New Amharic Standard Version

2 ጴጥሮስ 3:1-18

የጌታ ቀን

1ወዳጆች ሆይ፤ ይህ አሁን የምጽፍላችሁ ሁለተኛው መልእክት ነው። ሁለቱንም መልእክቶች የጻፍሁላችሁ ቅን ልቦናችሁን እንድታነቃቁ ለማሳሰብ ነው፤ 2ደግሞም ቀድሞ በቅዱሳን ነቢያት የተነገረውን ቃል እንዲሁም በሐዋርያት አማካይነት በጌታችንና በአዳኛችን የተሰጠውን ትእዛዝ እንድታስቡ ነው።

3ከሁሉ አስቀድሞ ይህን ዕወቁ፤ በመጨረሻው ዘመን የራሳቸውን ክፉ ምኞት የሚከተሉ ዘባቾች እየዘበቱ ይመጣሉ። 4እነርሱም፣ “ ‘እመጣለሁ’ ያለው ታዲያ የት አለ? አባቶች ከሞቱበት ከፍጥረት መጀመሪያ አንሥቶ እስካሁን ድረስ ሁሉም ነገር እንዳለ ይኖራል” ይላሉ። 5ነገር ግን እነዚህ ሰዎች ሰማያት ከጥንት ጀምሮ በእግዚአብሔር ቃል ተፈጥረው እንደሚኖሩ፣ መሬትም በውሃ መካከልና በውሃም እንደ ተሠራች ሆን ብለው ይክዳሉ፤ 6በዚያን ጊዜ የነበረው ዓለም በውሃ ተጥለቅልቆ ጠፋ። 7በዚያው ቃል ደግሞ አሁን ያሉት ሰማያትና ምድር፣ ኀጢአተኞች እስከሚጠፉበት እስከ ፍርድ ቀን ድረስ ለእሳት ተጠብቀዋል።

8ወዳጆች ሆይ፤ በጌታ ዘንድ አንድ ቀን እንደ ሺህ ዓመት፣ ሺህ ዓመትም እንደ አንድ ቀን መሆኑን ይህን አንድ ነገር አትርሱ። 9አንዳንድ ሰዎች የዘገየ እንደሚመስላቸው ጌታ የተስፋ ቃሉን ለመፈጸም አይዘገይም፤ ነገር ግን ማንም እንዳይጠፋ ፈልጎ፣ ሁሉ ለንስሓ እንዲበቃ ስለ እናንተ ይታገሣል።

10የጌታ ቀን ግን እንደ ሌባ ይመጣል፤ በዚያች ቀን ሰማያት በታላቅ ድምፅ ያልፋሉ፤ የሰማይም ፍጥረት በእሳት ይጠፋል፤ ምድርና በእርሷም ላይ ያለ ነገር ሁሉ ይቃጠላል።3፥10 በአንዳንድ ቅጅዎች ምድር ወና ትሆናለች ይላል

11እንግዲህ ሁሉም ነገር በዚህ ሁኔታ የሚጠፋ ከሆነ፣ እናንተ እንዴት ዐይነት ሰዎች ልትሆኑ ይገባችኋል? አዎን፣ በቅድስናና በእውነተኛ መንፈሳዊነት ልትኖሩ ይገባችኋል፤ 12ደግሞም የእግዚአብሔርን ቀን እየተጠባበቃችሁ መምጫውን ልታፋጥኑ3፥12 ወይም የእግዚአብሔርን ቀን መምጣት በናፍቆት ስትጠብቁ ይገባል። በዚያን ቀን ሰማያት በእሳት ተቃጥለው ይጠፋሉ፤ የሰማይም ፍጥረት በታላቅ ትኵሳት ይቀልጣል። 13እኛ ግን ጽድቅ የሚኖርበትን አዲስ ሰማይና አዲስ ምድር በተስፋ ቃሉ መሠረት እንጠባበቃለን።

14ስለዚህ ወዳጆች ሆይ፤ እነዚህን ሁሉ ነገሮች የምትጠባበቁ ስለ ሆናችሁ፣ ያለ ነውርና ያለ ነቀፋ ከእርሱ ጋር በሰላም እንድትገኙ ትጉ። 15የጌታችን ትዕግሥት እናንተ እንድትድኑ እንደሆነ አስቡ፤ እንዲሁም ወንድማችን ጳውሎስ እንደ ተሰጠው ጥበብ መጠን ጻፈላችሁ፤ 16እርሱ ስለ እነዚህ ነገሮች በመልእክቶቹ ሁሉ ጽፎአል፤ በመልእክቶቹም ውስጥ በቀላሉ ለመረዳት የሚያዳግቱ ነገሮች አሉ። ዕውቀት የጐደላቸውና ጽናት የሌላቸው ሰዎች ሌሎችን ቅዱሳት መጻሕፍት እንደሚያጣምሙ፣ እነዚህንም ደግሞ ለገዛ ጥፋታቸው ያጣምማሉ።

