Marek 7 – SNC & HCB

Slovo na cestu

Marek 7:1-37

Ježíš hovoří o skryté čistotě

1Jednou za Ježíšem přišli z Jeruzaléma farizejové a učitelé zákona. 2Všimli si, že jeho učedníci nedodržují obřad umývání rukou před jídlem a tak porušují židovskou tradici. 3Židé a zvláště znalci zákona úzkostlivě lpěli na zvycích svých předků a nedotkli se jídla dříve, než si pečlivě umyli ruce. 4A když přišli z trhu, vždy se umyli celí, než se pustili do přípravy pokrmů. Stejně pečliví byli i při omývání číší, džbánů a kuchyňského nádobí. Už po staletí dodržovali mnoho podobných předpisů.

5Teď tedy dotírali na Ježíše: „Proč tvoji učedníci nedodržují zvyky našich předků a jedí neumytýma rukama?“

6„Pokrytci!“ odrazil je. „Pravdivě o vás řekl Izajáš:

‚Ústa mají plná Boha,

ale srdce prázdné.

7Jejich obřady jsou k ničemu,

jejich učení nic než lidské výmysly.‘

8Opomíjíte skutečné Boží příkazy a nahrazujete je svými předpisy. 9Vždyť vy vlastně rušíte Boží zákon ve jménu svých tradic.

10Tak například Mojžíš vám tlumočil toto přikázání Božího zákona: ‚Měj v úctě svého otce i svou matku.‘ K tomu dodal, že každý, kdo by třeba jen nadával svým rodičům, propadá trestu smrti. 11-12Vy však připouštíte, aby člověk zanedbával své rodiče, kteří potřebují pomoc, jestliže má výmluvu: ‚Nemohu se o vás postarat, protože to, co z mého výdělku mělo patřit vám, jsem odevzdal jako příspěvek v chrámu.‘ 13Tak stavíte svoje názory nad Boží zákon. A to je jenom jeden příklad z mnoha.“

14Pak k sobě přivolal zástup lidí a řekl jim: 15-16„Poslouchejte mě a snažte se porozumět. To, co sníte, nemůže nijak ublížit vaší duši; ničíte ji však, když se zabýváte nečistými a zlými myšlenkami a šíříte je kolem sebe.“

17Když potom vešel do nějakého domu, aby si odpočinul, začali se ho učedníci vyptávat na význam toho, co právě řekl.

18„Ani vy tomu nerozumíte?“ divil se Ježíš. „Nechápete, že duši člověka nemůže uškodit to, co snědl?

19Vždyť jídlo neznečišťuje nitro; projde jen žaludkem a vychází ven.“

20K tomu připojil: „Člověku škodí to, co pochází z jeho nitra. 21Tam se líhnou zlé myšlenky, necudnost, 22nevěra, krádež, vražda, sobectví, zlost, podlost, sprostota, závist, urážky, pýcha a všelijaké výstřednosti. 23To je to zlo, které vychází z nitra člověka a odděluje ho od Boha.“

Ježíš vyhání démona z dívky

24Když opustil Ježíš Galileu, odešel na sever do pohanské Fénicie, kde se ubytoval v jednom domě. Chtěl utajit svou přítomnost, ale bylo to marné; už se o něm vědělo i tam.

25Tak o něm uslyšela i jedna Syroféničanka. 26Přišla a prosila ho na kolenou, aby uzdravil její pomatenou dceru.

27Ježíš jí odpověděl: „Přišel jsem především pro ty, kdo se hlásí k živému Bohu. Nech nejprve najíst děti. Nebylo by správné vzít jim jídlo a hodit je štěňatům.“

28Žena se však nevzdala: „To je pravda, Pane, ale i štěňata sbírají pod stolem, co dětem upadne.“

29„Když to vidíš tak,“ řekl jí, „jdi klidně domů, tvoje dcera je zdravá.“

30Vrátila se tedy domů, kde nalezla dítě, jak klidně spí, beze stopy pomatenosti.

Zástup se podivuje Ježíšovu uzdravování

31Z Fénicie se Ježíš vracel velikou oklikou zpět ke Genezaretskému jezeru, až se ocitl na území Desítiměstí. 32Tamější lidé k němu přivedli hluchoněmého člověka a žádali, aby ho uzdravil.

33Ježíš si vzal muže stranou od zástupu. Nasliněným prstem se dotkl jeho jazyka a vložil mu své prsty do uší. (To byla jeho řeč k hluchoněmému.) 34Pak se Ježíš krátce pomodlil a zvolal: „Otevři se!“ 35V té chvíli začal muž slyšet a srozumitelně mluvit.

