Zuwa ga ikkilisiya a Afisa
1“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Afisa, ka rubuta,
Waɗannan su ne kalmomi na wannan wanda yake riƙe da taurari bakwai a hannunsa na dama yana kuma tafiya a tsakanin alkukan fitilu bakwai na zinariya.
2Na san ayyukanka, faman aikinka da daurewarka. Na san cewa ba ka iya haƙuri da mugayen mutane, ka gwada waɗanda suke cewa su manzanni ne, alhali kuwa ba haka ba ne, ka kuwa tarar cewa su na ƙarya ne. 3Kai kam ka daure ka kuma jimre da wahala saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba.
4Duk da haka ina riƙe da wannan game da kai. Ka watsar da ƙaunarka ta farko. 5Ka tuna da matsayinka a dā kafin ka fāɗi! Ka tuba ka kuma yi ayyukan da ka yi da fari. In ba ka tuba ba, zan zo wajenka in ɗauke wurin ajiye fitilanka daga inda yake. 6Sai dai kana da wannan abu mai kyau. Ka ƙi ayyukan Nikolaitawa da ni ma nake ƙi.
7Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah.
Zuwa ga ikkilisiya a Simirna
8“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Simirna, ka rubuta,
Waɗannan su ne kalmomin wannan da yake na Farko da na Ƙarshe, wanda ya mutu ya kuma sāke tashi da rai.
9Na san wahalarka da kuma talaucinka, duk da haka kai mai arziki ne! Na san ɓata suna da waɗannan suke yi maka waɗannan da suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, su dai majami’ar Shaiɗan ne. 10Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.
11Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara mutuwa ta biyu ba za tă cuce shi ba ko kaɗan.
Zuwa ga ikkilisiya a Fergamum
12“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Fergamum, ka rubuta,
Waɗannan su ne kalmomin wannan wanda yake da takobi mai kaifi biyu.
13Na san inda kake da zama, inda Shaiɗan yana da gadon sarautarsa. Duk da haka ka riƙe sunana da gaske. Ba ka yi mūsun bangaskiyarka gare ni ba, har ma a kwanakin Antifas, amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a birninku, inda Shaiɗan yake zama.
14Duk da haka, ina da abubuwa kima game da kai. Kana da mutane a can waɗanda suke riƙe da koyarwar Bala’am, wanda ya koya wa Balak yă ja hankalin Isra’ilawa su yi zunubi ta wurin cin abincin da aka miƙa wa gumaka hadaya, su kuma yi fasikanci. 15Haka ma kana da waɗanda suke riƙe da koyarwar Nikolaitawa. 16Saboda haka ka tuba! In ba haka ba, zan zo wajenka ba da daɗewa ba in yaƙe su da takobin bakina.
17Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara zan ba shi kaɗan daga cikin ɓoyayyiyar Manna. Zan kuma ba shi farin dutse tare da sabon suna a rubuce a bisansa, sananne kawai ga mai karɓan dutsen.
Zuwa ga ikkilisiya a Tiyatira
18“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Tiyatira, ka rubuta,
Waɗannan su ne kalmomin Ɗan Allah, wanda idanunsa suna kama da harshen wuta wanda kuma ƙafafunsa suna kama da tagullar da aka goge.
19Na san ayyukanka, ƙaunarka da bangaskiyarka, hidimarka da daurewarka, kuma cewa kana yin abubuwa a yanzu fiye da abin da ka yi da farko.
20Duk da haka, ina da wannan game da kai. Kana haƙuri da matan nan Yezebel, wadda take kira kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta tana ɓad da bayina ga yin fasikanci suka kuma ci abincin da aka miƙa wa gumaka. 21Na ba ta lokaci tă tuba daga fasikancinta, amma ba ta da niyya. 22Don haka zan jefa ta a kan gadon wahala, zan kuma sa waɗanda suke zina da ita, su sha azaba ƙwarai, sai dai in sun tuba daga hanyoyinta. 23Zan kashe ’ya’yanta. Sa’an nan dukan ikkilisiyoyi za su san cewa ni ne mai bincika zukata da tunani, zan kuwa sāka wa kowannenku gwargwadon ayyukansa.
24Yanzu, ina ce wa sauranku da kuke a Tiyatira, ku da ba ku riƙe da koyarwarta ba kuma ba ku koyi abin da suke kira zurfafan asiran Shaiɗan, ‘Ba zan ƙara muku wani nauyi ba. 25Sai dai ku riƙe abin da kuke da shi har sai na zo.’
26Gare shi wanda ya ci nasara ya kuma aikata nufina har ƙarshe, zan ba shi iko a kan al’ummai. 27‘Zai yi mulki a kansu da sandar sarauta ta ƙarfe, zai farfashe su, kamar tukwanen yumɓu’2.27 Zab 2.9 kamar yadda na karɓi iko daga Ubana. 28Zan kuma ba shi tauraron asubahi. 29Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.