ज़करयाह 14 – HCV & HCB

Hindi Contemporary Version

ज़करयाह 14:1-21

याहवेह आकर राज्य करते हैं

1हे येरूशलेम, याहवेह का एक ऐसा दिन आनेवाला है, जब तुम्हारी संपत्ति लूट ली जाएगी और तुम्हारे अपने घेरे के अंदर ही बांट ली जाएगी.

2मैं जाति-जाति के लोगों को येरूशलेम के विरुद्ध युद्ध करने के लिए इकट्ठा करूंगा; शहर पर अधिकार कर लिया जाएगा, घर-द्वार लूट लिये जाएंगे, और स्त्रियों से बलात्कार किया जाएगा. शहर की आधी जनसंख्या बंधुआई में चली जाएगी, पर बचे लोग शहर में ही रहेंगे. 3तब याहवेह जाकर उन जातियों के विरुद्ध ऐसे लड़ेंगे जैसे वे युद्ध के दिन लड़ते हैं. 4उस दिन याहवेह येरूशलेम के पूर्व में जैतून पहाड़ पर जा खड़े होंगे, और जैतून पहाड़ पूर्व और पश्चिम दो भाग में बंट जाएगा और बीच में एक बड़ी घाटी बन जाएगी, जिससे आधा पहाड़ उत्तर की ओर तथा आधा पहाड़ दक्षिण की ओर हट जाएगा. 5तब तुम मेरी इस पहाड़ की घाटी से होकर भागोगे, क्योंकि यह घाटी आत्सल तक फैली होगी. तुम ऐसे भागोगे, जैसे तुम यहूदिया के राजा उज्जियाह के दिनों में हुए भूकंप के समय भागे थे. तब याहवेह मेरे परमेश्वर सब पवित्र लोगों के साथ आएंगे.

6उस दिन न तो सूर्य का प्रकाश होगा और न ही ठंडा, कुहरे से भरा अंधेरा. 7वह एक अतुलनीय दिन होगा—ऐसा दिन जिसे सिर्फ याहवेह ही जानते हैं—दिन और रात के बीच कोई अंतर न होगा. जब शाम होगी, तभी प्रकाश होगा.

8उस दिन जीवन का जल येरूशलेम से बह निकलेगा, इसमें का आधा पानी पूर्व से मृत सागर की ओर तथा आधा पानी पश्चिम से भूमध्य सागर की ओर बहेगा, और यह ग्रीष्मकाल और साथ ही साथ शीतकाल में भी बहता रहेगा.

9सारी पृथ्वी पर याहवेह ही राजा होंगे. उस दिन एक ही याहवेह होंगे, और सिर्फ उन्हीं का ही नाम होगा.

10सारी भूमि, गेबा से लेकर येरूशलेम के दक्षिण में रिम्मोन तक अराबाह के समान हो जाएगी. परंतु बिन्यामिन द्वार से लेकर पहले द्वार के लिए चिन्हित स्थान तक, तथा कोने के द्वार तक और हनानेल के मीनार से लेकर राजा के रसकुण्डों तक येरूशलेम को ऊंचा उठाया जाएगा, और यह अपने स्थान में बना रहेगा. 11लोग आकर इसमें बसेंगे; और यह फिर कभी नाश नहीं किया जाएगा. येरूशलेम सुरक्षित होगा.

12वे जनता, जिन्होंने येरूशलेम से युद्ध किया है, उन सब पर याहवेह ऐसी महामारी लायेंगे कि जब वे अपने पैरों पर खड़े ही होंगे तो उनका मांस सड़ जाएगा, उनकी आंखें उनके गोलकों में ही सड़ जाएंगी, और उनकी जीभ उनके मुंह में ही सड़ जाएगी. 13उस दिन याहवेह की ओर से लोगों में बड़े आतंक के साथ घबराहट फैलेगी. वे एक दूसरे को हाथ से पकड़कर एक दूसरे पर वार करेंगे. 14यहूदिया भी आकर येरूशलेम में लड़ेगा. आस-पास की सभी जनताओं की संपत्ति इकट्ठी की जाएगी—जिसमें बहुत सारा सोना, चांदी और कपड़ा होगा. 15घोड़ों, खच्चरों, ऊंटों, गधों और उन शिविरों में सब पशुओं पर भी इसी प्रकार की महामारी आ पड़ेगी.

16तब वे सब जनता, जिन्होंने येरूशलेम पर आक्रमण किया था, उनमें से बचे लोग हर साल येरूशलेम जाकर राजा, सर्वशक्तिमान याहवेह की आराधना करेंगे, और तंबुओं का त्योहार मनायेंगे. 17और यदि पृथ्वी के लोगों में से कोई भी राजा, सर्वशक्तिमान याहवेह की आराधना करने के लिये येरूशलेम नहीं जाएगा, तो उनके यहां वर्षा न होगी. 18यदि मिस्र के लोग आराधना और उत्सव में भाग लेने के लिये नहीं जाएंगे, तो उनके यहां भी वर्षा न होगी. याहवेह उन पर वह महामारी लायेगा, जो वह उन जनताओं पर लाता है, जो तंबुओं का उत्सव मनाने नहीं जाते हैं. 19यह मिस्र देश के लोगों की सजा और उन सब जनताओं की सजा होगी, जो तंबुओं का उत्सव मनाने नहीं जाते हैं.

