Luka 6 – CRO & HCB

Knijga O Kristu

Luka 6:1-49

Rasprava o suboti

(Mt 12:1-8; Mk 2:23-28)

1Neke su subote, dok je Isus prolazio poljem usjeva, učenici počeli trgati klasje, trti ga rukama i jesti. 2A neki farizeji rekoše: “Zašto činite ono što je subotom zabranjeno? Zakonom je zabranjeno skupljati usjev subotom!”

3Isus im odgovori: “Niste li u Pismu čitali o tomu što je učinio kralj David kad su on i njegovi pratitelji ogladnjeli? 4Ušao je u Dom Božji6:4 U Hram. i jeo prineseni kruh6:4 Vidjeti 1 Samuelova 21:1-7. koji je dopušteno jesti samo svećenicima te ga je dao jesti i svojim pratiocima. 5Ja, Sin Čovječji, gospodar sam subote.”

Isus iscjeljuje u subotu

(Mt 12:9-14; Mk 3:1-6)

6Druge subote Isus uđe u sinagogu i počne poučavati. Ondje je bio neki čovjek usahnule desne ruke. 7Pismoznanci i farizeji budno su pazili hoće li Isus u subotu iscijeliti, da ga mogu optužiti. 8Ali Isus je znao za njihovu nakanu pa reče čovjeku usahnule ruke: “Ustani i dođi ovamo na sredinu!” Čovjek ustane i stane ispred svih.

9Tada Isus reče farizejima i pismoznancima: “Pitam vas: Je li subotom dopušteno činiti dobro ili zlo, život spasiti ili uništiti?” 10Pogleda ih sve uokolo pa reče čovjeku: “Ispruži ruku!” On ju ispruži, a ruka mu postane zdrava. 11Isusovi se neprijatelji nato silno razgnjeve te se počnu dogovarati što da poduzmu protiv njega.

Isus izabire dvanaestoricu apostola

(Mt 10:2-4; Mk 3:13-19; Djela 1:13)

12Nedugo zatim Isus ode u goru moliti se. Cijelu se noć molio Bogu. 13Kad se razdanilo, dozove učenike te od njih izabere dvanaestoricu i imenuje ih apostolima:

14Šimuna (kojega je prozvao Petrom),

Andriju (Šimunova brata),

Jakova,

Ivana,

Filipa,

Bartolomeja,

15Mateja,

Tomu,

Jakova (Alfejeva sina),

Šimuna (zvanoga Revnitelj),

16Judu (Jakovljeva sina)

i Judu Iškariotskoga, koji ga je poslije izdao.

Mnoštvo slijedi Isusa

17Isus s njima siđe s gore i zaustavi se na nekoj visoravni. Mnoštvo njegovih učenika te silno mnoštvo naroda iz cijele Judeje, Jeruzalema te iz tirskog i sidonskog primorja 18nagrnulo je da ga sluša i izliječi se od bolesti. Ozdravljali su i ljudi koje su mučili nečisti duhovi. 19Svi su ga pokušavali dotaknuti jer je iz njega izlazila sila koja je sve iscjeljivala.

Blaženstva

(Mt 5:3-12)

20Isus se okrene prema učenicima i reče:

“Blago vama, siromasi,

jer imate kraljevstvo Božje!

21Blago vama koji ste sada gladni,

jer ćete se nasititi!

Blago vama koji sada plačete,

jer ćete se smijati!

22Blago vama kad vas ljudi zamrze,

kad vas izopće i pogrde

i prezru vaše ime kao zločinačko

zbog Sina Čovječjega!

23Kad se to dogodi, radujte se u poskakujte! Jer velika vas nagrada čeka na nebu. Tako su i njihovi očevi postupali prema prorocima.”

Pretkazanje nevolja

24“Teško vama, bogataši,

jer ste već primili svoju utjehu!

25Teško vama koji ste sada siti,

jer ćete gladovati!

Teško vama koji se sada smijete,

jer ćete tugovati i plakati!

26Teško vama kad vas svi budu hvalili,

jer su tako i lažne proroke hvalili njihovi!”

O ljubavi prema neprijatelju

(Mt 5:39-42)

27“Želite li me poslušati, kažem vam: Ljubite svoje neprijatelje! Činite dobro onima koji vas mrze. 28Blagoslivljajte one koji vas proklinju i molite se za one koji vas zlostavljaju. 29Udari li vas tko po obrazu, pružite mu i drugi. Uzima li vam tko ogrtač, dajte mu i košulju. 30Tko god vas što zamoli, dajte mu, a od onoga tko vam otima ne tražite svoje natrag. 31Činite drugima ono što biste htjeli da drugi čine vama!

32Mislite li da zaslužujete nagradu ako volite one koji vas vole? Ta i grešnici tako čine. 33I ako dobro činite onima koji vama čine dobro, zar ste zaslužili nagradu? To čine i grešnici! 34Ako posuđujete samo onima od kojih se nadate povratu, kakvu ste nagradu zaslužili? I grešnici posuđuju grešnicima da jednako prime natrag.

