Kira don komawa ga Ubangiji
1A wata na bakwai na shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.
2“Ubangiji ya yi fushi sosai da kakanninku. 3Saboda haka ka gaya wa mutanen, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku komo gare ni,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘ni kuma zan komo gare ku,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. 4Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na dā suka ce musu, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku juya daga mugayen hanyoyinku da mugayen abubuwan da kuke yi.’ Amma ba su saurara ba, ko ma su kula da ni, in ji Ubangiji. 5Yanzu ina kakanninku suke? Annabawan kuma fa, sun rayu har abada ne? 6Amma maganata da dokokina da na umarta ta wurin bayina annabawa fa, ashe, ba su tabbata ba a kan kakanninku?
“Sa’an nan suka tuba suka ce, ‘Ubangiji Maɗaukaki ya yi mana daidai abin da hanyoyinmu suka cancanci mu samu, kamar dai yadda ya yi niyya yi.’ ”
Mutumin a cikin itatuwan ci-zaƙi
77-8 A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato, watan Shebat, a shekara ta biyu ta Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.
8Da dare, na ga wahayi, a gabana kuwa ga mutum a kan jan doki! Yana tsaye a cikin itatuwa masu furanni, a bayansa a cikin itatuwan ci-zaƙi, a bayansa kuwa akwai dawakai masu ruwan ja, ruwan ƙasa-ƙasa da kuma ruwan fari.
9Sai na yi tambaya na ce, “Mene ne waɗannan ranka yă daɗe?”
Mala’ikan da yake magana da ni ya amsa ya ce, “Zan nuna maka mene ne su.”
10Sai mutumin da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin ya yi bayani cewa, “Su ne waɗanda Ubangiji ya aika ko’ina a duniya.”
11Sai suka ce wa mala’ikan da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin, “Mun ratsa ko’ina a duniya, sai muka ga duniya duka tana zaman lafiya.”
12Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Maɗaukaki, har yaushe za ka ci gaba da ƙi nuna wa Urushalima da kuma garuruwan Yahuda jinƙai, waɗanda kake fushi da su shekarun nan saba’in?” 13Sai Ubangiji ya yi wa mala’ikan da ya yi magana da ni magana da kalmomi masu daɗi da kuma masu ta’azantarwa.
14Sai mala’ikan da yake magana da ni ya ce, “Ka yi shelar maganan nan, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ina kishi domin Urushalima da Sihiyona, 15amma ina fushi da ƙasashen da suke ji suna zaman lafiya, na ɗan yi fushina kawai, amma sai suka ƙara musu masifar.’
16“Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Zan komo Urushalima da jinƙai, a can ne za a sāke gina gidana. Za a kuma miƙe ma’auni a bisa Urushalima,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
17“Ci gaba da yin shela, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Garuruwana za su sāke kwarara da wadata, Ubangiji kuma zai sāke yi wa Sihiyona ta’aziyya, yă kuma zaɓi Urushalima.’ ”
Ƙahoni huɗu da maƙera huɗu
18Sa’an nan na dubi sama a gabana kuwa sai ga ƙahoni huɗu! 19Na tambayi mala’ikan da yake mini magana, na ce, “Mene ne waɗannan?”
Ya amsa mini ya ce, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda, Isra’ila da kuma Urushalima.”
20Sa’an nan Ubangiji ya nuna mini maƙera guda huɗu. 21Na yi tambaya na ce, “Mene ne waɗannan suke zuwa yi?”
Ya amsa ya ce, “Waɗannan ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda har ba wanda yake iya ɗaga kansa, amma maƙeran sun zo don su tsorata su su kuma saukar da ƙahonin ƙasashen nan waɗanda suka ɗaga ƙahoninsu gāba da ƙasar Yahuda don su warwatsa ta.”
A Call to Return to the Lord
1In the eighth month of the second year of Darius, the word of the Lord came to the prophet Zechariah son of Berekiah, the son of Iddo:
2“The Lord was very angry with your ancestors. 3Therefore tell the people: This is what the Lord Almighty says: ‘Return to me,’ declares the Lord Almighty, ‘and I will return to you,’ says the Lord Almighty. 4Do not be like your ancestors, to whom the earlier prophets proclaimed: This is what the Lord Almighty says: ‘Turn from your evil ways and your evil practices.’ But they would not listen or pay attention to me, declares the Lord. 5Where are your ancestors now? And the prophets, do they live forever? 6But did not my words and my decrees, which I commanded my servants the prophets, overtake your ancestors?
“Then they repented and said, ‘The Lord Almighty has done to us what our ways and practices deserve, just as he determined to do.’ ”
The Man Among the Myrtle Trees
7On the twenty-fourth day of the eleventh month, the month of Shebat, in the second year of Darius, the word of the Lord came to the prophet Zechariah son of Berekiah, the son of Iddo.
8During the night I had a vision, and there before me was a man mounted on a red horse. He was standing among the myrtle trees in a ravine. Behind him were red, brown and white horses.
9I asked, “What are these, my lord?”
The angel who was talking with me answered, “I will show you what they are.”
10Then the man standing among the myrtle trees explained, “They are the ones the Lord has sent to go throughout the earth.”
11And they reported to the angel of the Lord who was standing among the myrtle trees, “We have gone throughout the earth and found the whole world at rest and in peace.”
12Then the angel of the Lord said, “Lord Almighty, how long will you withhold mercy from Jerusalem and from the towns of Judah, which you have been angry with these seventy years?” 13So the Lord spoke kind and comforting words to the angel who talked with me.
14Then the angel who was speaking to me said, “Proclaim this word: This is what the Lord Almighty says: ‘I am very jealous for Jerusalem and Zion, 15and I am very angry with the nations that feel secure. I was only a little angry, but they went too far with the punishment.’
16“Therefore this is what the Lord says: ‘I will return to Jerusalem with mercy, and there my house will be rebuilt. And the measuring line will be stretched out over Jerusalem,’ declares the Lord Almighty.
17“Proclaim further: This is what the Lord Almighty says: ‘My towns will again overflow with prosperity, and the Lord will again comfort Zion and choose Jerusalem.’ ”
Four Horns and Four Craftsmen
18Then I looked up, and there before me were four horns. 19I asked the angel who was speaking to me, “What are these?”
He answered me, “These are the horns that scattered Judah, Israel and Jerusalem.”
20Then the Lord showed me four craftsmen. 21I asked, “What are these coming to do?”
He answered, “These are the horns that scattered Judah so that no one could raise their head, but the craftsmen have come to terrify them and throw down these horns of the nations who lifted up their horns against the land of Judah to scatter its people.”1:21 In Hebrew texts 1:18-21 is numbered 2:1-4.