20उस दिन घोड़ों की गर्दन में लटकी घण्टियों पर ये शब्द खुदे हुए होंगे, “याहवेह के लिए पवित्र,” और याहवेह के भवन में भोजन पकाने के बर्तन, वेदी के सामने रखे पवित्र कटोरों के समान होंगे. 21येरूशलेम और यहूदिया में हर एक बर्तन सर्वशक्तिमान याहवेह के लिये पवित्र होगा, और वे सब जो बलि चढ़ाने के लिए आएंगे, वे उन बर्तनों में से कुछ को लेंगे और उनमें पकायेंगे. और उस दिन सर्वशक्तिमान याहवेह के भवन में फिर कोई कनानी (व्यापारी) न होगा.

Hausa Contemporary Bible

Zakariya 14:1-21

Ubangiji zai zo yă yi mulki

1Ranar Ubangiji tana zuwa sa’ad da za a raba muku ganimar da aka washe daga gare ku.

2Zan tara dukan al’ummai su yaƙi Urushalima; za a ci birnin da yaƙi, za a washe gidaje, a kuma yi wa mata fyaɗe. Rabin birnin zai je bauta, amma ba za a kwashe sauran mutanen daga birnin ba.

3Sa’an nan Ubangiji zai fita yă yi yaƙi da waɗannan al’ummai, kamar yadda yake yaƙi a ranar yaƙi. 4A ranan nan ƙafafunsa za su tsaya a kan Dutsen Zaitun, gabas da Urushalima, za a kuma tsage Dutsen Zaitun kashi biyu daga gabas zuwa yamma, yă zama babban kwari, rabin dutsen zai matsa zuwa wajen arewa, rabi kuma zai matsa zuwa wajen kudu. 5Za ku gudu ta wajen kwarin dutsena, gama zai miƙe har zuwa Azel. Za ku gudu kamar yadda kuka guje wa girgizar ƙasa14.5 Ko kuwa 5 Za a tare kwarin dutsena a kuma miƙe shi har zuwa Azel. Za a tare shi yadda aka tare saboda girgizar ƙasa a kwanakin Uzziya sarkin Yahuda. Sa’an nan Ubangiji Allahna zai zo, tare da duk masu tsarki.

6A ranan nan ba za a kasance da haske ko sanyi ba, ko hazo mai duhu ba. 7Za tă zama rana ce ta musamman, ba yini ko dare, rana da take sananne ga Ubangiji. Sa’ad da yamma ta yi, za a yi haske.

8A ranan nan ruwan rai zai kwararo daga Urushalima, rabi zai gangara gabas zuwa teku14.8 Wato, Bahar Rum rabi kuma zai gangara yamma zuwa Bahar Rum,14.8 Wato, Bahar Maliya a damina da rani.

9Ubangiji zai sama sarki bisa dukan duniya. A ranan nan za a kasance da Ubangiji ɗaya, ba wani suna kuma sai nasa.

10Ƙasar gaba ɗaya daga Geba zuwa Rimmon, kudu da Urushalima, za tă zama kamar Araba. Amma Urushalima za tă kasance a wurinta, daga Ƙofar Benyamin zuwa sashen Ƙofa ta Farko, zuwa Ƙofar Kusurwa, daga kuma Hasumiyar Hananel zuwa wurin matsin ruwan inabin sarki. 11Za a zauna a cikinka; ba za a ƙara hallaka ta ba. Urushalima za tă zauna lafiya.

12Ga bala’in da Ubangiji zai bugi dukan al’umman da suka yi yaƙi da Urushalima. Fatar jikinsu za tă ruɓe tun suna tsaye a ƙafafunsu, idanunsu za su ruɓe a cikin kwarminsu, harsunansu kuma zai ruɓe a cikin bakunansu. 13A ranan nan Ubangiji zai sa maza su cika da tsoro ƙwarai. Kowane mutum zai kama hannun ɗan’uwansa, za su kai wa juna hari. 14Yahuda ma za tă yi yaƙi a Urushalima. Za a tattara dukiyar al’umman da suke kewaye, za a tara zinariya da azurfa masu yawan gaske tare da tufafi. 15Irin wannan bala’i zai auko wa dawakai da alfadarai, raƙuma da jakuna, da kuma dukan dabbobi a wannan sansani.

16Sa’an nan waɗanda suka tsira daga cikin al’umman da suka yaƙe Urushalima za su haura shekara-shekara su yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada, su kuma yi Bikin Tabanakul. 17In waɗansu mutanen da suke duniya ba su haura Urushalima suka yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. 18In mutanen Masar ba su haura sun yi sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. Ubangiji14.18 Ko kuwa sashe, sai Ubangiji zai kawo masu bala’in da ya aika wa al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba. 19Wannan ne zai zama hukuncin Masar da kuma na dukan al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba.

20A ranan nan za a rubuta TSARKI GA Ubangiji a jikin ƙararrawar dawakai, kuma tukwanen dahuwa a gidan Ubangiji za su zama kamar kwanoni masu tsarki a gaban bagade. 21Kowace tukunya a Urushalima da Yahuda za tă zama mai tsarki ga Ubangiji Maɗaukaki, kuma duk wanda ya zo don miƙa hadaya zai ɗauki waɗansu tukwane yă yi dahuwa da su. A ranan nan kuwa, ba Bakan’ane14.21 Ko kuwa mai ciniki da zai ƙara kasance a gidan Ubangiji Maɗaukaki.