New International Version

Acts 26:1-32

1Then Agrippa said to Paul, “You have permission to speak for yourself.”

So Paul motioned with his hand and began his defense: 2“King Agrippa, I consider myself fortunate to stand before you today as I make my defense against all the accusations of the Jews, 3and especially so because you are well acquainted with all the Jewish customs and controversies. Therefore, I beg you to listen to me patiently.

4“The Jewish people all know the way I have lived ever since I was a child, from the beginning of my life in my own country, and also in Jerusalem. 5They have known me for a long time and can testify, if they are willing, that I conformed to the strictest sect of our religion, living as a Pharisee. 6And now it is because of my hope in what God has promised our ancestors that I am on trial today. 7This is the promise our twelve tribes are hoping to see fulfilled as they earnestly serve God day and night. King Agrippa, it is because of this hope that these Jews are accusing me. 8Why should any of you consider it incredible that God raises the dead?

9“I too was convinced that I ought to do all that was possible to oppose the name of Jesus of Nazareth. 10And that is just what I did in Jerusalem. On the authority of the chief priests I put many of the Lord’s people in prison, and when they were put to death, I cast my vote against them. 11Many a time I went from one synagogue to another to have them punished, and I tried to force them to blaspheme. I was so obsessed with persecuting them that I even hunted them down in foreign cities.

12“On one of these journeys I was going to Damascus with the authority and commission of the chief priests. 13About noon, King Agrippa, as I was on the road, I saw a light from heaven, brighter than the sun, blazing around me and my companions. 14We all fell to the ground, and I heard a voice saying to me in Aramaic,26:14 Or Hebrew ‘Saul, Saul, why do you persecute me? It is hard for you to kick against the goads.’

15“Then I asked, ‘Who are you, Lord?’

‘I am Jesus, whom you are persecuting,’ the Lord replied. 16‘Now get up and stand on your feet. I have appeared to you to appoint you as a servant and as a witness of what you have seen and will see of me. 17I will rescue you from your own people and from the Gentiles. I am sending you to them 18to open their eyes and turn them from darkness to light, and from the power of Satan to God, so that they may receive forgiveness of sins and a place among those who are sanctified by faith in me.’

19“So then, King Agrippa, I was not disobedient to the vision from heaven. 20First to those in Damascus, then to those in Jerusalem and in all Judea, and then to the Gentiles, I preached that they should repent and turn to God and demonstrate their repentance by their deeds. 21That is why some Jews seized me in the temple courts and tried to kill me. 22But God has helped me to this very day; so I stand here and testify to small and great alike. I am saying nothing beyond what the prophets and Moses said would happen— 23that the Messiah would suffer and, as the first to rise from the dead, would bring the message of light to his own people and to the Gentiles.”

24At this point Festus interrupted Paul’s defense. “You are out of your mind, Paul!” he shouted. “Your great learning is driving you insane.”

25“I am not insane, most excellent Festus,” Paul replied. “What I am saying is true and reasonable. 26The king is familiar with these things, and I can speak freely to him. I am convinced that none of this has escaped his notice, because it was not done in a corner. 27King Agrippa, do you believe the prophets? I know you do.”

28Then Agrippa said to Paul, “Do you think that in such a short time you can persuade me to be a Christian?”

29Paul replied, “Short time or long—I pray to God that not only you but all who are listening to me today may become what I am, except for these chains.”

30The king rose, and with him the governor and Bernice and those sitting with them. 31After they left the room, they began saying to one another, “This man is not doing anything that deserves death or imprisonment.”

32Agrippa said to Festus, “This man could have been set free if he had not appealed to Caesar.”

Hausa Contemporary Bible

Ayyukan Manzanni 26:1-32

1Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “An ba ka izini ka yi magana.”

Saboda haka Bulus ya yi alama da hannunsa ya fara kāriyarsa. 2Ya ce, “Sarki Agiriffa, na yi sa’a da na tsaya a gabanka yau yayinda nake kāriyata game da dukan zargin Yahudawa, 3musamman ma domin ka saba sosai da dukan al’adun Yahudawa da kuma maganganunsu. Saboda haka ina roƙonka ka saurare ni da haƙuri.

