Malaki 1 – HCB & NIV

Hausa Contemporary Bible

Malaki 1:1-14

1Annabci, wannan ita ce maganar Ubangiji ga Isra’ila ta wurin Malaki.1.1 Malaki yana nufin manzona.

An ƙaunaci Yaƙub, aka ƙi Isuwa

2“Na ƙaunace ku, in ji Ubangiji.

“Amma sai kuka ce, ‘Yaya ka ƙaunace mu?’

“Isuwa ba ɗan’uwan Yaƙub ba ne?” In ji Ubangiji. “Duk da haka na ƙaunaci Yaƙub, 3amma na ƙi Isuwa, na kuma mai da ƙasarsa da take kan duwatsu kango, na ba da gādonsa ga dilolin hamada.”

4Edom zai iya cewa, “Ko da yake an ragargaza mu, ai, za mu sāke gina kufanmu.”

Amma ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Za su iya gini, amma zan rushe. Za a ce da su Muguwar Ƙasa, mutane da kullum suke a ƙarƙashi fushin Ubangiji. 5Za ku ga wannan da idanunku ku kuma ce, ‘Ubangiji da girma yake, har gaba da iyakokin Isra’ila ma!’

Hadayu masu aibi

6“Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bawa kuma yakan girmama maigidansa. In ni mahaifi ne, ina girman da ya dace da ni? In ni maigida ne, ina girman da ya dace da ni?” In ji Ubangiji Maɗaukaki.

“Ku firistoci, ku ne kuka rena sunana.

“Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka rena sunanka?’

7“Kun ajiye abinci mai ƙazanta a kan bagadena.

“Sai kuka ce, ‘Yaya muka ƙazantar da kai?’

“Ta wurin cewa teburin Ubangiji abin reni ne. 8Sa’ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, wannan daidai ne? Sa’ad da kuka miƙa gurguwar dabba ko marar lafiya, wannan daidai ne? Ku gwada ba wa gwamnanku irin wannan ku gani! Kuna gani zai ji daɗinku? Zai karɓe ku ne?” In ji Ubangiji Maɗaukaki.

9“To, firistoci yanzu ku gwada ku roƙi Allah yă yi mana alheri. Da irin hadayun nan a hannuwanku ne zai ji ku?” In ji Ubangiji Maɗaukaki.

10“Kash, da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ba na jin daɗinku, ba zan kuwa karɓi hadaya daga hannuwanku ba” in ji Ubangiji Maɗaukaki. 11Sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta. A kowane wuri za a miƙa wa sunana turare da tsabtacciyar hadaya domin sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, in ji Ubangiji Maɗaukaki.

12“Amma kun ƙazantar da sunana ta wurin cewa ‘Teburin Ubangiji ya ƙazantu,’ kuka kuma yi magana a kan abincinsa kuna cewa, ‘Abin reni ne.’ 13Kun kuma ce, ‘Mun gaji da irin wannan wahala!’ Kuna hura mini hancin reni,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

“Sa’ad da kuka kawo raunannu, gurguntattun dabbobi, ko kuma dabbobi masu fama da cuta, kuka kuma miƙa su hadaya, kuna gani zan karɓi wannan daga gare ku?” In ji Ubangiji. 14“La’ananne ne macucin da yake da lafiyayyiyar dabba namiji a garkensa wadda ya yi alkawari zai bayar, amma sai ya miƙa hadayar dabba mai aibi ga Ubangiji. Gama ni babban sarki ne, za a kuma ji tsoron sunana a cikin al’ummai,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

New International Version

Malachi 1:1-14

1A prophecy: The word of the Lord to Israel through Malachi.1:1 Malachi means my messenger.

Israel Doubts God’s Love

2“I have loved you,” says the Lord.

“But you ask, ‘How have you loved us?’

“Was not Esau Jacob’s brother?” declares the Lord. “Yet I have loved Jacob, 3but Esau I have hated, and I have turned his hill country into a wasteland and left his inheritance to the desert jackals.”

4Edom may say, “Though we have been crushed, we will rebuild the ruins.”

But this is what the Lord Almighty says: “They may build, but I will demolish. They will be called the Wicked Land, a people always under the wrath of the Lord. 5You will see it with your own eyes and say, ‘Great is the Lord—even beyond the borders of Israel!’

Breaking Covenant Through Blemished Sacrifices

6“A son honors his father, and a slave his master. If I am a father, where is the honor due me? If I am a master, where is the respect due me?” says the Lord Almighty.

“It is you priests who show contempt for my name.

“But you ask, ‘How have we shown contempt for your name?’

7“By offering defiled food on my altar.

“But you ask, ‘How have we defiled you?’

“By saying that the Lord’s table is contemptible. 8When you offer blind animals for sacrifice, is that not wrong? When you sacrifice lame or diseased animals, is that not wrong? Try offering them to your governor! Would he be pleased with you? Would he accept you?” says the Lord Almighty.

9“Now plead with God to be gracious to us. With such offerings from your hands, will he accept you?”—says the Lord Almighty.

10“Oh, that one of you would shut the temple doors, so that you would not light useless fires on my altar! I am not pleased with you,” says the Lord Almighty, “and I will accept no offering from your hands. 11My name will be great among the nations, from where the sun rises to where it sets. In every place incense and pure offerings will be brought to me, because my name will be great among the nations,” says the Lord Almighty.

12“But you profane it by saying, ‘The Lord’s table is defiled,’ and, ‘Its food is contemptible.’ 13And you say, ‘What a burden!’ and you sniff at it contemptuously,” says the Lord Almighty.

“When you bring injured, lame or diseased animals and offer them as sacrifices, should I accept them from your hands?” says the Lord. 14“Cursed is the cheat who has an acceptable male in his flock and vows to give it, but then sacrifices a blemished animal to the Lord. For I am a great king,” says the Lord Almighty, “and my name is to be feared among the nations.