King James Version

2 Corinthians 3:1-18

1Do we begin again to commend ourselves? or need we, as some others, epistles of commendation to you, or letters of commendation from you? 2Ye are our epistle written in our hearts, known and read of all men: 3Forasmuch as ye are manifestly declared to be the epistle of Christ ministered by us, written not with ink, but with the Spirit of the living God; not in tables of stone, but in fleshy tables of the heart.

4And such trust have we through Christ to God-ward: 5Not that we are sufficient of ourselves to think any thing as of ourselves; but our sufficiency is of God; 6Who also hath made us able ministers of the new testament; not of the letter, but of the spirit: for the letter killeth, but the spirit giveth life. 7But if the ministration of death, written and engraven in stones, was glorious, so that the children of Israel could not stedfastly behold the face of Moses for the glory of his countenance; which glory was to be done away: 8How shall not the ministration of the spirit be rather glorious? 9For if the ministration of condemnation be glory, much more doth the ministration of righteousness exceed in glory. 10For even that which was made glorious had no glory in this respect, by reason of the glory that excelleth. 11For if that which is done away was glorious, much more that which remaineth is glorious. 12Seeing then that we have such hope, we use great plainness of speech: 13And not as Moses, which put a vail over his face, that the children of Israel could not stedfastly look to the end of that which is abolished: 14But their minds were blinded: for until this day remaineth the same vail untaken away in the reading of the old testament; which vail is done away in Christ. 15But even unto this day, when Moses is read, the vail is upon their heart. 16Nevertheless when it shall turn to the Lord, the vail shall be taken away. 17Now the Lord is that Spirit: and where the Spirit of the Lord is, there is liberty. 18But we all, with open face beholding as in a glass the glory of the Lord, are changed into the same image from glory to glory, even as by the Spirit of the Lord.

Hausa Contemporary Bible

2 Korintiyawa 3:1-18

1Yabon kanmu ne kuma muka fara yi? Ko kuwa muna bukatar wasiƙun yabo ne zuwa gare ku, ko daga gare ku, kamar yadda waɗansu suke yi? 2Ai, ku kanku ku ne wasiƙarmu, wadda aka rubuta a zukatanku, domin kowa yă santa, yă kuma karanta ta. 3Kun nuna cewa ku wasiƙa ce daga Kiristi, sakamakon hidimarmu, ba wadda aka rubuta da inki ba, sai dai da Ruhun Allah mai rai. Ba kuma a kan allunan dutse ba, sai dai a kan allunan zukatan mutane.

4Amincewa kamar wannan shi ne namu ta wurin Kiristi a gaban Allah. 5Ba mu da wani abin da za mu nuna cewa da iyawarmu ne muke aikin nan. Iyawarmu daga wurin Allah ne. 6Shi ya sa muka gwaninta a matsayinmu na masu hidimar sabon alkawari ba ta rubutacciyar Dokar ba, amma ta Ruhu; don Dokar, kisa take yi, Ruhu kuwa yana ba da rai.

Ɗaukakar sabon alkawari

7To, in hidimar da ta kawo mutuwa, wadda an rubuta a kan allon dutse, ta zo da ɗaukaka har Isra’ilawa suka kāsa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta, ko da yake mai shuɗewa ce, 8ashe, hidimar Ruhu ba za tă fi wannan ɗaukaka ba? 9In hidimar da take jawo wa mutane hukunci tana da ɗaukaka haka, to, lalle, hidimar da take kawo adalci za tă fi ta ɗaukaka nesa! 10Gama abin da dā take da ɗaukaka, ba ta da ɗaukaka a yanzu, in aka kwatantata da mafificiyar ɗaukaka ta yanzu. 11In kuma aba mai shuɗewa ta zo da ɗaukaka, ashe, abin da yake dawwammame, lalle ne yă kasance da ɗaukakar da ta fi haka nesa!

12Da yake muna da bege irin wannan, to, muna da ƙarfin zuciya sosai ke nan. 13Mu ba kamar Musa ba ne, wanda ya rufe fuskarsa da lulluɓi, don kada Isra’ilawa su ga ƙarewar ɗaukakan nan mai shuɗewa. 14Amma aka sa hankulansu suka dushe, gama har yă zuwa yau akwai lulluɓin nan a duk sa’ad da ake karatun tsohon alkawari. Ba a kawar da shi ba, sai a cikin Kiristi ne kaɗai ake kawar da shi. 15Har yă zuwa yau, duk sa’ad da ake karatun littattafan Musa, lulluɓin nan yakan rufe zukatansu. 16Amma duk sa’ad da wani ya juyo ga Ubangiji, akan kawar da lulluɓin. 17Ubangiji fa, shi ne Ruhu, kuma duk inda Ruhun Ubangiji yake, a nan ’yanci yake. 18Mu da ba mu da lulluɓi a fuskokinmu duk muna nuna ɗaukakar Ubangiji, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa. Ubangiji wanda yake ruhu kuwa shi ne mai zartar da haka.