Chinese Contemporary Bible (Simplified)

启示录 16:1-21

1我听见殿中有宏亮的声音对七位天使说:“去将那盛满上帝烈怒的七个碗倾倒在地上。”

2第一位天使离去,将碗倒在了地上,那些有怪兽的印记、敬拜兽像的人身上长出奇痛无比的毒疮。

3第二位天使将碗倒在了海洋里,海水变得像死人的血,海中的活物都死光了。

4第三位天使将碗倒在了江河与水泉里,水就变成了血。 5我听见掌管各水源的天使说:

“昔在今在的圣者啊!

你是公义的,

因为你施行了审判。

6由于他们流了众圣徒和先知们的血,

现在你使他们喝血,

这正是他们应得的报应。”

7我又听见从祭坛发出的声音说:

“是的,全能的主上帝,

你的判决真实公义。”

8第四位天使将碗倒在太阳上,太阳就变得炙热如火,可以灼伤人。 9人们被炙热灼伤,就亵渎掌管这些灾祸的上帝的名,他们毫无悔意,不肯归荣耀给上帝。

10第五位天使将碗倒在那海中怪兽的座位上,它的国便被黑暗笼罩,它的国民痛苦难当,咬自己的舌头。 11他们因为痛苦和毒疮就亵渎天上的上帝,不肯为自己的所作所为悔改。

12第六位天使将碗倒在幼发拉底大河上,河水立刻干了,为东方各国的王预备了道路。 13我又看见三个像青蛙一样的污鬼分别从巨龙、怪兽和假先知的口里跳出来。 14其实它们都是鬼魔的灵,能行奇迹。它们到普天下召集各王,预备在全能上帝的大日子来临时聚集争战。

15“看啊!我要像贼一样出其不意地来到。那警醒等候,看守自己衣裳,不致赤身行走蒙受羞辱的人有福了。”

16鬼魔把众王召集到一个希伯来话叫哈米吉多顿的地方。

17第七位天使将碗倒在空中时,从殿里的宝座上传出响亮的声音说:“成了!” 18随后雷电交加,伴随着巨响,还有空前剧烈的大地震。 19巴比伦大城裂作三段,其他各国的城邑也都倒塌了。上帝并没有忘记巴比伦大城的罪恶,要把那杯盛满祂烈怒的酒给她喝。 20海岛都沉没了,山岭也都不见了, 21又有重达三十四公斤16:21 三十四公斤”希腊文是“一他连得”。的巨型冰雹从天而降,打在世人身上。世人无法忍受这极大的灾祸,就亵渎上帝。

Hausa Contemporary Bible

Ruʼuya ta Yohanna 16:1-21

Kwanoni bakwai na fushin Allah

1Sai na ji wata babbar murya daga haikalin tana ce wa mala’iku bakwai nan, “Ku tafi ku zuba kwanoni bakwai nan na fushin Allah a kan duniya.”

2Mala’ika na fari ya je ya juye kwanonsa a bisan ƙasa, sai munanan gyambuna masu zafi suka fito a jikin mutanen da suke da alamar dabbar suka kuma yi wa siffarta sujada.

3Mala’ika na biyu ya juye kwanonsa a bisan teku, sai tekun ya zama jini kamar na mataccen mutum, kuma kowane abu mai rai da yake cikin tekun ya mutu.

4Mala’ika na uku ya juye kwanonsa a bisan koguna da maɓulɓulan ruwa, sai suka zama jini. 5Sa’an nan na ji mala’ikan da yake lura da ruwaye ya ce,

“Kai mai adalci ne cikin waɗannan hukuntai,

kai da kake yanzu, kake kuma a dā, Mai Tsarki, saboda yadda ka yi hukuncin nan;

6gama sun zub da jinin tsarkakanka da kuma annabawanka,

ka kuwa ba su jini su sha, yadda ya dace da su.”

7Na kuma ji bagaden ya amsa,

“I, Ubangiji Allah, Maɗaukaki,

hukuntanka daidai yake na adalci ne kuma.”

8Mala’ika na huɗu ya juye kwanonsa a bisan rana, sai aka ba wa rana iko ta ƙona mutane da wuta. 9Aka ƙone su da zafin wuta mai tsanani suka kuwa la’anci sunan Allah wanda yake da iko a kan waɗannan annoban, amma suka ƙi su tuba su kuma ɗaukaka shi.

10Mala’ika na biyar ya juye kwanonsa a bisan gadon sarautar dabbar, mulkinta kuwa ya zama duhu. Mutane suka yi ta cizon bakinsu saboda azaba 11suka kuma la’anci Allah na sama saboda zafinsu, da kuma saboda gyambunansu, amma suka ƙi su tuba daga abin da suka riga suka yi.

12Mala’ika na shida ya juye kwanonsa a bisan babban kogin Yuferites, sai ruwansa ya shanye don a shirya hanya saboda sarakuna daga Gabas. 13Sa’an nan na ga mugayen ruhohi guda uku da suka yi kamar kwaɗi; suka fito daga bakin macijin nan, da kuma daga bakin dabbar, da kuma daga bakin annabin ƙaryan nan. 14Su ruhohin aljanu ne da suke aikata abubuwan banmamaki, sukan je wurin sarakunan dukan duniya, don su tattara su don yaƙi a babbar ranar Allah Maɗaukaki.

15“Ga shi, ina zuwa kamar ɓarawo! Mai albarka ne wanda yake zama a faɗake yana kuma saye da tufafinsa, don kada yă yi tafiya tsirara a kuma kunyata shi.”

16Sa’an nan aka tattara sarakuna zuwa wurin da a Ibraniyanci ake kira Armageddon.

17Mala’ika na bakwai ya juye kwanonsa cikin iska, daga haikalin kuwa sai aka ji wata babbar murya daga kursiyin, tana cewa, “An gama!” 18Sai ga walƙiya, ƙararraki, tsawa da kuma matsananciyar girgizar ƙasa. Ba a taɓa yin irin wannan girgizar ƙasar ba, tun kasancewar mutum a duniya, girgizar ƙasar kuwa gawurtacciya ce. 19Babban birnin ya rabu kashi uku, biranen al’ummai kuma suka rurrushe. Allah ya tuna da Babilon Mai Girma ya kuma ba ta kwaf cike da ruwan inabin fushinsa. 20Kowane tsibiri ya gudu ba a kuwa ƙara ganin duwatsu ba. 21Daga sararin sama manyan ƙanƙara masu nauyin gaske suka fāɗo a kan mutane. Suka kuma la’anci Allah saboda annobar ƙanƙarar, domin annobar ta yi muni ƙwarai.