17እንግዲህ ወዳጆች ሆይ፤ ይህን አስቀድማችሁ ስላወቃችሁ፣ ጸንታችሁ ከቆማችሁበት መሠረት በዐመፀኞች ስሕተት ተስባችሁ እንዳትወድቁ ተጠንቀቁ። 18ነገር ግን በጌታችንና በአዳኛችን በኢየሱስ ክርስቶስ ጸጋና ዕውቀት እደጉ፤ ለእርሱ አሁንም፣ ለዘላለምም ክብር ይሁን፤ አሜን።

Hausa Contemporary Bible

2 Bitrus 3:1-18

Ranar Ubangiji

1Abokaina ƙaunatattu, wannan ita ce wasiƙata ta biyu gare ku. Na rubuta su biyun su zama abin tuni don su faɗakar da ku ga tunani mai kyau. 2Ina so ku tuna da kalmomin da annabawa masu tsarki na dā suka faɗa da kuma umarnin da Ubangijinmu da Mai Cetonmu ya bayar ta wurin manzanninku.

3Da farko dai, dole ku fahimci wannan cewa a kwanakin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna bin mugayen sha’awace-sha’awacensu. 4Za su ce, “Ina wannan ‘dawowar’ da ya yi alkawari ne? Tun mutuwar kakanninmu, kome yana tafiya kamar yadda yake tun farkon halitta.” 5Amma da gangan suke manta cewa tun dā can ta wurin maganar Allah sammai suka kasance aka kuma yi ƙasa daga ruwa ta wurin ruwa kuma. 6Ta wurin waɗannan ruwan ne aka nutsar, aka kuma hallakar da duniya ta wancan lokaci. 7Ta wurin wannan magana ce aka ajiye sammai da ƙasa na yanzu domin wuta, an ajiye su kuma don ranar hukunci da hallaka ta mutane marasa tsoron Allah.

8Amma kada ku manta da wannan abu guda ɗaya, abokaina ƙaunatattu. Ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekaru dubu ne, shekaru dubu kuma kamar kwana ɗaya ne. 9Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.

10Amma ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo. Sammai za su ɓace da ruri, abubuwan da suke cikinsu za su ƙone, ƙasa kuma da dukan abin da yake cikinta za su tonu.

11Da yake za a hallaka dukan abubuwa ta haka, waɗanne irin mutane ne ya kamata ku zama? Ya kamata ku yi rayuwar tsarki da ta tsoron Allah, 12yayinda kuke zuba ido ga zuwan ranar Allah kuna gaggauta zuwanta. Wannan rana za tă kawo wa sammai hallaka ta ƙunan wuta, abubuwa kuma za su narke don zafi. 13Amma bisa ga alkawarinsa muna zuba ido ga sabuwar sama da kuma sabuwar ƙasa, inda adalci zai yi zama.

14Saboda haka, abokaina ƙaunatattu, da yake kuna zuba ido ga wannan, sai ku yi matuƙar ƙoƙari don a same ku ba tabo, sai dai zaman salama da shi. 15Ku yi zaman sanin cewa haƙurin Ubangijinmu yana nufin ceto ne, kamar yadda ƙaunataccen ɗan’uwanmu Bulus ma ya rubuta muku da hikimar da Allah ya ba shi. 16Haka yake rubutu cikin dukan wasiƙunsa, yana magana a cikinsu a kan waɗannan al’amura. Wasiƙunsa sun ƙunshi waɗansu abubuwa masu wuyar fahimta, waɗanda jahilai da kuma waɗanda ba tsayayyu ba ne suke murɗe ma’anarsu, kamar yadda suke yi da sauran Nassosi, ta haka suke jawo wa kansu hallaka.

17Saboda haka, abokaina ƙaunatattu, da yake kun riga kun san wannan, sai ku zauna a faɗake don kada a ɗauke hankalinku ta wurin kuskuren marasa bin dokan nan har ku fāɗi daga matsayinku. 18Sai dai ku yi girma cikin alheri da sanin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi.

A gare shi ɗaukaka ta tabbata yanzu da har abada! Amin.