Lukáš 7 – SNC & HCB

Slovo na cestu

Lukáš 7:1-50

Římský setník projevuje svoji víru

1Když Ježíš skončil kázání k lidem, šel do Kafarnaum. 2Tam žil jeden římský důstojník, který vlastnil otroka. Velice si ho cenil, a proto těžce nesl, když otrok smrtelně onemocněl. 3Důstojník se doslechl o Ježíšovi a poslal k němu židovské starší s prosbou, aby přišel a otroka zachránil. 4Ti se vydali za Ježíšem a naléhali: „Ten muž si zaslouží tvou pomoc. 5Má rád náš národ a dokonce nám dal postavit synagogu.“ 6Ježíš s nimi šel. Když už byli nedaleko jeho domu, poslal k němu důstojník své přátele se vzkazem: „Pane, neobtěžuj se tolik, nezasloužím si, abys mne poctil svou návštěvou. 7Jako pohan jsem se ani neodvážil jít za tebou osobně. Stačí, když řekneš slovo, a můj otrok se určitě uzdraví. 8Vždyť i já musím splnit rozkaz svých nadřízených a moji podřízení se musí zase podrobit mým povelům. Řeknu-li vojákovi: ‚Jdi!‘ tak jde, a řeknu-li druhému: ‚Přijď!‘ tak přijde. Poručím-li svému otrokovi: ‚Udělej toto!‘ tedy to udělá.“ 9Ježíš byl těmi slovy velmi udiven a řekl svým průvodcům: „S tak velkou vírou jsem se nesetkal u žádného Žida.“ 10Když se poslové vrátili do domu římského důstojníka, byl již otrok zdráv.

Ježíš křísí syna vdovy

11Brzy nato se Ježíš odebral do města Naim. Jeho žáci a mnozí další lidé ho doprovázeli. 12V blízkosti městské brány potkali pohřební průvod. Jedna vdova pochovávala svého jediného syna. K pohřbu se sešlo hodně lidí. 13Když Ježíš spatřil tu vdovu, bylo mu jí velice líto a řekl: „Neplač!“ 14Pak přistoupil blíže, dotkl se már a zastavil průvod. „Mládenče, vstaň!“ zvolal. 15Tu se mrtvý posadil a promluvil. Tak Ježíš vrátil matce syna. 16Počáteční zděšení okolostojících vystřídala radost a začali chválit Boha: „Velký prorok přišel mezi nás! Bůh navštívil svůj lid.“ 17Zpráva o této události se rozšířila po celém Judsku a okolí.

Ježíš rozptyluje Janovy pochybnosti

18O tom všem vyprávěli učedníci Jana Křtitele svému učiteli. 19Jan poslal dva z nich za Ježíšem, aby se zeptali: „Jsi Mesiáš, anebo máme čekat ještě někoho jiného!“ 20-21Když přišli s tou otázkou, Ježíš právě uzdravoval nemocné, všelijak postižené, osvobozoval spoutané duševními nemocemi, mnohým slepým vracel zrak. 22Poslům odpověděl: „Jděte zpět k Janovi a řekněte mu, co jste viděli a slyšeli: slepí vidí, chromí chodí, hluší slyší, mrtví ožívají a těm, kteří nic nemají, nabízí Bůh podíl ve svém království. 23Šťasten je každý, kdo mne neodmítne.“ 24Když poslové odešli, začal Ježíš mluvit ke shromážděným lidem o Janu Křtiteli: „Když jste chodili za mužem, který strávil život v pustinách, koho jste očekávali? Rákos, který se otočí podle větru? 25Nebo jste chtěli vidět člověka v přepychových šatech? Takoví jsou jen v palácích. 26Chtěli jste slyšet proroka? Ano, poznali jste někoho ještě většího než proroka. 27Jan je ten, o němž je napsáno:

‚Posílám svého posla před tebou,

aby ti připravil cestu.‘

28Jan dostal nejvyšší úkol ze všech lidí: oznámit, že Kristus přichází! A přece i ten nejnepatrnější, kdo se dočkal a uvěřil, byl poctěn více než Jan. 29Víte, že Janovi posluchači – a byli mezi nimi i lidé s všelijakou pověstí – přijali Jana jako Božího posla a dali se proto od něho pokřtít. 30Farizejové a znalci zákona však Janův křest odmítli, protože nepochopili, že i oni potřebují Boží odpuštění.“ 31Ježíš pokračoval: „Komu se tak podobají? 32Jsou nespokojení a náladoví jako děti, které si hrají na návsi chvíli na svatbu, chvíli na pohřeb a vzájemně si vyčítají:

‚Pískali jsme vám,

a vy jste netancovali.

