King James Version

Acts 3:1-26

1Now Peter and John went up together into the temple at the hour of prayer, being the ninth hour. 2And a certain man lame from his mother’s womb was carried, whom they laid daily at the gate of the temple which is called Beautiful, to ask alms of them that entered into the temple; 3Who seeing Peter and John about to go into the temple asked an alms. 4And Peter, fastening his eyes upon him with John, said, Look on us. 5And he gave heed unto them, expecting to receive something of them. 6Then Peter said, Silver and gold have I none; but such as I have give I thee: In the name of Jesus Christ of Nazareth rise up and walk. 7And he took him by the right hand, and lifted him up: and immediately his feet and ankle bones received strength. 8And he leaping up stood, and walked, and entered with them into the temple, walking, and leaping, and praising God. 9And all the people saw him walking and praising God: 10And they knew that it was he which sat for alms at the Beautiful gate of the temple: and they were filled with wonder and amazement at that which had happened unto him. 11And as the lame man which was healed held Peter and John, all the people ran together unto them in the porch that is called Solomon’s, greatly wondering.

12¶ And when Peter saw it, he answered unto the people, Ye men of Israel, why marvel ye at this? or why look ye so earnestly on us, as though by our own power or holiness we had made this man to walk? 13The God of Abraham, and of Isaac, and of Jacob, the God of our fathers, hath glorified his Son Jesus; whom ye delivered up, and denied him in the presence of Pilate, when he was determined to let him go. 14But ye denied the Holy One and the Just, and desired a murderer to be granted unto you; 15And killed the Prince of life, whom God hath raised from the dead; whereof we are witnesses. 16And his name through faith in his name hath made this man strong, whom ye see and know: yea, the faith which is by him hath given him this perfect soundness in the presence of you all. 17And now, brethren, I wot that through ignorance ye did it, as did also your rulers. 18But those things, which God before had shewed by the mouth of all his prophets, that Christ should suffer, he hath so fulfilled.

19¶ Repent ye therefore, and be converted, that your sins may be blotted out, when the times of refreshing shall come from the presence of the Lord; 20And he shall send Jesus Christ, which before was preached unto you: 21Whom the heaven must receive until the times of restitution of all things, which God hath spoken by the mouth of all his holy prophets since the world began. 22For Moses truly said unto the fathers, A prophet shall the Lord your God raise up unto you of your brethren, like unto me; him shall ye hear in all things whatsoever he shall say unto you. 23And it shall come to pass, that every soul, which will not hear that prophet, shall be destroyed from among the people. 24Yea, and all the prophets from Samuel and those that follow after, as many as have spoken, have likewise foretold of these days. 25Ye are the children of the prophets, and of the covenant which God made with our fathers, saying unto Abraham, And in thy seed shall all the kindreds of the earth be blessed. 26Unto you first God, having raised up his Son Jesus, sent him to bless you, in turning away every one of you from his iniquities.

Hausa Contemporary Bible

Ayyukan Manzanni 3:1-26

Bitrus ya warkar da gurgu mai bara

1Wata rana, Bitrus da Yohanna suna haurawa zuwa haikali a lokacin addu’a da ƙarfe uku na rana. 2To, sai ga wani da aka haifa gurgu ana ɗauke da shi zuwa ƙofar haikalin da ake kira Kyakkyawa, inda akan ajiye kowace rana, don yă yi bara daga masu shigowa cikin filayen haikali. 3Da ya ga Bitrus da Yohanna suna gab da shiga, sai ya roƙe su kuɗi. 4Bitrus kuwa ya kafa masa ido, haka ma Yohanna. Sai Bitrus ya ce, “Dube mu!” 5Saboda haka mutumin ya mai da hankalinsa a kansu, yana fata samun wani abu daga gare su.

6Sai Bitrus ya ce, “Azurfa ko zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, shi zan ba ka. A cikin sunan Yesu Kiristi Banazare, ka yi tafiya.” 7Ta wurin kama hannunsa na dama, ya taimake shi ya miƙe, nan take ƙafafu da idon sawun mutumin suka yi ƙarfi. 8Sai ya yi wuf da ƙafafunsa ya fara tafiya. Ya tafi tare da su ya shiga cikin filin haikali yana tafiya yana tsalle, yana kuma yabon Allah. 9Sa’ad da dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana yabon Allah, 10sai suka gane cewa shi ne mutumin nan wanda dā yake zama yana bara a bakin ƙofar haikalin da ake kira Kyakkyawa, suka kuwa cika da mamaki da tsoro a kan abin da ya faru gare shi.

Bitrus ya yi wa masu kallo magana

11Tun mai bawan yana riƙe da Bitrus da Yohanna, dukan mutanen suka yi mamaki, suka zo wurinsu a guje a inda ake kira Shirayin Solomon. 12Da Bitrus ya ga haka, sai ya ce musu, “Mutanen Isra’ila, don me wannan ya ba ku mamaki? Don me kuke kallonmu sai ka ce da ikon kanmu ne ko kuwa don ibadarmu ne muka sa wannan mutum ya yi tafiya? 13Allah na Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub, Allah na kakanninmu, ya ɗaukaka bawansa Yesu. Ku kuka ba da shi domin a kashe, kuka yi mūsun saninsa a gaban Bilatus, ko da yake ya yi niyya ya sake shi. 14Kuka yi mūsun sanin Mai Tsarki da Mai Adalci kuka roƙa a sakar muku mai kisankai. 15Kuka kashe tushen rai, amma Allah ya tashe shi daga matattu. Mu shaidu ne ga wannan. 16Ta wurin bangaskiya cikin sunan Yesu ne wannan mutum da kuke gani kuka kuma sani ya sami ƙarfi. Da sunan Yesu, da kuma bangaskiyar da take samuwa ta wurinsa ne ya ba shi cikakkiyar warkarwa, yadda dukanku kuke gani.

17“To, ’yan’uwa, na san cewa, kun aikata wannan cikin jahilci ne, yadda shugabanninku suka yi. 18Amma ta haka ne Allah ya cika abin da ya rigyafaɗi ta bakin dukan annabawa cewa, Kiristinsa zai sha wahala. 19Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokutan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji, 20don kuma ya iya aika da Kiristi, wanda aka naɗa tun dā saboda ku, Yesu ke nan. 21Dole yă kasance a sama, sai lokaci ya yi da Allah zai mai da kome sabo, yadda ya yi alkawari tun dā ta wurin annabawansa masu tsarki. 22Gama Musa ya ce, ‘Ubangiji Allahnku zai tasar muku wani annabi kamar ni daga cikin mutanenku; dole ku saurari duk abin da ya faɗa muku. 23Duk wanda bai saurare shi ba za a ware shi gaba ɗaya daga mutanensa.’3.23 M Sh 18.15,18,19

24“Tabbatacce, dukan annabawa daga Sama’ila zuwa gaba, dukansu da suka yi magana, sun rigya faɗin waɗannan kwanaki. 25Ku kuwa magādan annabawan ne da kuma na alkawarin da Allah ya yi da kakanninku. Ya ce wa Ibrahim, ‘Ta wurin zuriyarka, dukan kabilan duniya za su sami albarka.’3.25 Far 22.18; Far 26.4 26Da Allah ya tashe bawansa, ya aike shi da fari zuwa gare ku don yă albarkace ku ta wurin juye kowannenku daga mugayen hanyoyinku.”