36Pak Ježíš žádal všechny shromážděné, aby se o tom nikomu nezmiňovali; ale čím více jim to zakazoval, tím více o tom mluvili, protože se s něčím podobným ještě nesetkali. 37Lidé žasli a říkali: „To už je schopen napravit všechno, když hluchým vrací sluch a němým řeč.“

Hausa Contemporary Bible

Markus 7:1-37

Mai tsabta da marar tsabta

(Mattiyu 15.1-9)

1Farisiyawa da waɗansu malaman dokoki waɗanda suka zo daga Urushalima, suka taru kewaye da Yesu. 2Sai suka ga waɗansu daga cikin almajiransa suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta, wato, da ba a wanke ba. 3(Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci, sai sun wanke hannuwa sarai tukuna, yadda al’adun dattawa suka ce. 4Sa’ad da suka dawo daga wurin kasuwanci, dole su wanke hannu kafin su ci abinci. Sukan kuma kiyaye waɗansu al’adu da yawa, kamar wanken kwafuna, tuluna da butoci.7.4 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da tuluna, butoci da kujeru)

5Saboda haka, Farisiyawa da malaman dokoki suka tambayi Yesu, suka ce, “Don me almajiranka ba sa bin al’adun dattawa, a maimakon haka suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta?”

6Ya amsa ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa,

“ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni,

amma zukatansu sun yi nesa da ni.

7A banza suke mini sujada,

koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’7.7 Ish 29.13

8Kun yar da umarnan Allah, kuna bin al’adun mutane.”

9Ya kuma ce musu, “Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye al’adunku! 10Gama Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’7.10 Fit 20.12; M Sh 5.16 kuma, ‘Duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.’7.10 Fit 21.17; Fir 20.9 11Amma ku, kukan ce, in mutum ya ce wa mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da ya kamata ku samu daga wurina, Korban ne,’ (wato, abin da aka keɓe wa Allah), 12sa’an nan haka ba kwa ƙara barinsa yă yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa wani abu. 13Ta haka kuke rushe maganar Allah ta wurin al’adun da kuke miƙa wa ’ya’yanku. Haka kuma kuke yin abubuwa da yawa.”

(Mattiyu 15.10-20)

14Sai Yesu ya sāke kiran taron wurinsa ya ce, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimci wannan. 15Ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. Sai dai abin da ya fita daga cikin mutum ne, yake ƙazantar da shi.”7.15 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da “marar tsabta.” 16 Duk mai kunnuwan ji, yă ji

17Bayan ya bar taron, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali. 18Ya ce, “Ashe, ba ku da saurin ganewa? Ba ku gane cewa ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. 19Gama ba ya shiga cikin zuciyarsa, sai dai cikin tumbinsa, sa’an nan kuma yă fita daga jikinsa.” (Da faɗin haka, Yesu ya nuna tsabtar kowane irin abinci.)

20Ya ci gaba, “Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi. 21Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, 22kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta. 23Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”

Bangaskiyar Baheleniya

(Mattiyu 15.21-28)

24Sai Yesu ya bar wurin, ya kuma tafi wajajen Taya. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa yă sani ba. Duk da haka, bai iya ɓoye kasancewarsa ba. 25Da jin labarinsa, sai wata mace wadda ƙaramar diyarta tana da mugun ruhu, ta zo ta durƙusa a gabansa. 26Macen kuwa mutuniyar Hellenawa ce, an haife ta a Funisiya a Suriya. Ta roƙi Yesu yă fitar da aljani da yake jikin diyarta.

27Yesu ya ce mata, “Da farko, bari ’ya’ya su ci su ƙoshi tukuna, gama ba daidai ba ne, a ɗauki burodin yara a jefa wa karnukansu.”

28Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, ko karnuka ma da suke ƙarƙashin tebur, sukan ci burbuɗin da suke fāɗuwa daga abincin yara.”

29Sai ya ce mata, “Saboda irin wannan amsa, ki tafi, aljanin ya rabu da diyarki.”

30Ta tafi gida, ta tarar da diyarta kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.

Warkar da kurma wanda yake kuma bebe

31Sai Yesu ya bar wajajen Taya, ya bi ta Sidon har zuwa Tekun Galili da kuma cikin yankin Dekafolis.7.31 Wato, Birane Goma 32A can ne waɗansu mutane suka kawo masa wani kurma, wanda da ƙyar yake magana. Sai suka roƙe shi yă ɗibiya hannunsa a kan mutumin.

33Bayan da ya jawo shi gefe, sai Yesu ya sa yatsotsinsa a kunnuwan mutumin, ya tofa miyau ya kuma taɓa harshen mutumin. 34Ya ɗaga kai sama, ya ja numfashi mai zurfi, sa’an nan ya ce masa,“Effata!” (Wato, “Buɗe!”). 35Bayan ya faɗa haka, sai kunnuwan mutumin suka buɗe, harshensa kuma ya kunce, sai ya fara magana sarai.

36Yesu ya umarce su, kada su gaya wa kowa. Amma ƙara yawan kwaɓarsu ƙara yawan yaɗa labarin suke ta yi. 37Mutane suka cika da mamaki, suka ce, “Kai, ya yi kome daidai. Har ma yana sa kurame su ji, bebaye kuma su yi magana.”