Łukasza 3 – SZ-PL & HCB

Słowo Życia

Łukasza 3:1-38

Jan Chrzciciel przygotowuje drogę

1Był piętnasty rok rządów Tyberiusza, rzymskiego cezara. W tym czasie gubernatorem prowincji Judei był Piłat, zarządcą Galilei—Herod Antypas, zarządcą Iturei i Trachonu—jego brat Filip, a zarządcą Abileny—Lizaniasz. 2Urząd najwyższego kapłana Izraela sprawowali Annasz i Kajfasz. Wtedy właśnie Jan, syn Zachariasza, mieszkający dotąd na pustyni, otrzymał od Boga misję. 3Wędrując brzegiem Jordanu, wzywał ludzi do opamiętania się i przyjęcia Bożego przebaczenia. Swoją przemianę mieli poświadczyć zanurzeniem w wodzie. 4To właśnie o nim mówił prorok Izajasz:

„Głos wołającego na pustyni:

Przygotujcie Panu drogę,

wyrównajcie przed Nim ścieżki!

5Zrównajcie góry, zasypcie doliny,

wyprostujcie zakręty, usuńcie wyboje!

6A wtedy wszyscy zobaczą Boże zbawienie”.

7Całe tłumy przychodziły do Jana, aby dać się zanurzyć, a on mówił do nich:

—Przebiegłe węże! Kto wam powiedział, jak uciec przed nadchodzącą karą Boga?! 8Najpierw pokażcie poprzez wasze uczynki, że naprawdę się opamiętaliście! Nie oszukujcie się, powtarzając: „Jesteśmy potomkami samego Abrahama”. Zapewniam was, że Bóg może stworzyć potomków Abrahama nawet z tych kamieni! 9Siekiera Bożego sądu już jest przyłożona do pnia. I każde drzewo, które nie wydaje owocu, zostanie wycięte i rzucone w ogień.

10—Co więc mamy czynić?—pytały tłumy.

11—Jeśli masz dwa ubrania, daj jedno biednemu. Jeśli masz co jeść, podziel się z głodnym—odpowiadał Jan.

12A przychodzili do niego nawet znani z nieuczciwości poborcy podatkowi, chcąc przyjąć chrzest. I pytali Go:

—Nauczycielu, co mamy czynić?

13—Nie pobierajcie większych podatków niż ustalono—odpowiadał im.

14—A co z nami?—pytali żołnierze.

—Od nikogo nie wymuszajcie pieniędzy. Zadowólcie się swoim żołdem!—odpowiedział. —I nikogo fałszywie nie oskarżajcie.

15Ponieważ wszyscy oczekiwali przyjścia Mesjasza, zaczęto się zastanawiać, czy przypadkiem to Jan Nim nie jest. 16On jednak zaprzeczył temu:

—Ja was zanurzam w wodzie. Lecz niebawem nadejdzie ktoś potężniejszy ode mnie. Ktoś, komu nie jestem nawet godzien zdjąć butów! On będzie was zanurzał w Duchu Świętym i w ogniu. 17On potrafi oddzielić plewy od ziarna i wszystko oczyścić—ziarno zbierze do magazynu, a plewy spali w niegasnącym ogniu.

18Jan wiele razy w podobny sposób ostrzegał ludzi i głosił im dobrą nowinę. 19Krytykował natomiast króla Heroda Antypasa za to, że ożenił się z Herodiadą, żoną swojego brata, oraz za inne złe czyny. 20W późniejszym czasie król jeszcze dalej posunął się w swoim grzechu i uwięził Jana.

Chrzest i rodowód Jezusa

21Pewnego dnia, gdy Jan zanurzał ludzi w wodzie, znalazł się wśród nich sam Jezus. Gdy został ochrzczony i modlił się, nagle otworzyło się niebo 22i Duch Święty zstąpił na Niego jak gołąb. A z nieba rozległ się głos:

—Jesteś moim ukochanym Synem, moją największą radością.

23Gdy Jezus rozpoczynał swoją publiczną działalność, miał około trzydziestu lat. Uważano Go za syna Józefa.

Ojcem zaś Józefa był Heli, a ojcem Helego 24—Mattat.

Kolejni ich przodkowie to: Lewi, Melchi, Jannaj, Józef,

25Matatiasz, Amos,

Nahum, Chesli, Naggaj, 26Maat,

Matatiasz, Semea, Josech, Joda,

27Jan, Resa,

Zorobabel, Salatiel, Neri, 28Melchi,

Addi, Kosam, Elmadan, Her, 29Jezus, Eliezer,

Jorim, Mattat, Lewi, 30Symeon,

Juda, Józef, Jonam, Eliakim,

31Meleasz, Menna,

Mattat, Natan, król Dawid, 32Jesse,

Jobed, Booz, Sala, Naasson,

33Aminadab, Admin,

Arni, Ezrom, Fares, Juda, 34Jakub,

Izaak, Abraham,

Tare, Nachor,

35Seruch, Ragau,

Falek, Eber, Sala, 36Kainam,

Arfaksad, Sem, Noe, Lamech,

37Matusala, Henoch,

Jaret, Maleleel, Kainam, 38Enos,

Set i Adam.

Adam zaś pochodził od Boga.

