路加福音 8 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

路加福音 8:1-56

撒种的比喻

1此后,耶稣到各城镇去传扬上帝国的福音。同行的有十二使徒, 2还有几个曾被邪灵和疾病缠身、现在已被医治的妇女。其中有抹大拉玛丽亚,耶稣曾经从她身上赶出七个鬼, 3还有希律的管家苦撒的妻子约亚拿,此外还有苏撒拿等其他妇女。她们用自己的钱财资助耶稣和门徒。

4那时,人群络绎不绝地从各地聚集到耶稣面前,耶稣用比喻教导他们,说: 5“有一个农夫到田里撒种,有些种子落在路旁,被人践踏,又被飞鸟吃掉了; 6有些落在盖着浅土的石头地上,因水分不足,幼苗刚长出来就枯萎了; 7有些落在荆棘丛中,荆棘长起来便把幼苗挤住了; 8有些落在沃土里,发芽生长,结出百倍的果实。”耶稣讲完这番话后,高声说:“有耳可听的,就要留心听。”

9门徒请耶稣解释这比喻的意思, 10耶稣便说:“上帝国的奥秘只让你们知道,对其他人,我就用比喻,使他们看却看不见,听却听不明白。 11这个比喻的意思是这样,种子代表上帝的道, 12种子落在路旁是指人听了道,随后魔鬼来把道从他们心里夺走了,不让他们相信并得救。 13种子落在盖着浅土的石头地上是指人听了道,欣然接受了,但是没有根基,只是暂时相信,一遇到试炼就放弃了。 14种子落在荆棘丛中是指人听了道,后来被生活的忧虑、钱财和享乐缠住了,以致结不出成熟的果实来。 15种子落在沃土里则是指人听了道,用诚实良善的心坚忍持守,至终结出果实。

点灯的比喻

16“没有人点了灯,却用器皿把它盖起来或放到床底下,而是放在灯台上,使进来的人能见到光。 17掩盖的事终会暴露出来,隐藏的秘密终会被人知道。 18因此,你们要留心听,因为凡有的,还要给他更多;凡没有的,连他自以为已经拥有的也要被夺去。”

耶稣的亲属

19这时,耶稣的母亲和兄弟来找祂,由于人太多,他们无法靠近耶稣, 20有人就对祂说:“你的母亲和兄弟在外面想见你。” 21耶稣却说:“听见上帝的话语并遵行的人就是我的母亲、我的弟兄。”

平静风浪

22有一天,耶稣对门徒说:“我们到湖的对岸去吧。”于是他们坐船前往对岸。 23途中耶稣睡着了。不料湖上忽然狂风大作,船灌满了水,非常危险。 24门徒过来唤醒耶稣,说:“主啊,主啊!我们快淹死了!”

耶稣醒来,就斥责风浪,顿时风平浪静了。

25耶稣对他们说:“你们的信心在哪里呢?”

门徒又惊又怕,彼此议论说:“祂究竟是谁?一发命令,连风浪都听祂的!”

格拉森赶鬼

26他们渡过加利利湖,到了格拉森地区。 27耶稣上岸后,迎面遇见当地一个被鬼附身的人。那人长期赤身露体,不住在房屋里,只住在墓穴中。 28他一见到耶稣,就扑倒在祂面前,高声喊叫:“至高上帝的儿子耶稣,我和你有什么关系?求求你,不要折磨我!” 29这是因为耶稣已命令污鬼离开那人。那人多次被污鬼操纵,人们用铁链脚镣把他锁起来看管,他竟把锁链也扯断,被鬼催逼到荒野。

30耶稣问他:“你叫什么名字?”