A pak jsme vám zase smutně zpívali,

a vy jste neplakali.‘

33Když se Jan Křtitel postil a nepil víno, říkali jste, že je fanatik, 34a když Syn člověka jí a pije, říkáte pohrdlivě: ‚Podívejte se na toho žrouta a pijana, který se přátelí i se zrádci národa a s kdejakou sebrankou.‘ 35Ale kdo přijme Boží moudrost, ten tomu porozumí.“

Hříšná žena potírá olejem Ježíšovy nohy

36Jeden farizej pozval Ježíše na oběd. Ten přišel a stoloval s ním. 37V tom městě žila také žena, která měla špatnou pověst. Když slyšela, že Ježíš je na návštěvě u farizeje Šimona, vzala alabastrovou nádobku s drahocenným vonným olejem a šla tam. 38Poklekla k Ježíšovým nohám, smáčela mu je slzami, utírala svými vlasy, líbala je a potírala vonným olejem. 39Když to viděl farizej, který Ježíše pozval, myslel si: „Kdyby to byl prorok, věděl by, co je to za ženu, a nedovolil by, aby se ho taková hříšnice vůbec dotkla.“ 40Tu ho Ježíš oslovil: „Rád bych se tě, Šimone, na něco zeptal.“ „Prosím, jen mluv,“ řekl Šimon. 41„Jeden věřitel měl dva dlužníky. První mu byl dlužen pět set stříbrných, druhý padesát. 42Když však ani jeden z nich nemohl zaplatit, věřitel odpustil dluh oběma. Co myslíš, který z nich ho bude mít víc rád?“ 43Šimon odpověděl: „Mám za to, že ten, kterému více prominul.“ „Správně,“ řekl Ježíš. 44Pak ukázal na ženu u svých nohou a pověděl Šimonovi: „Podívej se na tu ženu. Přišel jsem do tvého domu a ty jsi mi nedal umýt nohy, jak je zvykem; tato žena mi je umyla svými slzami a vytřela svými vlasy. 45Na uvítanou jsi mne jako hostitel nepolíbil, ale tato žena mi nepřestává líbat nohy. 46Nepotřel jsi mi hlavu olejem, ale tato žena nelitovala drahocenného oleje na mé nohy. 47Je to jako s těmi dlužníky: velký hřích je jí odpuštěn a to se projevuje na lásce, kterou mi prokazuje. Kdo si myslí, že odpuštění nepotřebuje, pak málo miluje.“ 48Potom se obrátil k ženě: „Tvoje hříchy jsou ti odpuštěny.“ 49Když si ostatní hosté říkali mezi sebou: „Co je to za člověka, že si troufá odpouštět hříchy?“ 50uklidnil ji: „Tvoje víra tě zachránila, jdi pokojně domů.“

Hausa Contemporary Bible

Luka 7:1-50

Bangaskiyar jarumin Roma

(Mattiyu 8.5-13; Yohanna 4.43-54)

1Bayan Yesu ya gama gaya wa mutanen dukan waɗannan abubuwa, sai ya shiga Kafarnahum. 2A can, akwai wani bawan wani jarumin yana ciwo, yana kuma a bakin mutuwa. Maigidansa kuwa yana sonsa sosai. 3Jarumin sojan ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu dattawan Yahudawa wajensa, yana roƙonsa yă zo yă warkar da bawansa. 4Da suka isa wurin Yesu, sai suka roƙe shi sosai, suka ce, “Wannan mutum, ai, ya dace a yi masa haka, 5gama yana ƙaunar al’ummarmu ta Yahudawa, har ya gina majami’armu.” 6Sai Yesu ya tafi tare da su.

Da ya yi kusa da gidan, sai jarumin nan, ya aiki abokai su ce masa, “Ubangiji, kada ka dami kanka, gama ban isa ka shiga gidana ba. 7Shi ya sa ban ma ga na isa in zo wurinka ba. Amma ka yi magana kawai, bawana zai warke. 8Gama ni kaina, mutum ne a ƙarƙashin iko, akwai kuma sojoji a ƙarƙashin ikona. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi, ga wani kuma in ce, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan kuma ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai yă yi.”

9Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki sosai. Ya juya ya wa taron da yake bin sa, “Ina faɗa muku, ban taɓa samun irin bangaskiya mai girma haka ko cikin Isra’ila ba.” 10Sai mutanen da aka aika, suka koma gida, suka tarar bawan ya warke.

Yesu ya tā da ɗan gwauruwa

11Ba a daɗe ba, sai Yesu ya tafi wani garin da ake kira Nayin. Almajiransa da taro mai yawa suka tafi tare da shi. 12Da ya yi kusa da ƙofar garin, sai ga wata gawa ana fitowa da ita. Shi ne ɗa kaɗai ga mahaifiyarsa, ita kuma gwauruwa ce. Taro mai yawa daga garin yana tare da ita. 13Da Ubangiji ya gan ta, sai ya ji tausayinta ya ce, “Kada ki yi kuka.”

14Yesu ya je ya taɓa akwatin gawar, sai masu ɗaukarsa suka tsaya cik. Sai ya ce, “Saurayi, na ce maka, tashi!” 15Sai mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuma ya ba da shi ga mahaifiyarsa.

16Sai tsoro ya kama su duka, suka yabi Allah, suna cewa, “Babban annabi ya bayyana a cikinmu. Allah ya zo domin yă taimaki mutanensa.” 17Wannan labarin game da Yesu, ya bazu ko’ina a Yahudiya da kewayenta.