4“Yahudawa duk sun san yadda na yi rayuwa tun ina yaro, daga farkon rayuwata a ƙasarmu da kuma a Urushalima. 5Sun san ni tun da daɗewa za su kuwa shaida, in suna so, cewa bisa ga ɗarikar addininmu mafi tsanani, na yi rayuwar Bafarisiye ne. 6Yanzu kuwa saboda begena cikin abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari ne, ake mini shari’a yau. 7Wannan shi ne alkawarin da kabilanmu goma sha biyu suke bege su ga cikawarsa, yayinda suke bauta wa Allah da himma dare da rana. Ya Sarki, saboda wannan bege ne fa Yahudawa suke zargena. 8Don me wani a cikinku zai yi shakka cewa Allah yana tā da matattu?

9“Ni ma a dā na tabbata cewa ya kamata in yi duk abin da zan iya yi domin in yi gāba da sunan Yesu Banazare. 10Abin da na yi ke nan a Urushalima. Da izinin manyan firistoci na sa tsarkaka da yawa a kurkuku, sa’ad da kuma ake kashe su, nakan ka da ƙuri’ata gāba da su. 11Sau da dama nakan bi majami’a-majami’a, in sa a yi musu hukunci. Na kuma yi ƙoƙarin tilasta su su yi saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.

12“A cikin irin tafiye-tafiyen nan ne ina kan hanya zuwa Damaskus tare da izini daga manyan firistoci. 13Da tsakar rana, ya sarki, sa’ad da nake kan hanya, sai na ga wani haske daga sama, fiye da hasken rana, yana haskakawa kewaye da ni da abokan tafiyata. 14Dukanmu muka fāɗi ƙasa, na kuwa ji wata murya tana ce mini da harshen Arameyik, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Yana da wuya ka shuri tsinken tsokanar dabba.’

15“Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’

“Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa. 16Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka. 17Zan tsirar da kai daga mutanenka da kuma daga Al’ummai. Ina aikan ka zuwa gare su domin 18ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’

19“Saboda haka fa, Sarki Agiriffa, ban yi rashin biyayya ga wahayin nan daga sama ba. 20Da farko ga waɗanda suke a Damaskus, sa’an nan ga waɗanda suke a Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya, da kuma ga Al’ummai su ma, na yi wa’azi don su tuba su juyo ga Allah su kuma tabbatar da tubansu ta wurin ayyukansu. 21Shi ya sa Yahudawa suka kama ni a filin haikali suka kuma yi ƙoƙarin kashe ni. 22Amma na sami taimakon Allah har yă zuwa yau. Yanzu ga ni a tsaye a nan, ina shaida ga babba da yaro. Ba na faɗin kome fiye da abin da annabawa da Musa suka ce zai faru, 23cewa Kiristi zai sha wahala, kuma a matsayin wanda yake na fari da zai tashi daga matattu, zai yi shelar haske ga mutanensa da kuma Al’ummai.”

24A nan ne fa Festus ya tsai da kāriyar Bulus. Ya yi ihu ya ce, “Bulus! Kai dai ruɗaɗɗe ne, yawan karatunka yana juya maka kai.”

25Bulus ya amsa ya ce, “Ba na hauka, ya mafifici Festus. Abin da nake faɗi gaskiya ne da kuma mai kyau. 26Sarki ya san waɗannan abubuwa, ina kuma iya yin magana da shi a sake. Na tabbata cewa ba ɗaya daga cikin waɗannan da ya kuɓuce saninsa, domin ba a ɓoye aka yi shi ba. 27Sarki Agiriffa ka gaskata da annabawa? Na san ka gaskata.”

28Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “Kana tsammani cewa a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kana so ka mai da ni Kirista?”

29Bulus ya amsa ya ce, “Ko a ɗan lokaci, ko a lokaci mai yawa, ina addu’a ga Allah cewa, ba kai kaɗai ba amma duk waɗanda suke saurare ni a yau su zama abin da nake, sai dai ban da sarƙoƙin nan.”

30Sai sarki ya tashi, haka kuma gwamna da Bernis da kuma waɗanda suke zaune tare da su. 31Suka bar ɗakin, kuma yayinda suke magana da juna, sai suka ce, “Wannan mutum ba ya yin kome da ya isa kisa ko dauri.”

32Sai Agiriffa ya ce wa Festus, “Da ba don wannan mutum ya ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba da an sake shi.”