35Ali vi volite svoje neprijatelje. Činite dobro i posuđujte ne nadajući se ničemu zauzvrat. Tako će vam plaća biti velika i bit ćete djeca Svevišnjega koji je dobrostiv i prema nezahvalnicima i prema opakima. 36Budite milosrdni kao što je milosrdan vaš Otac.”

O osuđivanju drugih

(Mt 7:1-5)

37“Ne sudite i nećete biti suđeni. Ne osuđujte, da ne budete osuđeni. Praštajte i oprostit će vam se. 38Dajte, pa ćete i vi dobiti. Vaš će vam se dar vratiti u punoj i prepunoj mjeri, dobro nabijenoj, natresenoj, preobilnoj. Jer kakvom mjerom dajete, takvom će se i vama davati.”

39Zatim im Isus ispriča prispodobe: “Može li slijepac slijepca voditi? Obojica završe u jarku. 40Učenik nije veći od svojega učitelja, a tko je potpuno poučen, ravan je svojem učitelju.

41Što imaš gledati trun u oku svojega brata kad u vlastitome oku ni brvna ne opažaš? 42Kako ti, koji u vlastitome oku ne vidiš ni brvna, možeš reći bratu: ‘Daj da ti izvadim trun iz oka’? Licemjeru! Izvadi najprije brvno iz vlastitog oka, pa ćeš onda dobro vidjeti kako da izvadiš trun iz bratova!”

Prispodoba o stablu i plodovima

(Mt 7:17-20)

43“Dobro stablo ne može roditi nevaljalim plodom niti nevaljalo stablo može roditi dobrim plodom. 44Svako se stablo po plodu poznaje. Ne beru se s trnja smokve niti s gloga grožđe. 45Dobar čovjek iz svojega srca iznosi dobra djela, a zao iz svojega zlog srca zla djela. Jer usta govore ono čega je srce prepuno.”

Kuća na stijeni i kuća na pijesku

(Mt 7:24-27)

46“Zašto me dakle nazivate Gospodinom, a ne činite što vam zapovijedam? 47Reći ću vam kakav je svaki koji dolazi k meni, sluša što govorim i čini tako: 48on je poput čovjeka koji gradi kuću te iskopa dubok temelj i izgradi kuću na stijeni. Kad dođe poplava i navale bujice, ona ostane čvrsto stajati jer je dobro izgrađena. 49A onaj tko sluša riječi i ne čini tako jest poput čovjeka koji kuću izgradi na tlu, bez temelja. Kad na nju navali bujica, ona se brzo sruši i od nje ostane velika razvalina.”

Hausa Contemporary Bible

Luka 6:1-49

Ubangijin Asabbaci

(Mattiyu 12.1-8; Markus 2.23-28)

1A wata ranar Asabbaci, Yesu yana bi ta gonakin hatsi, sai almajiran suka fara kakkarya kan hatsi suna murjewa a hannuwansu suna ci. 2Sai waɗansu Farisiyawa suka ce, “Me ya sa kuke yin abin da doka ta hana yi a ranar Asabbaci?”

3Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi, sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa ba? 4Ya shiga gidan Allah, ya ɗauki keɓaɓɓen burodi, sa’an nan ya ci abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka. Ya kuma ba wa abokan tafiyarsa?” 5Sai Yesu ya ce musu, “Ai, Ɗan Mutum ne Ubangijin Asabbaci.”

(Mattiyu 12.9-14; Markus 3.1-6)

6A wata ranar Asabbaci kuma, Yesu ya shiga majami’a yana koyarwa. To, a nan kuwa akwai wani mutumin da hannun damansa ya shanye. 7Farisiyawa da malaman dokoki suka zuba wa Yesu ido, su ga ko zai warkar a ranar Asabbaci, don su sami dalilin zarginsa. 8Amma Yesu ya san abin da suke tunani. Sai ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.” Sai ya tashi ya tsaya.

9Yesu ya ce musu, “Ina tambayarku, me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a hallaka shi?”

10Sai ya kalle su duka, sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙe, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye. 11Amma Farisiyawa da malaman Doka suka fusata, suka fara tattauna da junansu a kan abin da za su yi wa Yesu.

Manzanni sha biyu

(Mattiyu 10.1-4; Markus 3.13-19)

12Wata rana, a cikin kwanakin nan, Yesu ya je wani dutse domin yă yi addu’a, ya kuma kwana yana addu’a ga Allah. 13Da gari ya waye, sai ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya zaɓi guda goma sha biyu daga cikinsu, waɗanda ya kira su, Manzanni.

14Siman (wanda ya kira Bitrus), ɗan’uwansa Andarawus,

Yaƙub,

Yohanna,

Filibus,

Bartolomeyu,

15Mattiyu,

Toma,

Yaƙub ɗan Alfayus,

Siman wanda ake kira Zilot,

16Yahuda ɗan Yaƙub,

da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.