他说:“我叫‘群’。”因为有一大群鬼附在那人身上。 31鬼不断央求耶稣不要叫它们到无底坑去。

32当时有一大群猪在附近山坡上觅食,污鬼就央求耶稣准许它们进入猪群,耶稣答应了。 33于是那群鬼便离开那人,进入猪群。那群猪就一路奔下陡坡,冲进湖里淹死了。 34放猪的人见此情形拔腿就跑,把这事告诉了城里和乡下的人。 35人们出来看个究竟,到了耶稣那里,发现那曾被鬼附身的人衣着整齐、神智清醒地坐在耶稣脚前,他们都很害怕。 36目击者把事情的始末告诉了他们。 37格拉森地区的居民都十分害怕,请求耶稣离开那里,耶稣便乘船回去了。

38那从前被鬼附身的人恳求跟耶稣同行,耶稣却对他说: 39“你回家吧,把上帝为你所行的奇事告诉别人。”他就回去,走遍全城,四处传扬耶稣为他所行的奇事。

雅鲁求救

40耶稣回到对岸,受到等候在那里的百姓的欢迎。 41一个名叫雅鲁的会堂主管走过来俯伏在耶稣脚前,求耶稣到他家去,因为他有一个大约十二岁的独生女快要死了。

42耶稣前去雅鲁家的时候,人群拥挤着祂。

患血漏病妇人的信心

43有一个患了十二年血漏病的妇人耗尽了积蓄,到处求医,但没有人能医治她。 44妇人挤到耶稣的背后,摸了一下祂衣服的穗边,她的血漏立刻止住了。

45耶稣问:“谁摸我?”没有人说摸过祂。

彼得说:“老师,众人都在拥挤你。”

46耶稣却说:“一定有人摸了我,因为我感觉有能力从我身上出去。”

47那妇人知道无法隐瞒,就战战兢兢地走过来,俯伏在耶稣脚前,把她摸了耶稣的衣裳后顽疾马上痊愈的始末当众说了出来。

48耶稣对她说:“女儿,你的信心救了你!安心回去吧。”

雅鲁女儿死而复活

49耶稣还在说话的时候,有人从雅鲁家赶来,对雅鲁说:“你的女儿已经死了,不用麻烦老师了。”

50耶稣听见,就对雅鲁说:“不要怕,只要信。你的女儿一定会好的!”

51到了雅鲁家,耶稣只准彼得雅各约翰雅鲁夫妇跟祂进去。 52屋内的人都在为那女孩哀伤哭泣,耶稣说:“不要哭,她没有死,只是睡着了。” 53众人就讥笑祂,因为他们明明知道那女孩死了。 54耶稣拉着那女孩的手,说:“孩子,起来!” 55她的灵魂就回来了,她立刻站了起来。耶稣吩咐人给她东西吃。 56她的父母非常惊讶,耶稣却嘱咐他们不要把这事传开。

Hausa Contemporary Bible

Luka 8:1-56

Misalin mai shuka

1Bayan wannan sai Yesu ya zazzaga gari da ƙauye, yana wa’azin bisharar mulkin Allah. Sha Biyun nan kuwa suna tare da shi, 2da kuma waɗansu mata waɗanda aka warkar da su daga cututtukansu, da kuma mugayen ruhohi. Cikinsu akwai Maryamu (wadda ake kira Magdalin) wadda aljanu bakwai suka fito daga cikinta. 3Da Yowanna matar Kuza, manajan iyalin Hiridus; da Suzana; da waɗansu mata da yawa. Waɗannan mata suna taimaka musu cikin hidima, daga cikin abin da suke da shi na zaman gari.

(Mattiyu 13.1-9; Markus 4.1-9)

4Yayinda taron mai girma na taruwa, mutane kuma daga garuruwa dabam-dabam suna zuwa wurin Yesu, sai ya ba da wannan misali ya ce, 5“Wani manomi ya fita domin ya shuka irinsa. Da yana watsa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, aka tattaka su, tsuntsayen sararin sama kuma suka cinye su. 6Waɗansu suka fāɗi a kan dutse, da suka tsira sai suka yanƙwane don babu ruwa a wurin. 7Waɗansu kuma suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma tare, sai ƙayan suka shaƙe su. 8Waɗansu kuma har yanzu, suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka yi girma, suka ba da amfani riɓi ɗari-ɗari, fiye da abin da aka shuka.”

Da faɗin haka sai ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”

(Mattiyu 13.10-17; Markus 4.10-12)

9Almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali. 10Sai ya ce, “Ku ne aka ba sanin asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane kam, ina magana da misalai, saboda,

“ ‘ko da yake suna kallo, ba za su gani ba,

ko da yake suna ji, ba za su gane ba.’

