Kološanima 3 – CRO & HCB

Knijga O Kristu

Kološanima 3:1-25

Novi život u Kristu

1Uskrsnuli ste s Kristom. Zato težite za nebeskim, gdje Krist sjedi na počasnome mjestu, Bogu zdesna. 2Razmišljajte o onome što u nebu; ne provodite vrijeme baveći se zemaljskim stvarima. 3Jer umrli ste s Kristom i vaš je pravi život skriven s Kristom u Bogu. 4A kada se Krist, koji je naš pravi život, objavi cijelome svijetu, tada će i vi imati udjela u njegovoj slavi.

5Usmrtite dakle ono zemaljsko u svojemu tijelu: blud, nečistoću, strasti, zlu požudu i pohlepu. Ne budite pohlepni za stvarima ovoga svijeta jer je to idolopoklonstvo 6zbog kojega će na ljude pasti Božji gnjev. 7I vi ste nekoć tako živjeli. 8Ali sada od sebe odbacite gnjev, srdžbu, opakost, hulu i prostotu! 9Ne lažite jedni drugima jer ste sa sebe svukli staru zlu narav i njezina zla djela. 10Obukli ste na sebe posve novoga čovjeka, koji se obnavlja spoznajući svojega Stvoritelja. 11Nema više ovdje ni Grka ni Židova, ni obrezana ni neobrezana, ni barbara ni skita, ni roba ni slobodna čovjeka; tu je samo Krist—koji je sve i u svima.

12Vi ste sveti i ljubljeni Božji izabranici. Obucite se stoga u milosrdno srce, dobrostivost, poniznost i strpljivost. 13Podnosite nedostatke drugih i praštajte onima kojima imate što zamjeriti. Kao što je Gospodin vama oprostio, tako i vi opraštajte drugima. 14A najvažnije je: obucite se u ljubav! Ona nas veže u savršeni sklad.

15Neka vašim srcima upravlja Kristov mir. Udovi ste istoga tijela i zato ste pozvani živjeti u miru. Budite zahvalni! 16Neka Kristova riječ u svem svojem bogatstvu prebiva u vama. Poučavajte se i opominjite međusobno sa svom mudrošću. U srcu pjevajte Bogu psalme, hvalospjeve i duhovne pjesme sa zahvalnošću. 17I ma što činili, riječju ili djelom, činite u ime Gospodina Isusa, zahvaljujući po njemu Bogu Ocu.

Upute kršćanskim obiteljima

18Žene, pokoravajte se svojim muževima kao što dolikuje u Gospodinu.

19Muževi, volite svoje žene i ne budite osorni prema njima.

20Djeco, slušajte u svemu roditelje jer je to ugodno Gospodinu.

21Očevi, ne ogorčujte svoju djecu da ne postanu malodušna.

22Robovi, budite poslušni svojim zemaljskim gospodarima u svemu. Ne trudite se da im ugodite samo dok vas vide, već uvijek tako činite, iskrena srca, u strahu Gospodnjem. 23Što god činili, činite od srca, kao Gospodinu, a ne ljudima. 24Znajte da ćete od Gospodina kao nagradu dobiti baštinu. Služite Gospodinu Kristu. 25Tko čini nepravdu, dobit će i plaću nepravednika. U Bogu nema pristranosti!

Hausa Contemporary Bible

Kolossiyawa 3:1-25

Umarnai don zaman tsarki

1Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah. 2Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba. 3Gama kun mutu, ranku yanzu kuwa yana ɓoye tare da Kiristi a cikin Allah. 4Sa’ad da Kiristi, wanda shi ne ranku,3.4 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da ranmu ya bayyana, ku ma za ku bayyana tare da shi cikin ɗaukaka.

5Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne. 6Gama fushin Allah zai sauko a kan masu aikata waɗannan.3.6 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da zuwa a kan waɗanda suke rashin biyayya 7Dā kun yi waɗannan abubuwa, sa’ad da rayuwar tana cikin duniya mai wannan hali. 8Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku. 9Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa 10kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa. 11A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome.

12Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa. 13Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku. 14Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.

15Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. 16Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. 17Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.

Umarnai don iyalan masu bi

18Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji.

19Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.

20’Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.

21Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.

22Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji. 23Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. 24Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa. 25Duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifinsa, babu sonkai.