King James Version

Acts 28:1-31

1And when they were escaped, then they knew that the island was called Melita. 2And the barbarous people shewed us no little kindness: for they kindled a fire, and received us every one, because of the present rain, and because of the cold. 3And when Paul had gathered a bundle of sticks, and laid them on the fire, there came a viper out of the heat, and fastened on his hand. 4And when the barbarians saw the venomous beast hang on his hand, they said among themselves, No doubt this man is a murderer, whom, though he hath escaped the sea, yet vengeance suffereth not to live. 5And he shook off the beast into the fire, and felt no harm. 6Howbeit they looked when he should have swollen, or fallen down dead suddenly: but after they had looked a great while, and saw no harm come to him, they changed their minds, and said that he was a god.

7In the same quarters were possessions of the chief man of the island, whose name was Publius; who received us, and lodged us three days courteously. 8And it came to pass, that the father of Publius lay sick of a fever and of a bloody flux: to whom Paul entered in, and prayed, and laid his hands on him, and healed him. 9So when this was done, others also, which had diseases in the island, came, and were healed: 10Who also honoured us with many honours; and when we departed, they laded us with such things as were necessary.

11And after three months we departed in a ship of Alexandria, which had wintered in the isle, whose sign was Castor and Pollux. 12And landing at Syracuse, we tarried there three days. 13And from thence we fetched a compass, and came to Rhegium: and after one day the south wind blew, and we came the next day to Puteoli: 14Where we found brethren, and were desired to tarry with them seven days: and so we went toward Rome. 15And from thence, when the brethren heard of us, they came to meet us as far as Appii forum, and The three taverns: whom when Paul saw, he thanked God, and took courage. 16And when we came to Rome, the centurion delivered the prisoners to the captain of the guard: but Paul was suffered to dwell by himself with a soldier that kept him.

17And it came to pass, that after three days Paul called the chief of the Jews together: and when they were come together, he said unto them, Men and brethren, though I have committed nothing against the people, or customs of our fathers, yet was I delivered prisoner from Jerusalem into the hands of the Romans. 18Who, when they had examined me, would have let me go, because there was no cause of death in me. 19But when the Jews spake against it, I was constrained to appeal unto Cæsar; not that I had ought to accuse my nation of. 20For this cause therefore have I called for you, to see you, and to speak with you: because that for the hope of Israel I am bound with this chain. 21And they said unto him, We neither received letters out of Judæa concerning thee, neither any of the brethren that came shewed or spake any harm of thee. 22But we desire to hear of thee what thou thinkest: for as concerning this sect, we know that every where it is spoken against. 23And when they had appointed him a day, there came many to him into his lodging; to whom he expounded and testified the kingdom of God, persuading them concerning Jesus, both out of the law of Moses, and out of the prophets, from morning till evening. 24And some believed the things which were spoken, and some believed not. 25And when they agreed not among themselves, they departed, after that Paul had spoken one word, Well spake the Holy Ghost by Esaias the prophet unto our fathers, 26Saying, Go unto this people, and say, Hearing ye shall hear, and shall not understand; and seeing ye shall see, and not perceive: 27For the heart of this people is waxed gross, and their ears are dull of hearing, and their eyes have they closed; lest they should see with their eyes, and hear with their ears, and understand with their heart, and should be converted, and I should heal them. 28Be it known therefore unto you, that the salvation of God is sent unto the Gentiles, and that they will hear it. 29And when he had said these words, the Jews departed, and had great reasoning among themselves.

30And Paul dwelt two whole years in his own hired house, and received all that came in unto him, 31Preaching the kingdom of God, and teaching those things which concern the Lord Jesus Christ, with all confidence, no man forbidding him.

Hausa Contemporary Bible

Ayyukan Manzanni 28:1-31

Tsibirin Malta

1Bayan da muka kai bakin tekun lafiya, sai muka tarar cewa sunan tsibirin Malta ne. 2Mutanen tsibirin kuwa suka nuna mana babban alheri. Suka hura wuta suka marabce mu duka saboda ana ruwan sama da kuma sanyi. 3Bulus ya tattara tarin itace, yayinda kuma yake sa itacen a wuta, sai maciji ya ɓullo saboda zafi, ya dāfe a hannunsa. 4Da mutanen tsibirin suka ga macijin yana lilo a hannunsa, sai suka ce wa juna “Lalle, wannan mutum mai kisankai ne; gama ko da yake ya tsira daga teku, Adalci bai bar shi ya rayu ba.” 5Amma Bulus ya karkaɗe macijin a cikin wuta, bai kuwa ji wani ciwo ba. 6Mutanen kuma suka yi zato zai kumbura ko kuma nan da nan zai fāɗi matacce, amma da aka daɗe ba su ga wani abu ya faru da shi ba, sai suka sāke ra’ayi suka ce shi wani allah ne.

