lord commanded him.
30He placed the basin between the tent of meeting and the altar and put water in it for washing, 31and Moses and Aaron and his sons used it to wash their hands and feet. 32They washed whenever they entered the tent of meeting or approached the altar, as the Lord commanded Moses.
33Then Moses set up the courtyard around the tabernacle and altar and put up the curtain at the entrance to the courtyard. And so Moses finished the work.
The Glory of the Lord
34Then the cloud covered the tent of meeting, and the glory of the Lord filled the tabernacle. 35Moses could not enter the tent of meeting because the cloud had settled on it, and the glory of the Lord filled the tabernacle.
36In all the travels of the Israelites, whenever the cloud lifted from above the tabernacle, they would set out; 37but if the cloud did not lift, they did not set out—until the day it lifted. 38So the cloud of the Lord was over the tabernacle by day, and fire was in the cloud by night, in the sight of all the Israelites during all their travels.
Kafawa tabanakul
1Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, 2“Ka kafa tabanakul, da Tentin Sujada, a kan rana ta fari ga watan fari. 3Ka sa akwatin Alkawari a cikinsa, sa’an nan ka rufe shi da labule. 4Ka shigar da teburin ka shirya kayayyakin a kansa. Sa’an nan ka shigar da wurin ajiye fitilan ka kuma sa fitilunsa. 5Ka sa bagaden zinariya na ƙona turare a gaban akwatin Alkawari, ka kuma sa labule a ƙofar shiga tabanakul.
6“Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar tabanakul, da Tentin Sujada; 7ka ajiye daron tsakanin Tentin Sujada da bagaden, ka kuma zuba ruwa a cikinsa. 8Ka yi fili kewaye da shi, ka kuma sa labule a ƙofar shiga filin.
9“Ka ɗauki man shafewa ka shafe tabanakul da duka abin da yake cikinsa; ka keɓe shi da dukan kayayyakinsa, zai zama tsarkake. 10Sa’an nan ka shafe bagaden hadaya ta ƙonawa da kayansa; ka keɓe bagaden, zai zama mai tsarki. 11Ka shafe daron da wurin ajiyarsa, ka kuma keɓe su.
12“Ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka wanke su da ruwa. 13Sa’an nan ka sa wa Haruna tsarkakun riguna, ka shafe shi, ka kuma keɓe shi don yă yi mini hidima a matsayin firist. 14Ka kawo ’ya’yansa maza ka sa musu taguwoyi. 15Ka shafe su yadda ka shafe mahaifinsu, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Shafe musu man, zai sa su zama firistoci na ɗinɗinɗin, dukan zamanansu.” 16Musa ya aikata dukan kome yadda Ubangiji ya umarce shi.
17Da haka aka kafa tabanakul, a rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu. 18Sa’ad da Musa ya kafa tabanakul, ya sa rammuka a wurinsu, ya sa katakan, ya kuma sa sandunan, ya kakkafa dogayen sandunan. 19Sa’an nan ya shimfiɗa tentin a bisa tabanakul, ya kuma sa murfi a bisa tentin, yadda Ubangiji ya umarce shi.
20Ya ɗauki dokokin Alkawari ya sa a cikin akwatin, ya kuma zura sandunan a zoban akwatin, sa’an nan ya sa murfin kafara a bisansa. 21Sai ya kawo akwatin a cikin tabanakul, ya kuma rataye labulen rufewa ya tsare akwatin Alkawarin, yadda Ubangiji ya umarce shi.
22Musa ya sa teburin a Tentin Sujada, a gefen arewa na tabanakul waje da labulen. 23Ya shirya burodin a kai a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.
24Ya sa wurin ajiye fitilan a Tentin Sujada ɗaura da teburin a gefen kudu na tabanakul 25ya kuma shirya fitilun a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.
26Musa ya sa bagaden zinariya a cikin Tentin Sujada a gaban labulen 27ya ƙone turare mai ƙanshi a kai, yadda Ubangiji ya umarce shi.
28Sa’an nan ya sa labule a ƙofar shiga na tabanakul. 29Ya sa bagaden hadaya ta ƙonawa kusa da ƙofar tabanakul, Tentin Sujada, sa’an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a kansa, yadda Ubangiji ya umarce shi.
30Ya sa daro tsakanin Tentin Sujada da bagade, ya kuma zuba ruwa a cikinsa don wanki, 31a cikin kuwa Musa da Haruna da ’ya’yansa maza sukan wanke hannunsa da ƙafafunsu. 32Sukan yi wanka a duk sa’ad da suka shiga Tentin Sujada, ko in suka kusaci bagade, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
33Sa’an nan Musa ya yi fili kewaye da tabanakul da kuma bagaden, ya rataye labule a ƙofar shiga filin. Da haka Musa ya gama aikin.
Ɗaukakar Ubangiji
34Sa’an nan girgije ya rufe Tentin Sujada sai ɗaukakar Ubangiji ta cika tabanakul. 35Musa bai iya shiga Tentin Sujada ba domin girgije ya riga ya sauka a kansa, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika tabanakul.
36Cikin tafiyar Isra’ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa’ad da girgijen ya tashi daga kan tabanakul. 37Idan girgijen bai tashi ba, ba za su tashi ba, sai a ranar da ya tashi. 38Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan tabanakul da rana, da dare kuwa wuta yake cikinsa domin dukan Isra’ilawa su gani.