Acts 22 – NIV & HCB

New International Version

Acts 22:1-30

1“Brothers and fathers, listen now to my defense.”

2When they heard him speak to them in Aramaic, they became very quiet.

Then Paul said: 3“I am a Jew, born in Tarsus of Cilicia, but brought up in this city. I studied under Gamaliel and was thoroughly trained in the law of our ancestors. I was just as zealous for God as any of you are today. 4I persecuted the followers of this Way to their death, arresting both men and women and throwing them into prison, 5as the high priest and all the Council can themselves testify. I even obtained letters from them to their associates in Damascus, and went there to bring these people as prisoners to Jerusalem to be punished.

6“About noon as I came near Damascus, suddenly a bright light from heaven flashed around me. 7I fell to the ground and heard a voice say to me, ‘Saul! Saul! Why do you persecute me?’

8“ ‘Who are you, Lord?’ I asked.

‘I am Jesus of Nazareth, whom you are persecuting,’ he replied. 9My companions saw the light, but they did not understand the voice of him who was speaking to me.

10“ ‘What shall I do, Lord?’ I asked.

‘Get up,’ the Lord said, ‘and go into Damascus. There you will be told all that you have been assigned to do.’ 11My companions led me by the hand into Damascus, because the brilliance of the light had blinded me.

12“A man named Ananias came to see me. He was a devout observer of the law and highly respected by all the Jews living there. 13He stood beside me and said, ‘Brother Saul, receive your sight!’ And at that very moment I was able to see him.

14“Then he said: ‘The God of our ancestors has chosen you to know his will and to see the Righteous One and to hear words from his mouth. 15You will be his witness to all people of what you have seen and heard. 16And now what are you waiting for? Get up, be baptized and wash your sins away, calling on his name.’

17“When I returned to Jerusalem and was praying at the temple, I fell into a trance 18and saw the Lord speaking to me. ‘Quick!’ he said. ‘Leave Jerusalem immediately, because the people here will not accept your testimony about me.’

19“ ‘Lord,’ I replied, ‘these people know that I went from one synagogue to another to imprison and beat those who believe in you. 20And when the blood of your martyr22:20 Or witness Stephen was shed, I stood there giving my approval and guarding the clothes of those who were killing him.’

21“Then the Lord said to me, ‘Go; I will send you far away to the Gentiles.’

Paul the Roman Citizen

22The crowd listened to Paul until he said this. Then they raised their voices and shouted, “Rid the earth of him! He’s not fit to live!”

23As they were shouting and throwing off their cloaks and flinging dust into the air, 24the commander ordered that Paul be taken into the barracks. He directed that he be flogged and interrogated in order to find out why the people were shouting at him like this. 25As they stretched him out to flog him, Paul said to the centurion standing there, “Is it legal for you to flog a Roman citizen who hasn’t even been found guilty?”

26When the centurion heard this, he went to the commander and reported it. “What are you going to do?” he asked. “This man is a Roman citizen.”

27The commander went to Paul and asked, “Tell me, are you a Roman citizen?”

“Yes, I am,” he answered.

28Then the commander said, “I had to pay a lot of money for my citizenship.”

“But I was born a citizen,” Paul replied.

29Those who were about to interrogate him withdrew immediately. The commander himself was alarmed when he realized that he had put Paul, a Roman citizen, in chains.

Paul Before the Sanhedrin

30The commander wanted to find out exactly why Paul was being accused by the Jews. So the next day he released him and ordered the chief priests and all the members of the Sanhedrin to assemble. Then he brought Paul and had him stand before them.

Hausa Contemporary Bible

Ayyukan Manzanni 22:1-30

1“’Yan’uwa da iyaye, ku saurari kāriyata yanzu.”

2Da suka ji ya yi musu magana da Arameyik, sai suka yi tsit.

Sai Bulus ya ce, 3“Ni mutumin Yahuda ne haifaffen Tarshish na Silisiya, amma a nan birnin ne aka rene ni. Aka horar da ni sosai cikin dokokin kakanninmu a ƙarƙashin Gamaliyel ni ma dā mai himma ne cikin bauta wa Allah kamar yadda kowannenku yake a yau. 4Na tsananta wa masu bin wannan Hanyar har ga mutuwarsu, ina kama maza da mata ina kuma jefa su cikin kurkuku, 5kamar yadda babban firist da dukan Majalisa za su iya shaida. Na ma karɓi wasiƙu daga gare su zuwa ga ’yan’uwansu a Damaskus, na kuma tafi can don in kawo waɗannan mutane a daure zuwa Urushalima don a hukunta su.