7Akwai wani filin nan kusa wanda yake na Fubiliyus, babban shugaban tsibirin. Shi ne ya karɓe mu a gidansa da alheri ya kuma ciyar da mu har kwana uku. 8Mahaifinsa kuwa yana kwanciya a gado yana fama da zazzaɓi da atuni. Bulus ya shiga ciki don yă gan shi, bayan ya yi masa addu’a, sai ya ɗibiya masa hannuwa ya warkar da shi. 9Sa’ad da wannan ya faru, sauran marasa lafiya a tsibirin suka zo aka kuma warkar da su. 10Suka girmama mu ta kowane hali da muka shirya za mu tashi, sai suka ba mu abubuwan da muke bukata.

Isowa a Roma

11Bayan wata uku sai muka tashi a wani jirgin ruwan da ya ci damina a tsibirin. Jirgin ruwa kuwa na Alekzandariya ne yana da siffar tagwayen allolin Kasto da Follus. 12Muka isa Sirakus a can muka yi kwana uku. 13Daga can muka tashi muka isa Regiyum. Kashegari iskar kudu ta taso, kashegari kuma muka kai Futeyoli. 14A can muka tarar da waɗansu ’yan’uwa waɗanda suka gayyaci mu mu yi mako ɗaya da su. Da haka dai muka kai Roma. 15’Yan’uwan da suke can sun sami labari cewa muna zuwa, sai suka tashi tun daga Kasuwar Affiyus da Masauƙi Uku don su tarye mu. Da ganin mutanen nan sai Bulus ya gode wa Allah ya kuma sami ƙarfafawa. 16Da muka isa Roma, sai aka yarda wa Bulus yă zauna shi kaɗai, tare da sojan da zai yi gadinsa.

Bulus ya yi wa’azi a Roma a tsare

17Bayan kwana uku sai ya kira taron shugabannin Yahudawa. Da suka taru, Bulus ya ce musu, “’Yan’uwana, ko da yake ban yi wa mutanenmu wani laifi ba ko kuma wani abu game da al’adun kakanninmu, aka kama ni a Urushalima aka kuma ba da ni ga Romawa. 18Suka tuhume ni suka kuma so su sake ni, domin ba a same ni da wani laifin da ya cancanci kisa ba. 19Amma da Yahudawa suka ƙi, sai ya zama mini dole in ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba don ina da wani zargin da zan kawo game da mutanena ba. 20Saboda wannan ne na nemi in gan ku in kuma yi magana da ku. Saboda begen Isra’ila ne, nake a daure da wannan sarƙa.”

21Suka amsa cewa, “Ba mu sami wani wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, kuma ba kowa daga cikin ’yan’uwan da suka zo daga can ya kawo wani labari ko ya faɗi wani mummuna abu game da kai. 22Amma muna so mu ji ra’ayinka, gama mun san cewa mutane ko’ina suna muguwar magana a kan wannan ɗarikar.”

23Suka shirya su sadu da Bulus wata rana, suka ma zo da yawa fiye da dā a wurin da Bulus yake zama. Daga safe har zuwa yamma ya yi ta yin musu bayani, ya kuma shaida musu mulkin Allah yana ƙoƙarin rinjayarsu game da Yesu daga Dokar Musa da kuma daga Annabawa. 24Waɗansu suka rinjayu da abin da ya faɗa, amma waɗansu suka ba su gaskata ba. 25Suka kāsa yarda da juna suka fara watsewa bayan Bulus ya yi wannan magana guda cewa, “Ruhu Mai Tsarki ya faɗa wa kakannin-kakanninku gaskiya sa’ad da ya ce ta bakin annabi Ishaya cewa,

26“ ‘Je ka wurin mutanen nan ka ce,

“Za ku yi ta ji amma ba za ku fahimta ba;

za ku yi ta dubawa, amma ba za ku gani ba.”

27Gama zuciyar mutanen nan ta yi tauri;

da ƙyar suke ji da kunnuwansu,

sun kuma rufe idanunsu.

In ba haka ba za su iya gani da idanunsu,

su ji da kunnuwansu,

su fahimta a zukatansu,

su kuma juyo, in kuwa warkar da su.’28.27 Ish 6.9,10

28“Saboda haka na so ku san cewa an aika da ceton Allah ga Al’ummai, za su kuwa saurara!”28.28 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da saurara! 29 Bayan ya faɗi haka, sai Yahudawa suka watse, suna gardama mai zafi a tsakaninsu

30Shekaru biyu cif Bulus ya zauna a can a gidansa na haya yana marabtar duk wanda ya je wurinsa. 31Ya yi wa’azin mulkin Allah yana kuma koyarwa game da Ubangiji Yesu Kiristi, gabagadi ba tare da wani abu ya hana shi ba.