Yesu da Yohanna Mai Baftisma

(Mattiyu 11.1-19)

18Almajiran Yohanna suka gaya masa dukan waɗannan abubuwa. Sai ya kira biyu daga cikinsu, 19ya aike su wurin Ubangiji, su tambaya su ce, “Kai ne wanda zai zo, ko kuma mu saurari wani dabam?”

20Da mutanen suka iso wurin Yesu, sai suka ce, “Yohanna Mai Baftisma ne ya aike mu wurinka, mu yi tambaya, ‘Ko kai ne wanda zai zo, ko kuma mu saurari wani dabam?’ ”

21A daidai lokacin nan, Yesu ya warkar da mutane da yawa masu ciwo, masu cututtuka, da kuma masu mugayen ruhohi. Ya kuma ba makafi da yawa ganin gari. 22Sai ya amsa wa almajiran Yohanna ya ce, “Ku koma ku faɗa wa Yohanna abin da kuka ji, da abin da kuka gani. Makafi suna ganin gari, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin bishara. 23Mai albarka ne mutumin da bai yi shakkar bangaskiyar da yake da ita a kaina ba.”

24Bayan almajiran Yohanna suka tafi, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna ya ce, “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne? 25In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da tufafi masu kyau ne? A’a, masu sa kayan tsada da suke cikin annashuwa, ai, a fada suke. 26Amma me kuka je kallo? Annabi? I, ina kuma faɗa muku, ya ma fi annabi. 27Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa,

“ ‘Zan aiko da ɗan saƙona yă sha gabanka,

wanda zai shirya hanya, a gabanka.’7.27 Mal 3.1

28Ina faɗa muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yohanna girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.”

29(Dukan mutane, har da masu karɓar haraji, da suka ji kalmomin Yesu, sai suka yarda cewa hanyar Allah gaskiya ce, domin Yohanna ne ya yi musu baftisma. 30Amma Farisiyawa da masanan dokoki, suka ƙi nufin Allah game da su, domin Yohanna bai yi musu baftisma ba.)

31Yesu ya ci gaba da cewa, “To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Kamar me suke? 32Suna kama da yaran da suke zama a bakin kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,

“ ‘Mun busa muku sarewa,

amma ba ku yi rawa ba,

Mun kuma yi muku waƙar makoki,

ba ku kuma yi kuka ba.’

33Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo, ba ya cin burodi, ba ya shan ruwan inabi, sai kuka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ 34Ɗan Mutum ya zo yana ci, yana sha, sai kuka ce, ‘Ga mai yawan ci, mashayi, da kuma abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ 35Amma akan tabbatar da hikima ta gaskiya bisa ga dukan ’ya’yanta.”

Mace mai zunubi ta shafe wa Yesu turare

36To, ana nan, sai ɗaya daga cikin Farisiyawa ya gayyaci Yesu cin abincin yamma a gidansa, ya kuwa tafi gidan Bafarisiyen, ya zauna a tebur. 37Da wata mace wadda ta yi rayuwar zunubi a wannan gari ta ji Yesu yana cin abinci a gidan Bafarisiyen, sai ta kawo ɗan tulun turaren alabasta, 38ta kuma tsaya daga bayansa, wajen ƙafafunsa tana kuka, sai hawayenta sun fara zuba a ƙafafunsa. Sai ta goge su da gashin kanta, ta sumbace su, sa’an nan ta shafa musu turare.

39Da Bafarisiyen da ya gayyace shi, ya ga wannan, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san ko wace ce take taɓansa, da kuma irin macen da take, cewa mai zunubi ce.”

40Sai Yesu ya ce masa, “Siman, ina da abin da zan faɗa maka.”

Shi kuwa ya ce, “Malam sai ka faɗa.”

41Yesu ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu da suke riƙe bashin mai ba da rance. Ana bin guda dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin. 42Dukan biyun suka gagara biyansa, sai ya yafe musu. To, a ganinka, wa zai fi ƙaunar mutumin nan?”

43Siman ya amsa ya ce, “A ganina, wanda aka yafe wa mai yawa ne.”

Sai Yesu ya ce, “Ka faɗa daidai.”

44Sai ya juya wajen macen, ya ce wa Siman, “Ka ga macen nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwa don ƙafafuna ba, amma ta wanke ƙafafuna da hawayenta, ta kuma goge su da gashin kanta. 45Ba ka yi mini sumba ba, amma tun shigowata a nan, macen nan ba tă daina sumbar ƙafafuna ba. 46Ba ka shafa mai a kaina ba, amma ta zubo turare a ƙafafuna.

47“Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawa, an gafarta mata, gama ƙaunarta mai yawa ce. Amma wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, yakan nuna ƙauna kaɗan.”

48Sai Yesu ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.”

49Sauran baƙin suka fara ce wa juna, “Wane ne wannan, wanda har yake gafarta zunubai?”

50Yesu ya ce wa macen, “Bangaskiyarki ta cece ki, ki sauka lafiya.”