Albarku da la’anu

(Mattiyu 4.23-25)

17Sai ya sauko tare da su, ya tsaya a wani fili. A can, akwai taro mai yawa na almajiransa, da kuma mutane masu yawan gaske daga ko’ina a Yahudiya, Urushalima da kuma Taya da Sidon da suke bakin teku, 18waɗanda suka zo domin su ji shi, a kuma warkar da cututtukansu. Waɗanda suke fama da mugayen ruhohi kuwa aka warkar da su. 19Kuma dukan mutane suka yi ƙoƙari su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.

(Mattiyu 5.1-12)

20Da ya dubi almajiransa, sai ya ce,

“Masu albarka ne ku da kuke matalauta,

gama mulkin Allah naku ne.

21Masu albarka ne ku da kuke jin yunwa yanzu,

gama za ku ƙoshi.

Masu albarka ne ku da kuke kuka yanzu,

gama za ku yi dariya.

22Masu albarka ne sa’ad da mutane suka ƙi ku,

suka ware ku, suka zage ku,

suna ce da ku mugaye,

saboda Ɗan Mutum.

23“Ku yi farin ciki a wannan rana, ku kuma yi tsalle don murna, saboda ladarku yana da yawa a sama. Gama haka kakanninsu suka yi wa annabawa.

24“Amma kaitonku da kuke da arziki,

gama kun riga kun sami ta’aziyyarku.

25Kaitonku da kuke ƙosassu yanzu,

gama za ku zauna da yunwa.

Kaitonku da kuke dariya yanzu,

gama za ku yi makoki da kuka.

26Kaitonku sa’ad da dukan mutane suna magana mai kyau a kanku,

gama haka kakanninsu suka yi da annabawan ƙarya.

Ƙaunar abokan gāba

(Mattiyu 5.38-48; 7.12)

27“Amma ina faɗa muku, ku da kuke ji na, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku yi wa masu ƙinku alheri. 28Ku albarkaci waɗanda suke la’anta ku, ku kuma yi wa waɗanda suke wulaƙanta ku addu’a. 29In wani ya mare ka a wannan kumatu, juya masa ɗayan ma, in wani ya ƙwace maka babban riga, kada ma ka hana masa ’yar cikin ma. 30Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema yă mayar maka. 31Ka yi wa waɗansu abin da kai kake so su yi maka.

32“In kana ƙaunar masu ƙaunarka ne kawai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma suna ƙaunar waɗanda suke ƙaunarsu. 33In kuma kana yin alheri ga masu yi maka ne kaɗai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma suna yin haka. 34In kana ba da bashi ga mutanen da za su iya biyan ka ne kawai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma, suna ba da bashi ga masu zunubi, da fata za a biya su tsab. 35Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ’ya’yan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye. 36Ku zama masu jinƙai, kamar yadda Ubanku mai jinƙai ne.

Ba wa waɗansu laifi

(Mattiyu 7.1-5)

37“Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku. 38Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yă yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku.”

39Ya kuma faɗa musu wannan misali cewa, “Makaho yana iya jagoran makaho ne? Ba sai dukansu biyu su fāɗa a rami ba? 40Ɗalibi bai fi malaminsa ba, sai dai kowane ɗalibi wanda ya sami cikakkiyar koyarwa, zai zama kamar malaminsa.

41“Don me kake duban ɗan tsinke da yake idon ɗan’uwanka, amma ba ka kula da gungumen da yake a naka ido ba? 42Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Ɗan’uwa, bari in cire maka ɗan tsinke da yake idonka,’ alhali kuwa, kai kanka ka kāsa ganin gungumen da yake a naka ido? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen daga idonka, sa’an nan za ka iya gani sosai, ka kuma cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka.”

Itace da ’ya’yansa

(Mattiyu 7.17-20; 12.34,35)

43“Ba itace mai kyau da yake ba da munanan ’ya’ya. Mummunan itace kuma ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. 44Kowane itace da irin ’ya’yansa ne ake saninsa. Mutane ba sa tsinke ’ya’yan ɓaure daga ƙaya, ko kuwa ’ya’yan inabi daga sarƙaƙƙiya. 45Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne.”

Mai gini mai hikima da mai gini marar hikima

(Mattiyu 7.24-27)

46“Don me kuke ce da ni, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ amma ba kwa yin abin da na faɗa? 47Zan nuna muku kwatancin mutumin da yakan zo wurina, yă ji kalmomina, yă kuma aikata. 48Yana kama da mutumin da ya gina gida, wanda ya haƙa ƙasa da zurfi, sa’an nan ya kafa tushen ginin a kan dutse. Da ambaliyar ruwa ta taso, ƙarfin ruwa kuwa ya buga gidan, wannan bai jijjiga shi ba, domin an yi masa tushen gini na ainihi. 49Amma wanda yakan ji kalmomina, ba ya kuma aikata su, yana kama da mutumin da ya gina gida a ƙasa, ba tare da ya kafa tushen gini ba. A sa’ad da ƙarfin ruwa ya buga gidan, sai gidan yă rushe, mummunar rushewa kuwa.”