Filibbiyawa 1 – Hausa Contemporary Bible HCB

Hausa Contemporary Bible

Filibbiyawa 1:1-30

1Bulus da Timoti, bayin Kiristi Yesu,

Zuwa ga dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu a Filibbi, tare da masu kula da Ikkilisiya1.1 A al’adance su bishob da kuma masu hidima.

2Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare ku.

Godiya da addu’a

3Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku. 4A cikin dukan addu’o’ina dominku duka, nakan yi addu’a da farin ciki kullum 5saboda tarayyarku a cikin bishara daga ranar farko har yă zuwa yanzu, 6da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yă zuwa ranar Kiristi Yesu.

7Daidai ne in yi wannan tunani game da dukanku, da yake kuna a zuciyata; domin ko ina daure cikin sarƙoƙi ko ina kāre bishara ina kuma tabbatar da ita, dukanku kuna tarayya cikin alherin Allah tare da ni. 8Allah shi ne shaidata, ya san yadda nake ƙaunarku duka da ƙaunar Kiristi Yesu.

9Addu’ata ita ce ƙaunarku tă yi ta cin gaba da ƙaruwa cikin sani da kuma zurfin ganewa, 10don ku iya rarrabe abin da yake mafi kyau, ku kuma zama da tsarki, marasa aibi har yă zuwa ranar Kiristi, 11cikakku da sakamakon aikin adalci da yake zuwa ta wurin Yesu Kiristi, zuwa ga ɗaukakar Allah da kuma yabonsa.

Sarƙoƙin Bulus sun sa ci gaban bishara

12To, ina so ku sani ’yan’uwa, cewa abin da ya faru da ni ya sa cin gaban bishara. 13Ta haka, ya zama sananne ga dukan masu gadin fada1.13 Ko kuwa dukan fada da kuma ga kowa cewa an daure ni da sarƙoƙi saboda Kiristi. 14Saboda sarƙoƙina, yawancin ’yan’uwa cikin Ubangiji sun sami ƙarfafawa su yi maganar Allah gabagadi da kuma babu tsoro.

15Gaskiya ce cewa waɗansu suna yin wa’azin Kiristi saboda kishi da neman faɗa, amma waɗansu da nufi mai kyau suke yi. 16Na biye suna yin haka cikin ƙauna, da sanin cewa an sa ni a nan ne domin kāriyar bishara. 17Na farin dai suna wa’azin Kiristi da sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin sarƙoƙi.1.17 Waɗansu rubuce-rubucen hannun da ba su daɗe ba suna da aya 17 kafin aya 16. 18Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Kiristi. Domin wannan kuwa ina farin ciki.

I, zan kuwa ci gaba da farin ciki, 19gama na san cewa ta wurin addu’o’inku da kuma taimako daga Ruhun Yesu Kiristi, abin da ya same ni zai zama sanadin kuɓutata. 20Ina saurara da marmari da kuma bege cewa ba zan taɓa shan kunya ba, sai dai zan sami issashen ƙarfin hali yanzu kamar kullum, za a ɗaukaka Kiristi a jikina, ko ta wurin rayuwa ko kuma ta wurin mutuwa. 21Gama a gare ni, rai Kiristi ne, mutuwa kuma riba ce. 22In zan ci gaba da rayuwa a cikin jiki, wannan zai zama aiki mai amfani a gare ni. Duk da haka me zan zaɓa? Ban sani ba! 23Na rasa wanda zan zaɓa cikin biyun nan. Ina sha’awa in yi ƙaura in zauna tare da Kiristi, wannan kuwa ya fi kyau nesa ba kusa ba; 24amma ya fi muku muhimmanci in rayu cikin jiki. 25Na tabbata haka ne, na kuwa san zan wanzu in zauna tare da ku duka, domin ku ci gaba, bangaskiyarku tana sa ku farin ciki, 26domin ta wurin kasancewata tare da ku, farin cikinku cikin Kiristi Yesu zai cika sosai ta dalilina.

Rayuwar da ta dace da bishara

27Kome ya faru, ku yi zaman da ya cancanci bisharar Kiristi. Ta haka, ko na zo na gan ku, ko ban zo ba, in ji labari cewa kun tsaya da ƙarfi a cikin ruhu ɗaya, kuna fama kamar mutum ɗaya saboda bangaskiyar bishara 28ba tare da kun ji tsoron waɗanda suke gāba da ku ta kowace hanya ba. Wannan alama ce a gare su cewa za a hallaka su, amma a gare ku za a cece ku, wannan tabbacin kuwa daga wurin Allah ne. 29Gama an ba ku zarafi a madadin Kiristi cewa ba gaskatawa da shi kaɗai ba kuka yi ba, har ma ku sha wahala dominsa, 30da yake kuna shan faman da kuka gan na sha, kuna kuma jin cewa har yanzu ina sha.