(Mattiyu 13.18-23; Markus 4.13-20)

11“Ga ma’anar misalin, irin, shi ne maganar Allah. 12Waɗanda suka fāɗi a kan hanya su ne mutanen da suka ji, amma Iblis, yakan zo ya ɗauke maganar daga zuciyarsu, don kada su gaskata, su sami ceto. 13Na kan dutse kuwa, su ne da jin maganar, sukan karɓa da murna, amma ba su da saiwa. Sukan gaskata na ɗan lokaci, amma lokacin gwaji, sai su ja da baya. 14Irin da suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa, su ne mutanen da suka ji, amma a kwana a tashi, tunanin kayan duniya, da neman arziki, da son jin daɗi, sukan hana su ba da ’ya’ya. 15Amma irin da suka fāɗi a ƙasa mai kyau kuwa, su ne mutane masu kyakkyawar zuciya, mai kyau, da suka ji, suka riƙe, suka kuma jimre har suka ba da ’ya’ya.”

Fitila a kan wurin ajiye fitila

(Markus 4.21-25)

16“Ba mai ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta a cikin tulu, ko kuma ya sa ta a ƙarƙashin gado ba. A maimakon haka, yakan sa ta a kan wurin ajiye fitila, saboda mutane masu shigowa su ga haske. 17Ba abin da yake ɓoye da ba za a fallasa ba. Kuma ba abin da yake rufe, da ba za a sani ba, ko a fitar da shi a fili ba. 18Saboda haka, ku yi tunani da kyau yadda kuke saurara. Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda ba shi da shi kuma, abin da yake tsammani yana da shi ma, za a karɓe daga gare shi.”

Mahaifiyar Yesu da ’yan’uwansa

(Mattiyu 12.46-50; Markus 3.31-35)

19Sai uwar Yesu da ’yan’uwansa suka zo, domin su gan shi, amma ba su iya zuwa kusa da shi ba, saboda taron. 20Sai wani ya faɗa masa cewa, “Ga uwarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje suna so su gan ka.”

21Ya amsa ya ce, “Mahaifiyata da ’yan’uwana, su ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma aikata ta.”

Yesu ya kwantar da ruwa da iska

(Mattiyu 8.23-27; Markus 4.35-41)

22Wata rana Yesu ya ce wa almajiransa, “Mu haye zuwa wancan gefen tafkin.” Sai suka shiga jirgin ruwa suka fara tafiya. 23Da suna cikin tafiya, sai barci ya kwashe shi. Sai wata babban iska ta taso kan tafkin, har ruwa ya fara shiga cikin jirgin. Suka shiga babban hatsari.

24Almajiran suka je suka tashe shi daga barci, suka ce, “Ubangiji, Ubangiji, za mu nutse!”

Ya tashi ya kwaɓe iskar da kuma haukar ruwan. Sai ruwan da iskar suka natsu. Kome ya yi tsit. 25Sai ya tambayi almajiransa, “Ina bangaskiyarku?”

A cikin tsoro da mamaki, suka ce wa junansu, “Wane ne wannan? Yana ba da umarni ga iska da ruwa ma, kuma suna biyayya da shi?”

Warkar da mai aljanu

(Mattiyu 8.28-34; Markus 5.1-20)

26Suka shiga jirgin ruwa zuwa yankin Gerasenawa da yake a hayin tafkin, daga wajen Galili. 27Da Yesu ya sauka daga jirgin, sai ga wani mutum mai aljanu daga garin. Mutumin ya daɗe bai sa tufafi ba, kuma ba ya zama a gida. Yana zama a cikin kaburbura. 28Da ya ga Yesu, sai mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi, ya fāɗi a gabansa, yana ihu cewa, “Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ina roƙonka, kada ka ba ni wahala!” 29Gama Yesu ya riga ya umarci mugun ruhun ya fita daga mutumin. Sau da yawa mugun ruhun ya sha kamunsa. Ko da yake akan daure shi hannu da ƙafa, da sarƙa, a kuma yi gadinsa, amma yakan tsinke sarƙoƙinsa, aljanun kuma su kore shi zuwa wuraren kaɗaici, inda ba kowa.

