Ƙarin gargaɗi ga firistoci
1“Yanzu fa wannan gargaɗi dominku ne, ku firistoci. 2In ba ku saurara ba, in kuma ba ku sa zuciyarku ga girmama sunana ba, zan aukar muku da la’ana, zan kuma la’antar da albarkunku. I, na riga na la’anta su, domin ba ku sa zuciyarku ga girmama ni ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.
3“Saboda ku zan tsawata2.3 Ko kuwa yanke (dubi Seftuwajin) wa zuriyarku;2.3 Ko kuwa za su lalace hatsi zan watsa kashin dabbobin hadayunku a fuskokinku, a kuma kwashe ku tare da shi. 4Za ku kuwa san cewa ni ne na aika muku da wannan gargaɗi domin alkawarina da Lawi yă ci gaba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. 5“Alkawarina da shi, alkawari ne na rai da salama, wanda na ba shi; domin yă girmama ni, ya kuwa girmama ni, ya kuma ji tsoron sunana ƙwarai. 6Umarnin gaskiya yana a bakinsa, ba a kuma sami wani ƙarya a leɓunansa ba. Ya yi tafiya tare da ni cikin salama da adalci, ya kuwa juyo da mutane masu yawa daga zunubi.
7“Gama ya kamata leɓunan firist su kiyaye ilimi, ya kamata kuma mutane su nemi umarni daga bakinsa, domin shi ne manzon Ubangiji Maɗaukaki. 8Amma sai kuka kauce hanya, ta wurin koyarwarku kuma kuka sa mutane da yawa suka yi tuntuɓe; kun keta alkawarin da na yi da Lawi,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. 9“Saboda haka na sa a rena ku, a kuma wulaƙanta ku a gaban dukan mutane, domin ba ku bi hanyoyina ba amma kuka nuna sonkai a al’amuran shari’a.”
Keta alkawari ta wurin kisan aure
10Ashe, ba Mahaifi guda dukanmu muke da shi ba? Ba Allah ɗaya ne ya halicce mu ba? Don me muka keta alkawarin kakanninmu ta wurin cin amanar juna?
11Yahuda ya ci amana. An yi abin kunya a Isra’ila da kuma a Urushalima. Yahuda ya ƙazantar da wuri mai tsarkin da Ubangiji yake ƙauna, ta wurin auren ’yar wani baƙon allah. 12Game da mutumin da ya aikata wannan, ko wane ne shi, bari Ubangiji yă yanke shi daga tentunan Yaƙub,2.12 Ko kuwa 12 Bari Ubangiji yă yanke daga tentunan Yaƙub duk wanda ya ba da shaida a madadin mutumin da ya aikata wannan ko da ma ya kawo hadayu ga Ubangiji Maɗaukaki.
13Ga kuma wani abin da kuke yi. Kukan cika bagaden Ubangiji da hawaye. Kukan yi kuka kuna ihu gama Ubangiji ba ya mai da hankali ga hadayunku ko yă karɓe su da farin ciki. 14Kukan ce, “Don me ba ya karɓan hadayunmu?” Ai, domin Ubangiji ya zama shaida tsakaninka da matar ƙuruciyarka, gama ka keta amanar da ka yi mata, ko da yake ita abokiyar zamanka ce, matar aurenka ta alkawari.
15Ashe, Ubangiji bai maishe su ɗaya ba? Cikin jiki da ruhu, su nasa ne. Me ya sa suke ɗaya? Domin yana neman ’ya’ya masu tsoron Allah.2.15 Ko kuwa 15 Amma wanda yake mahaifinmu bai yi haka ba, muddin yana da rai. Me yake nema? Zuriya daga Allah Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amanar matar ƙuruciyarka.
16“Na ƙi kisan aure,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila. “Na kuma ƙi mutumin da ya rufe kansa da tashin hankali kamar riga,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amana.
Ranar shari’a
17Kun sa Ubangiji Maɗaukaki ya gaji da maganganunku.
Sai kuka ce, “Yaya muka sa ya gaji?”
Kun yi haka ta wurin cewa, “Duk waɗanda suke aikata mugunta, mutanen kirki ne a gaban Ubangiji, yana kuwa jin daɗinsu,” kuna kuma cewa, “Ina Allah mai adalci yake?”
Additional Warning to the Priests
1“And now, you priests, this warning is for you. 2If you do not listen, and if you do not resolve to honor my name,” says the Lord Almighty, “I will send a curse on you, and I will curse your blessings. Yes, I have already cursed them, because you have not resolved to honor me.
3“Because of you I will rebuke your descendants2:3 Or will blight your grain; I will smear on your faces the dung from your festival sacrifices, and you will be carried off with it. 4And you will know that I have sent you this warning so that my covenant with Levi may continue,” says the Lord Almighty. 5“My covenant was with him, a covenant of life and peace, and I gave them to him; this called for reverence and he revered me and stood in awe of my name. 6True instruction was in his mouth and nothing false was found on his lips. He walked with me in peace and uprightness, and turned many from sin.
7“For the lips of a priest ought to preserve knowledge, because he is the messenger of the Lord Almighty and people seek instruction from his mouth. 8But you have turned from the way and by your teaching have caused many to stumble; you have violated the covenant with Levi,” says the Lord Almighty. 9“So I have caused you to be despised and humiliated before all the people, because you have not followed my ways but have shown partiality in matters of the law.”
Breaking Covenant Through Divorce
10Do we not all have one Father2:10 Or father? Did not one God create us? Why do we profane the covenant of our ancestors by being unfaithful to one another?
11Judah has been unfaithful. A detestable thing has been committed in Israel and in Jerusalem: Judah has desecrated the sanctuary the Lord loves by marrying women who worship a foreign god. 12As for the man who does this, whoever he may be, may the Lord remove him from the tents of Jacob2:12 Or 12 May the Lord remove from the tents of Jacob anyone who gives testimony in behalf of the man who does this—even though he brings an offering to the Lord Almighty.
13Another thing you do: You flood the Lord’s altar with tears. You weep and wail because he no longer looks with favor on your offerings or accepts them with pleasure from your hands. 14You ask, “Why?” It is because the Lord is the witness between you and the wife of your youth. You have been unfaithful to her, though she is your partner, the wife of your marriage covenant.
15Has not the one God made you? You belong to him in body and spirit. And what does the one God seek? Godly offspring.2:15 The meaning of the Hebrew for the first part of this verse is uncertain. So be on your guard, and do not be unfaithful to the wife of your youth.
16“The man who hates and divorces his wife,” says the Lord, the God of Israel, “does violence to the one he should protect,”2:16 Or “I hate divorce,” says the Lord, the God of Israel, “because the man who divorces his wife covers his garment with violence,” says the Lord Almighty.
So be on your guard, and do not be unfaithful.
Breaking Covenant Through Injustice
17You have wearied the Lord with your words.
“How have we wearied him?” you ask.
By saying, “All who do evil are good in the eyes of the Lord, and he is pleased with them” or “Where is the God of justice?”