2 Bitrus 1 – HCB & KLB

Hausa Contemporary Bible

2 Bitrus 1:1-21

1Siman Bitrus, bawa da kuma manzon Yesu Kiristi,

Zuwa ga waɗanda ta wurin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi sun sami bangaskiya mai daraja irin tamu.

2Alheri da salama su zama naku a yalwace ta wurin sanin Allah da Yesu Ubangijinmu.

Mai da kira da kuma zaɓen da aka wa mutum yă zama tabbatacce

3Ikonsa na Allahntaka ya ba mu kome da muke bukata don rayuwa da kuma tsoron Allah ta wurin sanin wanda ya kira mu ta wurin ɗaukakarsa da nagartarsa. 4Ta wurin waɗannan ya ba mu alkawaransa masu girma da kuma masu daraja, domin ta wurinsu ku iya yin tarayya cikin Allahntakarsa, ku kuma kuɓuta daga lalatar da take cikin duniya wadda mugayen sha’awace-sha’awace suke jawowa.

5Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani; 6ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara da daurewa; ga daurewa kuwa ku ƙara da tsoron Allah; 7ga tsoron Allah kuma ku ƙara da nuna alheri ga ’yan’uwa; ga nuna alheri ga ’yan’uwa kuma ku ƙara da ƙauna. 8Domin in kuna ƙaruwa a waɗannan halaye, za su kāre ku daga rashin tasiri da rayuwa na rashin amfani cikin saninku na Ubangijinmu Yesu Kiristi. 9Amma in wani ba shi da su, ba shi da hangen nesa ke nan kuma makaho ne, ya kuma manta cewa an tsarkake shi daga zunubansa na dā.

10Saboda haka ’yan’uwana, ku ƙara aniya wajen tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Gama in kuka yi waɗannan abubuwa, ba za ku taɓa fāɗuwa ba, 11za ku sami kyakkyawar marabta cikin madawwamin mulkin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi.

Annabcin nassi

12Saboda haka kullum zan tuna muku da waɗannan, ko da yake kun sansu kun kuma kahu ƙwarai cikin gaskiyar da kuke da ita yanzu. 13A ganina ya dace in tunashe ku muddin ina raye cikin tentin wannan jiki, 14domin na sani na kusa in ajiye shi a gefe, yadda Ubangijinmu Yesu Kiristi ya nuna mini a sarari. 15Zan kuwa yi iyakacin ƙoƙari in ga cewa bayan rabuwata kullum za ku iya tuna da waɗannan abubuwa.

16Ba mu bi tatsuniyoyin da aka ƙaga da wayo sa’ad da muka gaya muku game da ikon Ubangijinmu Yesu Kiristi da zuwansa ba, sai dai mu shaidu ne na ɗaukakarsa mai girma da muka gani da ido. 17Gama ya sami girma da ɗaukaka daga Allah Uba sa’ad da murya ta zo masa daga Mafificiyar Ɗaukaka cewa, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; da shi nake jin daɗi ƙwarai.”1.17 Mat 17.5; Mar 9.7; Luk 9.35 18Mu kanmu mun ji wannan muryar da ta zo daga sama sa’ad da muke tare da shi a kan dutse mai tsarki.

19Muna kuwa da maganar annabawa da aka ƙara tabbatar mana, zai fi kyau in kuka lura da ita, kamar hasken da yake haskakawa a wuri mai duhu, har yă zuwa wayewar gari da kuma haskakawar tauraron asubahi a zukatanku. 20Gaba da kome dai, dole ku gane cewa babu annabcin Nassin da ya fito daga fassarar annabi da kansa. 21Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su.

Korean Living Bible

베드로후서 1:1-21

1예수 그리스도의 종이며 사도인 시몬 베드로는 우리 하나님과 구주 예수 그리스 도의 의를 통해 우리와 같이 소중한 믿음을 받은 여러분에게

2하나님과 예수 그리스도를 아는 지식으로 은혜와 평안이 더욱 넘치기를 기도합니다.

하나님을 더 잘 알자

3그리스도께서는 신적인 능력으로 생명과 경건에 관한 모든 것을 우리에게 주셨습니다. 이것은 자신의 영광과 선으로써 우리를 부르신 분을 우리가 알게 될 때 얻어지는 것입니다.

4이것으로 그리스도는 아주 소중하고 중대한 약속을 우리에게 주셨으며 이 약속을 통해 여러분이 세상의 파괴적인 정욕을 피하여 신의 성품에 참여하도록 하셨습니다.

5그러므로 여러분은 최선을 다하여 여러분의 믿음에 선을, 선에 지식을,

6지식에 절제를, 절제에 인내를, 인내에

7경건을, 경건에 형제 우애를, 형제 우애에 사랑을 더하십시오.

8이런 것들을 넉넉히 갖춘다면 여러분은 우리 주 예수 그리스도를 아는 지식이 더욱 풍부해질 것입니다.

9그러나 이런 것을 갖추지 못한 사람은 앞 못 보는 소경이며 자기의 옛 죄가 깨끗해진 것을 잊어버린 사람입니다.

10그러므로 형제 여러분, 더욱 힘써 하나님이 여러분을 불러 주시고 선택해 주셨다는 데 대한 확실한 경험을 갖도록 하십시오. 그러면 여러분이 넘어지지 않고

11우리 주 예수 그리스도의 영원한 나라에 넉넉히 들어가게 될 것입니다.

12여러분이 이런 일을 잘 알고 또 여러분이 받은 진리에 굳게 서 있겠지만 나는 언제나 여러분에게 이 일을 일깨워 주려고 합니다.

13나는 이 육체의 천막 속에 사는 동안 여러분에게 이런 것을 일깨워 주는 것이 옳다고 생각합니다.

14그것은 우리 주 예수 그리스도께서 나에게 분명히 보여 주신 대로 내가 이 육체의 천막을 벗어 버릴 날이 가까웠다는 것을 알고 있기 때문입니다.

15그래서 내가 이 세상을 떠난 뒤에라도 여러분이 언제든지 이 일을 잊지 않도록 열심히 일깨워 주려는 것입니다.

16우리 주 예수 그리스도의 능력과 다시 오심을 여러분에게 말할 때 우리는 꾸며낸 이야기를 전한 것이 아닙니다. 우리는 그분의 위엄 있는 모습을 똑똑히 보았습니다.

17장엄한 영광 가운데서 “이 사람은 내가 사랑하고 기뻐하는 내 아들이다” 라는 음성이 들릴 때 예수님은 하나님 아버지께 영광과 존귀를 받으셨습니다.

18우리도 거룩한 산에서 그분과 함께 있을 때 하늘에서 들려온 그 소리를 들었습니다.

19그리고 우리에게는 보다 확실한 예언의 말씀이 있습니다. 날이 새어 샛별이 여러분의 마음에 떠오를 때까지 여러분은 어두움을 밝혀 주는 등불과 같은 그 말씀에 귀를 기울이는 것이 좋습니다.

20그러나 먼저 알아야 할 것은 성경의 예언을 자기 멋대로 해석해서는 안 된다는 점입니다.

21예언은 결코 사람의 뜻에서 나온 것이 아니라 성령님의 감동을 받은 사람들이 하나님에게 받아 말한 것이기 때문입니다.