6“Wajen tsakar rana da na yi kusa da Damaskus, ba zato ba tsammani sai wani babban haske daga sama ya haskaka kewaye da ni. 7Sai na fāɗi a ƙasa na kuma ji wata murya ta ce mini, ‘Shawulu! Shawulu! Don me kake tsananta mini?’

8“Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’

“Ya amsa ya ce, ‘Ni ne Yesu Banazare, wanda kake tsanantawa.’ 9Abokan tafiyata suka ga hasken, amma ba su fahimci muryar mai magana da ni ba.

10“Sai na yi tambaya, na ce, ‘Me zan yi, ya Ubangiji?’

“Ubangiji ya ce, ‘Tashi, ka tafi cikin Damaskus. A can za a faɗa maka duk abin da aka shirya za ka yi.’ 11Abokan tafiyata suka ja ni a hannu zuwa cikin Damaskus, saboda ƙarfin hasken ya makanta ni.

12“Wani mutumin da ake kira Ananiyas ya zo ya gan ni. Shi mai ibada ne wajen kiyaye dokoki wanda dukan Yahudawan da suke zama a can suna girmama shi ƙwarai. 13Ya tsaya kusa da ni ya ce, ‘Ɗan’uwa Shawulu, ka sami ganin garinka!’ A daidai lokacin kuwa na iya ganinsa.

14“Sa’an nan ya ce, ‘Allah na kakanninmu ya zaɓe ka ka san nufinsa ka kuma ga Mai Adalcin nan ka kuma ji kalmomi daga bakinsa. 15Za ka zama mai shaidarsa ga dukan mutane game da abin da ka gani ka kuma ji. 16Yanzu me kake jira? Ka tashi, a yi maka baftisma, a wanke zunubanka, ta wurin kira bisa ga sunansa.’

17“Sa’ad da na dawo Urushalima ina cikin addu’a a haikali, sai na ga wahayi 18na ga Ubangiji yana magana. Ya ce mini, ‘Maza! Ka bar Urushalima, gama ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.’

19“Na amsa na ce, ‘Ubangiji, waɗannan mutane sun san cewa na bi majami’a-majami’a na jefa waɗanda suka gaskata da kai a cikin kurkuku, in kuma yin musu dūka. 20Sa’ad da kuma aka zub da jinin Istifanus mashaidinka, na tsaya can ina ba da goyon bayana ina kuma tsaron tufafin masu kisansa.’

21“Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, ‘Je ka; zan aike ka can nesa a wurin Al’ummai.’ ”

Bulus ɗan ƙasar Roma

22Taron suka saurari Bulus sai da ya yi wannan magana. Sa’an nan suka ɗaga muryoyinsu suka yi ihu suka ce, “A raba duniya da wannan mutum! Bai cancanci yă rayu ba!”

23Da suna ihu suna kaɗa mayafansu suna da tā da ƙura sama, 24sai shugaban ƙungiyar sojan ya umarta a kai Bulus a barikin soja. Ya ba da umarni a yi masa bulala a kuma tambaye shi abin da ya sa mutane suke masa ihu haka. 25Suna kwantar da shi ke nan domin a yi masa bulala, sai Bulus ya ce wa jarumin da yake tsaye a nan, “Ashe, daidai ne bisa ga doka a yi wa ɗan ƙasar Roma bulala wanda ba a ma tabbatar da laifi a kansa ba?”

26Da jarumin ya ji haka sai ya je wurin shugaban ƙungiyar sojan ya ce masa, “Me kake so yi ne? Wannan mutum ɗan ƙasar Roma ne.”

27Sai shugaban ƙungiyar sojan ya je ya tambayi Bulus ya ce, “Faɗa mini, kai ɗan ƙasar Roma ne?”

Bulus ya ce, “I.”

28Sai shugaban ƙungiyar sojan ya ce, “Sai da na biya kuɗi mai yawa kafin in zama ɗan ƙasa.”

Bulus ya ce, “Ni kuwa an haife ni ɗan ƙasa.”

29Waɗanda dā suke shirin yin masa tambayoyi suka ja da baya nan da nan. Shugaban ƙungiyar sojan kansa ya tsorata da ya fahimci cewa ya sa wa Bulus, ɗan ƙasar Roma sarƙa.

A gaban majalisa

30Kashegari da yake shugaban ƙungiyar sojan ya so yă tabbatar da ainihin abin da ya sa Yahudawa suke zargin Bulus, sai ya sake shi ya kuwa umarci manyan firistoci da dukan Majalisar su taru. Sa’an nan ya kawo Bulus ya sa ya tsaya a gabansu.