King James Version

2 Corinthians 6:1-18

1We then, as workers together with him, beseech you also that ye receive not the grace of God in vain. 2(For he saith, I have heard thee in a time accepted, and in the day of salvation have I succoured thee: behold, now is the accepted time; behold, now is the day of salvation.) 3Giving no offence in any thing, that the ministry be not blamed: 4But in all things approving ourselves as the ministers of God, in much patience, in afflictions, in necessities, in distresses, 5In stripes, in imprisonments, in tumults, in labours, in watchings, in fastings; 6By pureness, by knowledge, by longsuffering, by kindness, by the Holy Ghost, by love unfeigned, 7By the word of truth, by the power of God, by the armour of righteousness on the right hand and on the left, 8By honour and dishonour, by evil report and good report: as deceivers, and yet true; 9As unknown, and yet well known; as dying, and, behold, we live; as chastened, and not killed; 10As sorrowful, yet alway rejoicing; as poor, yet making many rich; as having nothing, and yet possessing all things.

11O ye Corinthians, our mouth is open unto you, our heart is enlarged. 12Ye are not straitened in us, but ye are straitened in your own bowels. 13Now for a recompence in the same, (I speak as unto my children,) be ye also enlarged. 14Be ye not unequally yoked together with unbelievers: for what fellowship hath righteousness with unrighteousness? and what communion hath light with darkness? 15And what concord hath Christ with Belial? or what part hath he that believeth with an infidel? 16And what agreement hath the temple of God with idols? for ye are the temple of the living God; as God hath said, I will dwell in them, and walk in them; and I will be their God, and they shall be my people. 17Wherefore come out from among them, and be ye separate, saith the Lord, and touch not the unclean thing; and I will receive you, 18And will be a Father unto you, and ye shall be my sons and daughters, saith the Lord Almighty.

Hausa Contemporary Bible

2 Korintiyawa 6:1-18

1A matsayinmu na abokan aikin Allah, muna roƙonku kada ku karɓi alherin Allah a banza. 2Gama ya ce,

“A lokacin samun alherina, na ji ka,

a ranar samun ceto kuma, na taimake ka.”6.2 Ish 49.8

Ina gaya muku, yanzu ne lokacin samun alherin Allah, yanzu ne ranar samun ceto.

Wahalolin Bulus

3Ba ma sa abin tuntuɓe wa kowa, domin kada hidimarmu ta zama abin zargi. 4A maimakon haka, duk abin da muke yi, muna yin shi ne don mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne. Muna yin haka cikin jimrewa, da shan wahala, da shan wuya, har da shan masifu. 5Da shan dūka, da shan dauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rashin barci, da kuma yunwa. 6Da cikin tsarki, da fahimta, da haƙuri, da kirki, da cikin Ruhu Mai Tsarki, da cikin ƙauna mai gaskiya, 7da cikin magana mai gaskiya, da kuma cikin ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu, 8ta wurin ɗaukaka da ƙasƙanci, da cikin ɓata suna, da kuma cikin yabo. Cikin faɗin gaskiya, an ɗauke mu masu ƙarya, 9mu sanannu ne, duk da haka an ɗauke mu kamar ba a san mu ba, muna mutuwa, duk da haka a raye muke, an ba mu horo, duk da haka ba a kashe mu ba, 10cikin baƙin ciki, duk da haka kullum cikin murna muke. Cikin matalauta, duk da haka muna azurtar da mutane da yawa. Ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.

11Ya ku Korintiyawa, mun yi muku magana a sake, muka kuma saki zuciya da ku ƙwarai. 12Ba mu ƙi nuna muku ƙaunarmu ba, sai dai ku kuka ƙi nuna mana. 13A wannan zance kam, ina magana da ku kamar ’ya’yana, ku ma ku saki zuciya da mu.

Kada ku haɗa kai da marasa bi

14Kada ku haɗa kai da marasa bi. Gama me ya haɗa adalci da mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu? 15Wace daidaituwa ce tsakanin Kiristi da Iblis? Me ya haɗa mai bi da marar bi? 16Wane alkawari ne tsakanin haikalin Allah da na gumaka? Gama mu haikalin Allah mai rai ne. Kamar yadda Allah ya ce,

“Zan zauna tare da su,

in yi tafiya a cikinsu,

zan zama Allahnsu,

su kuma za su zama mutanena.”6.16 Fir 26.12; Irm 32.38; Ezk 37.27

17Saboda haka,

“Sai ku fito daga cikinsu,

ku keɓe kanku,

in ji Ubangiji.

Kada ku taɓa wani abu marar tsabta,

zan kuma karɓe ku.”6.17 Ish 52.11; Ezk 20.34,41

18Kuma,

“Zan zama Uba a gare ku,

ku kuma za ku zama ’ya’yana, maza da mata,

in ji Ubangiji Maɗaukaki.”6.18 2Sam 7.14; 2Sam 7.8