King James Version

1 Peter 3:1-22

1Likewise, ye wives, be in subjection to your own husbands; that, if any obey not the word, they also may without the word be won by the conversation of the wives; 2While they behold your chaste conversation coupled with fear. 3Whose adorning let it not be that outward adorning of plaiting the hair, and of wearing of gold, or of putting on of apparel; 4But let it be the hidden man of the heart, in that which is not corruptible, even the ornament of a meek and quiet spirit, which is in the sight of God of great price. 5For after this manner in the old time the holy women also, who trusted in God, adorned themselves, being in subjection unto their own husbands: 6Even as Sara obeyed Abraham, calling him lord: whose daughters ye are, as long as ye do well, and are not afraid with any amazement. 7Likewise, ye husbands, dwell with them according to knowledge, giving honour unto the wife, as unto the weaker vessel, and as being heirs together of the grace of life; that your prayers be not hindered. 8Finally, be ye all of one mind, having compassion one of another, love as brethren, be pitiful, be courteous: 9Not rendering evil for evil, or railing for railing: but contrariwise blessing; knowing that ye are thereunto called, that ye should inherit a blessing. 10For he that will love life, and see good days, let him refrain his tongue from evil, and his lips that they speak no guile: 11Let him eschew evil, and do good; let him seek peace, and ensue it. 12For the eyes of the Lord are over the righteous, and his ears are open unto their prayers: but the face of the Lord is against them that do evil.

13And who is he that will harm you, if ye be followers of that which is good? 14But and if ye suffer for righteousness’ sake, happy are ye: and be not afraid of their terror, neither be troubled; 15But sanctify the Lord God in your hearts: and be ready always to give an answer to every man that asketh you a reason of the hope that is in you with meekness and fear: 16Having a good conscience; that, whereas they speak evil of you, as of evildoers, they may be ashamed that falsely accuse your good conversation in Christ. 17For it is better, if the will of God be so, that ye suffer for well doing, than for evil doing. 18For Christ also hath once suffered for sins, the just for the unjust, that he might bring us to God, being put to death in the flesh, but quickened by the Spirit: 19By which also he went and preached unto the spirits in prison; 20Which sometime were disobedient, when once the longsuffering of God waited in the days of Noah, while the ark was a preparing, wherein few, that is, eight souls were saved by water. 21The like figure whereunto even baptism doth also now save us (not the putting away of the filth of the flesh, but the answer of a good conscience toward God,) by the resurrection of Jesus Christ: 22Who is gone into heaven, and is on the right hand of God; angels and authorities and powers being made subject unto him.

Hausa Contemporary Bible

1 Bitrus 3:1-22

Matan aure da mazan Aure

1Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba 2sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi. 3Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada. 4Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah. 5Gama haka matan masu tsarki na dā waɗanda suka sa begensu ga Allah suka yi wa kansu ado. Sun yi wa mazansu biyayya, 6kamar Saratu, wadda ta yi biyayya ga Ibrahim, har ta kira shi maigidanta. Ku ’ya’yanta ne mata in kun aikata abin da yake daidai, ba ku kuma ba tsoro dama ba.

7Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yă hana addu’o’inku.

Shan wahala saboda yin ayyuka alheri

8A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar ’yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u. 9Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi, sai dai ku sa albarka, gama ga wannan ne aka kira ku, ku kuma gāji albarka. 10Gama,

“Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa,

yă kuma ga kwanaki masu kyau

dole yă ƙame harshensa daga mugunta

leɓunansa kuma daga maganar yaudara.

11Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta;

dole yă nemi salama yă kuma bi ta.

12Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci

kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu,

amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”3.12 Zab 34.12-16

13Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta? 14Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.”3.14 Ish 8.12 15Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi, 16tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi. 17Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta. 18Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu, 19ta wurin wanda kuma ya tafi ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku wa’azi 20waɗanda dā ba su yi biyayya ba sa’ad da Allah ya jira da haƙuri a kwanaki Nuhu yayinda ake sassaƙa jirgi. A cikinsa mutane kima ne kawai, su takwas, aka kuɓutar ta ruwa, 21ruwan nan kuwa kwatancin baftisma ne da yanzu ya cece ku ku ma, ba kawar da dauda daga jiki ba, sai dai yin alkawari na lamiri mai kyau ga Allah. Ya cece ku ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, 22wanda ya tafi sama, yana kuma a hannun dama na Allah, mala’iku, mulkoki da kuma masu iko suna masa biyayya.