Upute za bogoštovlje
1Prije svega, molite se za sve ljude; prizivajte Božju milost za njih i zahvaljujte Bogu. 2Molite se i za kraljeve i za sve koji su na vlasti, da možemo živjeti u miru i spokojno, u svoj pobožnosti i svetosti. 3To je dobro i ugodno našemu Bogu Spasitelju 4jer on želi da se svi ljudi spase i da spoznaju ovu istinu: 5jedan je Bog i jedan je posrednik između Boga i ljudi, Čovjek Isus Krist, 6koji je svoj život položio kao otkupninu za sve čovječanstvo. To je poruka koju je Bog dao svijetu u pravo vrijeme. 7A ja sam—istinu govorim, ne lažem—postavljen propovjednikom i apostolom, da poučavam pogane u vjeri i istini.
8Želim da se muškarci, gdje god se okupljate, mole podižući čiste ruke prema Bogu, bez srdžbe i raspravljanja. 9A žene neka se oblače pristojno. Neka se rese skromnošću i razborom, a ne upadljivim frizurama, zlatom, biserjem ili skupocjenom odjećom. 10Žena koja se smatra vjernicom trebala bi se resiti dobrim djelima.
11Neka žene slušaju pouku i uče tiho i pokorno. 12Ne dopuštam da žena poučava niti da gospodari nad mužem. Neka šuti i sluša. 13Jer Bog je najprije stvorio Adama, pa tek onda Evu. 14I Sotona nije prevario Adama, nego Evu; ona je prva zgriješila. 15Ali Bog će ženama sačuvati život za vrijeme porođaja2:15 Ili: žena će se spasiti rađanjem djece budu li ustrajale u vjeri, ljubavi, svetosti i razboritosti.
Umarnai a kan sujada
1Da farko dai, ina gargaɗe ku cewa a yi roƙe-roƙe, ana addu’o’i, ana yin addu’a a madadin waɗansu da kuma a yi godiya saboda kowane mutum 2da sarakuna da dukan masu mulki, domin mu zauna lafiya, rai kuma kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa. 3Wannan yana da kyau, yakan kuma gamshi Allah Mai Cetonmu, 4wanda yake so dukan mutane su sami ceto su kuma zo ga sanin gaskiya. 5Gama Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya tsakanin Allah da mutane, shi ne kuwa Kiristi Yesu, 6wanda ya ba da kansa fansa domin dukan mutane, shaidar da aka bayar a daidai lokaci. 7Don haka ne aka sa ni mai wa’azi, da manzo kuma, gaskiya nake faɗa, ba ƙarya ba, na kuma zama malami mai koya wa al’ummai al’amarin bangaskiya da kuma na gaskiya.
8Ina so maza a ko’ina su ɗaga hannuwansu masu tsarki cikin addu’a, ba tare da fushi ko faɗa ba. 9Ina kuma so mata su lura su yi wa kansu adon da ya cancanta, da rigunan da suka dace, ba da adon kitso ko sa kayan zinariya ko lu’ulu’u ko kuma tufafi masu tsada ba, 10sai dai su yi ayyuka masu kyan da suka dace da matan da suke masu bauta wa Allah.
11Ya kamata mace ta riƙa koyo cikin natsuwa da cikakkiyar biyayya. 12Ban ba mace izini ta koyar ko tă yi mulki a kan namiji ba; sai dai ta zauna shiru. 13Gama Adamu ne aka fara halitta, sa’an nan Hawwa’u. 14Ba kuma Adamu ne aka yaudara ba; macen ce aka yaudara ta kuma zama mai zunubi. 15Amma mata2.15 Da Girik ita Za tă sami ceto2.15 Ko kuwa maido za su sami ceto ta wurin haihuwa, in suka ci gaba cikin bangaskiya, ƙauna da kuma tsarki tare da halin sanin ya kamata.