1 John 4 – NIV & HCB

New International Version

1 John 4:1-21

On Denying the Incarnation

1Dear friends, do not believe every spirit, but test the spirits to see whether they are from God, because many false prophets have gone out into the world. 2This is how you can recognize the Spirit of God: Every spirit that acknowledges that Jesus Christ has come in the flesh is from God, 3but every spirit that does not acknowledge Jesus is not from God. This is the spirit of the antichrist, which you have heard is coming and even now is already in the world.

4You, dear children, are from God and have overcome them, because the one who is in you is greater than the one who is in the world. 5They are from the world and therefore speak from the viewpoint of the world, and the world listens to them. 6We are from God, and whoever knows God listens to us; but whoever is not from God does not listen to us. This is how we recognize the Spirit4:6 Or spirit of truth and the spirit of falsehood.

God’s Love and Ours

7Dear friends, let us love one another, for love comes from God. Everyone who loves has been born of God and knows God. 8Whoever does not love does not know God, because God is love. 9This is how God showed his love among us: He sent his one and only Son into the world that we might live through him. 10This is love: not that we loved God, but that he loved us and sent his Son as an atoning sacrifice for our sins. 11Dear friends, since God so loved us, we also ought to love one another. 12No one has ever seen God; but if we love one another, God lives in us and his love is made complete in us.

13This is how we know that we live in him and he in us: He has given us of his Spirit. 14And we have seen and testify that the Father has sent his Son to be the Savior of the world. 15If anyone acknowledges that Jesus is the Son of God, God lives in them and they in God. 16And so we know and rely on the love God has for us.

God is love. Whoever lives in love lives in God, and God in them. 17This is how love is made complete among us so that we will have confidence on the day of judgment: In this world we are like Jesus. 18There is no fear in love. But perfect love drives out fear, because fear has to do with punishment. The one who fears is not made perfect in love.

19We love because he first loved us. 20Whoever claims to love God yet hates a brother or sister is a liar. For whoever does not love their brother and sister, whom they have seen, cannot love God, whom they have not seen. 21And he has given us this command: Anyone who loves God must also love their brother and sister.

Hausa Contemporary Bible

1 Yohanna 4:1-21

Gwada ruhohi

1Abokaina ƙaunatattu, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku gwada ruhohi don ku ga ko daga Allah ne, domin annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya. 2Ga yadda za ku gane Ruhun Allah, duk ruhun da ya yarda cewa Yesu Kiristi ya zo cikin jiki, to, daga Allah yake. 3Amma duk ruhun da bai yarda da Yesu ba, ba daga Allah ba ne, ruhun magabcin Kiristi ne, wanda kuka ji yana zuwa, har ma ya riga ya shigo duniya.

4Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma. 5Su daga duniya ne saboda haka suke magana yadda duniya take ganin abubuwa, duniya kuwa tana sauraronsu. 6Mu daga Allah ne, kuma duk wanda ya san Allah yakan saurare mu. Amma duk wanda ba daga Allah ba, ba ya sauraronmu. Ta haka ne muke gane Ruhun gaskiya, da kuma ruhun ƙarya.

Ƙaunar Allah da kuma tamu

7Abokaina ƙaunatattu, mu ƙaunaci juna, domin ƙauna tana zuwa daga Allah ne. Duk mai ƙauna, haifaffe ne na Allah, ya kuma san Allah. 8Duk wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba, domin Allah ƙauna ne. 9Ga yadda Allah ya nuna ƙaunarsa a cikinmu, Allah ya aiki makaɗaici Ɗansa zuwa duniya domin mu rayu ta wurinsa. 10Wannan ita ce ƙauna, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya kuma aiko Ɗansa yă zama hadaya ta kafara saboda zunubanmu. 11Abokaina ƙaunatattu, da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ya kamata mu ma mu ƙaunaci juna. 12Ba wanda ya taɓa ganin Allah; amma in muna ƙaunar juna, Allah yana raye a cikinmu, ƙaunarsa kuwa ta zama cikakkiya a cikinmu ke nan.

13Mun san cewa muna rayuwa a cikinsa shi kuma a cikinmu, domin ya ba mu Ruhunsa. 14Mun gani, mun kuma shaida cewa Uba ya aiko Ɗansa domin yă zama Mai Ceton duniya. 15Duk wanda ya yarda cewa Yesu Ɗan Allah ne, Allah yana raye a cikinsa, shi kuma a cikin Allah. 16Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana.

Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa. 17Ta haka, ƙauna ta zama cikakkiya a cikinmu domin mu kasance masu ƙarfin hali a ranar shari’a, domin a wannan duniya muna kama da shi. 18Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna.

19Muna ƙauna, domin ya ƙaunace mu da farko. 20Duk wanda ya ce, “Ina ƙaunar Allah,” amma yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne. Gama duk wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba. 21Ya kuma ba mu wannan umarni cewa duk wanda yake ƙaunar Allah, dole yă ƙaunaci ɗan’uwansa.