New International Version

1 Corinthians 6:1-20

Lawsuits Among Believers

1If any of you has a dispute with another, do you dare to take it before the ungodly for judgment instead of before the Lord’s people? 2Or do you not know that the Lord’s people will judge the world? And if you are to judge the world, are you not competent to judge trivial cases? 3Do you not know that we will judge angels? How much more the things of this life! 4Therefore, if you have disputes about such matters, do you ask for a ruling from those whose way of life is scorned in the church? 5I say this to shame you. Is it possible that there is nobody among you wise enough to judge a dispute between believers? 6But instead, one brother takes another to court—and this in front of unbelievers!

7The very fact that you have lawsuits among you means you have been completely defeated already. Why not rather be wronged? Why not rather be cheated? 8Instead, you yourselves cheat and do wrong, and you do this to your brothers and sisters. 9Or do you not know that wrongdoers will not inherit the kingdom of God? Do not be deceived: Neither the sexually immoral nor idolaters nor adulterers nor men who have sex with men6:9 The words men who have sex with men translate two Greek words that refer to the passive and active participants in homosexual acts. 10nor thieves nor the greedy nor drunkards nor slanderers nor swindlers will inherit the kingdom of God. 11And that is what some of you were. But you were washed, you were sanctified, you were justified in the name of the Lord Jesus Christ and by the Spirit of our God.

Sexual Immorality

12“I have the right to do anything,” you say—but not everything is beneficial. “I have the right to do anything”—but I will not be mastered by anything. 13You say, “Food for the stomach and the stomach for food, and God will destroy them both.” The body, however, is not meant for sexual immorality but for the Lord, and the Lord for the body. 14By his power God raised the Lord from the dead, and he will raise us also. 15Do you not know that your bodies are members of Christ himself? Shall I then take the members of Christ and unite them with a prostitute? Never! 16Do you not know that he who unites himself with a prostitute is one with her in body? For it is said, “The two will become one flesh.”6:16 Gen. 2:24 17But whoever is united with the Lord is one with him in spirit.6:17 Or in the Spirit

18Flee from sexual immorality. All other sins a person commits are outside the body, but whoever sins sexually, sins against their own body. 19Do you not know that your bodies are temples of the Holy Spirit, who is in you, whom you have received from God? You are not your own; 20you were bought at a price. Therefore honor God with your bodies.

Hausa Contemporary Bible

1 Korintiyawa 6:1-20

Kaiwa juna kotu

1In wani a cikinku yana da damuwa da wani, don me zai kai ƙara a gaban marasa bi, maimakon yă kai ƙara a gaban tsarkaka? 2Ba ku san cewa tsarkaka ne za su yi wa duniya shari’a ba? In kuwa za ku yi wa duniya shari’a, ai, kun isa ku yi shari’a a kan ƙananan damuwoyi ke nan. 3Ba ku san cewa za mu yi wa mala’iku shari’a ba? Balle al’amuran da suka shafi duniyan nan! 4Saboda haka, in kuna da damuwa game da irin waɗannan al’amura, sai ku naɗa alƙalai ko cikin waɗanda ba kome ba ne a ikkilisiya! 5Na faɗi haka ne don ku ji kunya. Ashe, ba za a iya samun wani a cikinku mai hikima wanda zai iya sasanta tsakanin masu bi ba? 6Me zai sa ɗan’uwa yă kai ƙarar ɗan’uwa, a gaban marasa bi?

7Ƙarar junanku ma da kuke yi, ai, kāsawa ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura ko an zambace ku? 8Amma ga shi ku da kanku kuna cuta, kuna kuma zamba, har ma ga ’yan’uwanku ne kuke yi wannan. 9Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, 10ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. 11Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.

Fasikanci

12“Ina da dama in yi kome,” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ina da dama in yi kome” sai dai ba abin da zai mallake ni. 13“An yi abinci domin ciki ne, ciki kuma domin abinci.” Amma Allah zai hallaka su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki. 14Ta wurin ikonsa, Allah ya tashe Ubangiji daga matattu, haka zai tashe mu mu ma. 15Ba ku sani ba cewa jikunanku gaɓoɓin Kiristi ne kansa? Zai kyautu in ɗauki gaɓoɓin Kiristi in haɗa da jikin karuwa? Sam! 16Ba ku san cewa shi wanda ya haɗa jikinsa da karuwa sun zama ɗaya a cikin jiki ke nan ba? Gama an ce, “Biyun za su zama jiki ɗaya.”6.16 Far 2.24 17Wanda kuwa ya haɗa jikinsa da Ubangiji ya zama ɗaya da shi ke nan a ruhu.

18Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubai da mutum yakan aikata suna waje da jikinsa, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne. 19Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; 20saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.