Farawa 1 – HCB & PCB Parallel Bible

Hausa Contemporary Bible

Farawa 1:1-31

Masomi

1A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. 2To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.

3Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske. 4Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu. 5Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan.

6Allah ya ce, “Bari sarari yă kasance tsakanin ruwaye domin yă raba ruwa da ruwa.” 7Saboda haka Allah ya yi sarari ya raba ruwan da yake ƙarƙashin sararin da ruwan da yake bisansa. Haka kuwa ya kasance. 8Allah ya kira sararin “sama.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyu ke nan.

9Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance. 10Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.

11Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance. 12Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau. 13Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta uku ke nan.

14Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru, 15bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance. 16Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari. 17Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya, 18su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 19Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan.

20Allah ya ce, “Bari ruwa yă cika da halittu masu rai, bari tsuntsaye kuma su tashi sama a bisa duniya a sararin sama.” 21Allah ya halicci manyan halittun teku, da kowane mai rai da abin da yake motsi a ruwa, bisa ga irinsu, da kuma kowane tsuntsu mai fiffike bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 22Allah ya albarkace su ya ce, “Ku yi ta haihuwa ku kuma ƙaru da yawa, ku cika ruwan tekuna, bari kuma tsuntsaye su yi yawa a bisa duniya.” 23Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyar ke nan.

24Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa tă ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance. 25Allah ya halicci namun jeji bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.

26Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.”

27Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.

Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.

Miji da mace ya halicce su.

28Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.”

29Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku. 30Na kuma ba da dukan dabbobin ƙasa, da dukan tsuntsayen sama, da dukan abin da yake rarrafe a ƙasa, da dai iyakar abin da yake numfashi; haka kuma na ba da ganyaye su zama abinci.” Haka kuwa ya kasance.

31Allah ya ga dukan abin da ya yi, yana da kyau ƙwarai. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta shida ke nan.

Persian Contemporary Bible

پیدایش 1:1-31

داستان آفرینش

1در آغاز، خدا آسمانها و زمین را آفرید. 2زمین، بی‌شکل و خالی بود، و تاریکی آبهای عمیق را پوشانده بود. و روح خدا بر سطح آبها در حرکت بود.

3خدا فرمود: «روشنایی بشود.» و روشنایی شد. 4خدا روشنایی را پسندید و آن را از تاریکی جدا ساخت. 5او روشنایی را «روز» و تاریکی را «شب» نامید. شب گذشت و صبح شد. این، روز اول بود.

6سپس خدا فرمود: «فضایی باشد بین آبها، تا آبهای بالا را از آبهای پائین جدا کند.» 7پس خدا فضایی به وجود آورد تا آبهای پائین را از آبهای بالا جدا کند. 8خدا این فضا را «آسمان» نامید. شب گذشت و صبح شد. این، روز دوم بود.

9پس از آن خدا فرمود: «آبهای زیر آسمان در یک جا جمع شوند تا خشکی پدید آید.» و چنین شد. 10خدا خشکی را «زمین» و اجتماع آبها را «دریا» نامید. و خدا دید که نیکوست. 11سپس خدا فرمود: «زمین نباتات برویاند، گیاهان دانه‌دار و درختان میوه‌دار که هر یک، نوع خود را تولید کنند.» و چنین شد. 12زمین نباتات رویانید، گیاهانی که برحسب نوع خود دانه تولید می‌کردند، و درختانی که برحسب نوع خود میوۀ دانه‌دار می‌آوردند. و خدا دید که نیکوست. 13شب گذشت و صبح شد. این، روز سوم بود.

14سپس خدا فرمود: «در آسمان اجسام نورافشانی باشند تا روز را از شب جدا کنند، و نشانه‌هایی باشند برای نشان دادن فصل‌ها، روزها، و سال‌ها. 15و این اجسام نورافشان در آسمان، بر زمین بتابند.» و چنین شد. 16پس خدا دو جسم نورافشان بزرگ ساخت: جسم نورافشان بزرگتر برای حکومت بر روز و جسم نورافشان کوچکتر برای حکومت بر شب. او همچنین ستارگان را ساخت. 17خدا آنها را در آسمان قرار داد تا زمین را روشن سازند، 18بر روز و شب حکومت کنند، و روشنایی و تاریکی را از هم جدا سازند. و خدا دید که نیکوست. 19شب گذشت و صبح شد. این، روز چهارم بود.

20سپس خدا فرمود: «آبها از موجودات زنده پر شوند و پرندگان بر فراز آسمان به پرواز درآیند.» 21پس خدا حیوانات بزرگ دریایی و انواع جانداران را که می‌جنبند و آبها را پر می‌سازند و نوع خود را تولید می‌کنند، و نیز همۀ پرندگان را که نوع خود را تولید می‌کنند، آفرید. و خدا دید که نیکوست. 22پس خدا آنها را برکت داده، فرمود: «بارور و زیاد شوید. حیوانات دریایی آبها را پُر سازند و پرندگان نیز بر زمین زیاد شوند.» 23شب گذشت و صبح شد. این، روز پنجم بود.

24سپس خدا فرمود: «زمین، انواع حیوانات را که هر یک نوع خود را تولید می‌کنند، به وجود آورد: چارپایان، خزندگان و جانوران وحشی را.» و چنین شد. 25خدا انواع جانوران وحشی، چارپایان، و تمام خزندگان را، که هر یک نوع خود را تولید می‌کنند، به وجود آورد. و خدا دید که نیکوست.

26سپس خدا فرمود: «انسان را به صورت خود و شبیه خودمان بسازیم، تا بر ماهیان دریا، پرندگان آسمان، و بر چارپایان و همۀ جانوران وحشی و خزندگان روی زمین حکومت کند.» 27پس خدا انسان را به صورت خود آفرید؛ ایشان را به صورت خدا آفرید؛ ایشان را مرد و زن آفرید. 28سپس خدا ایشان را برکت داده، فرمود: «بارور و زیاد شوید، زمین را پُر سازید، بر آن تسلط یابید، و بر ماهیان دریا و پرندگان آسمان و همۀ حیواناتی که بر زمین حرکت می‌کنند، فرمانروایی کنید.»

29آنگاه خدا گفت: «تمام گیاهان دانه‌دار روی زمین را و همۀ میوه‌های درختان را برای خوراک به شما دادم، 30و همۀ علفهای سبز را به همۀ جانوران وحشی، پرندگان آسمان و خزندگان روی زمین، یعنی به هر موجودی که جان در خود دارد، بخشیدم.»

31آنگاه خدا به آنچه آفریده بود نظر کرد و کار آفرینش را از هر لحاظ عالی دید. شب گذشت و صبح شد. این، روز ششم بود.