30Yesu ya tambaye shi, “Mene ne sunanka?”

Sai ya amsa, “Tuli,”8.30 Lejiyon yana nufin Tuli. gama aljanu masu ɗumbun yawa ne suna cikinsa. 31Suka yi ta roƙonsa kada yă umarce su su shiga ramin Abis.

32A wurin kuwa, akwai babban garken aladu da suke kiwo a gefen tudu. Aljanun suka roƙi Yesu ya bar su, su shiga cikin aladun, ya kuwa yardar musu. 33Da aljanun suka fita daga cikin mutumin, sai suka shiga cikin aladun. Garken kuma ya gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, kuma suka nutse.

34Da masu kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka ruga da gudu zuwa garin da kewaye suka kai labari. 35Mutanen kuma suka fito don su ga abin da ya faru. Da suka iso wurin Yesu, sai suka tarar da mutumin da aljanun suka fita daga cikinsa, yana zaune kusa da Yesu sanye da tufafi, kuma cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su. 36Waɗanda suka ga abin da faru, suka gaya wa mutanen yadda aka warkar da mai aljanun. 37Sai dukan mutanen yankin Gerasenawa suka roƙi Yesu ya bar su, don sun tsorata sosai. Sai Yesu ya shiga jirgin ruwa ya tafi.

38Mutumin da aka fitar da aljanun daga cikinsa, ya roƙi Yesu don yă tafi tare da shi, amma Yesu ya sallame shi ya ce, 39“Koma gida, ka shaida babban alherin da Allah ya yi maka.” Sai mutumin ya tafi yana faɗin abin da Yesu ya yi masa a duk garin.

Yarinya da ta mutu da mace marar lafiya

(Mattiyu 9.18-26; Markus 5.21-43)

40Da Yesu ya koma, taron suka marabce shi, don dā ma duk suna jiransa. 41Sai wani mutum mai suna Yayirus, wani mai mulkin majami’a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, yana roƙonsa ya zo gidansa, 42domin diyarsa ɗaya tak, wadda ta kai shekara goma sha biyu, tana bakin mutuwa. Da Yesu yake kan hanyarsa, taron mutane masu yawa suka yi ta matsa shi a kowane gefe. 43A wurin kuwa, akwai wata mace wadda tana da ciwon zubar da jini, har na shekara goma sha biyu, amma babu wanda ya iya warkar da ita. 44Sai ta zo ta bayansa, ta taɓa bakin rigarsa. Nan da nan, zubar da jininta ya tsaya.

45Yesu ya yi tambaya, “Wa ya taɓa ni?”

Bayan kowa ya yi musu, sai Bitrus ya ce, “Ubangiji, ai, mutane da yawa suna matsinka ta kowane gefe.”

46Amma Yesu ya ce, “Wani ya taɓa ni, na san cewa iko ya fita daga wurina.”

47Sai macen, da ta ga ba halin ɓoyewa, sai ta fita, jikinta na rawa, ta fāɗi a gabansa. A gaban dukan mutanen, ta faɗi dalilin da ya sa ta taɓa shi, da yadda ta warke nan take. 48Sai Yesu ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”

49Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’ar ya ce, “Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu.”

50Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita.”

51Da ya iso gidan Yayirus, sai ya hana kowa yă bi shi cikin ɗakin, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma mahaifin da mahaifiyar. 52Ana cikin haka, dukan mutanen kuma sai kuka da makoki suke ta yi, domin yarinyar. Sai Yesu ya ce, “Ka daina yin kuka, ba tă mutu ba, tana barci ne.”

53Sai suka yi masa dariya, da yake sun san cewa, ta mutu. 54Amma Yesu ya kama ta a hannu ya ce, “Diyata, tashi.” 55Ruhunta ya dawo, kuma ta tashi, nan take. Yesu ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci. 56Iyayenta suka yi mamaki, amma ya ba su umarni kada su faɗa wa kowa abin da ya faru.