Hausa Contemporary Bible

Luka 3:1-38

Yohanna Mai Baftisma ya shirya hanya

(Mattiyu 3.1-12; Markus 1.1-8; Yohanna 1.19-28)

1A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tiberiyus, a lokacin Buntus Bilatus ne gwamnar Yahudiya, Hiridus kuma yana sarautar Galili, ɗan’uwansa Filibus yana sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiline.  2A lokacin ne Annas da Kayifas suke manyan firistoci. Sai maganar Allah ta zo wa Yohanna, ɗan Zakariya a hamada. 3Ya zaga dukan ƙasar da take kewaye da Urdun, yana wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai. 4Kamar yadda yake a rubuce a littafin annabi Ishaya.

“Muryar mai kira a hamada,

‘Ku shirya wa Ubangiji hanya,

ku miƙe hanyoyi dominsa.

5Za a cike kowane kwari,

a farfashe kowane dutse da kowane tudu.

Za a miƙe hanyoyin da suka karkace,

a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul.

6Dukan ’yan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’ ”3.6 Ish 40.3-5

7Yohanna ya ce wa taron da suke zuwa domin yă yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa? 8Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim. 9An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.”

10Sai taron suka tambaye shi, suka ce “Me za mu yi ke nan?”

11Ya amsa ya ce, “Ya kamata, mutumin da yake da riguna biyu, yă raba da wanda ba shi da riga, mai abinci kuma yă yi haka.”

12Masu karɓar haraji ma suka zo, domin a yi musu baftisma. Suka yi tambaya, suka ce “Malam, me ya kamata mu yi?”

13Ya ce musu, “Kada ku karɓa fiye da abin da aka ce a karɓa.”

14Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?”

Sai ya amsa ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.”

15Mutane suka zuba ido, suna kuma tunani a zuciyarsu, ko Yohanna ne Kiristi wanda ake sauraron zuwansa. 16Yohanna ya amsa musu duka ya ce, “Ina muku baftisma da ruwa. Amma wani wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban ma isa in kunce igiyar takalmansa ba. Shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da wuta kuma. 17Matankaɗinsa yana a hannunsa don yă tankaɗe sussukarsa ya kuma tattara alkama cikin rumbunsa, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.” 18Da kalmomi masu yawa Yohanna ya yi wa mutane gargaɗi, ya kuma yi musu wa’azin bishara.

19Amma da Yohanna ya tsawata wa Hiridus mai mulki saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa, da kuma dukan sauran mugayen abubuwan da ya yi, 20Hiridus dai ya ƙara ɓata al’amarin. Ya sa a kulle Yohanna a kurkuku.

Baftismar Yesu da kuma asalinsa

(Mattiyu 3.13-17; Markus 1.9-11)

21Sa’ad da ake wa dukan mutane baftisma, sai aka yi wa Yesu shi ma. Da yana cikin addu’a, sai sama ya buɗe, 22Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauko masa a wata siffa, kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama, ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, kai ne kuma kana faranta mini zuciya ƙwarai.”

(Mattiyu 1.1-17)

23To, Yesu kansa yana da shekaru kusan talatin da haihuwa sa’ad da ya fara aikinsa. An ɗauka shi ɗan Yusuf ne,

ɗan Heli, 24ɗan Mattat,

ɗan Lawi, ɗan Melki,

ɗan Yannai, ɗan Yusuf,

25ɗan Mattatiyas, ɗan Amos,

ɗan Nahum, ɗan Esli,

ɗan Naggai, 26ɗan Ma’at,

ɗan Mattatiyas, ɗan Semeyin,

ɗan Yosek, ɗan Yoda,

27ɗan Yowanan, ɗan Resa,

ɗan Zerubbabel, ɗan Sheyaltiyel,

ɗan Neri, 28ɗan Melki,

ɗan Addi, ɗan Kosam,

ɗan Elmadam, ɗan Er,

29ɗan Yoshuwa, ɗan Eliyezer,

ɗan Yorim, ɗan Mattat,

ɗan Lawi, 30ɗan Simeyon,

ɗan Yahuda, ɗan Yusuf,

ɗan Yonam, ɗan Eliyakim,

31ɗan Meleya, ɗan Menna,

ɗan Mattata, ɗan Natan,

ɗan Dawuda, 32ɗan Yesse,

ɗan Obed, ɗan Bowaz,

ɗan Salmon,3.32 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da Sala ɗan Nashon,

33ɗan Amminadab, ɗan Ram,3.33 Waɗansu rubuce-rubucen hannu suna Amminadab, ɗan Admin, ɗan Arni; waɗansu rubuce-rubucen hannun kuma sun bambanta sosai.

ɗan Hezron, ɗan Ferez,

ɗan Yahuda, 34ɗan Yaƙub,

ɗan Ishaku, ɗan Ibrahim,

ɗan Tera, ɗan Nahor,

35ɗan Serug, ɗan Reyu,

ɗan Feleg, ɗan Eber,

ɗan Sala, 36ɗan Kainan,

ɗan Arfakshad, ɗan Shem,

ɗan Nuhu, ɗan Lamek,

37ɗan Metusela, ɗan Enok,

ɗan Yared, ɗan Mahalalel,

ɗan Kainan, 38ɗan Enosh,

ɗan Shitu, ɗan Adamu,

ɗan Allah.