2. Tesalonickým 1 – SNC & HCB

Slovo na cestu

2. Tesalonickým 1:1-12

Jasná naděje Kristova návratu

1-2Drazí bratři v Tesalonice, opět se hlásíme s přáním milosti a pokoje od Boha Otce i Pána Ježíše Krista.

3Nemůžeme jinak, než za vás Bohu stále děkovat. Je to namístě, když navzdory všemu pronásledování vaše víra i láska dělá tak úžasné pokroky, 4že vás můžeme v ostatních církvích dávat za příklad. 5-8V tom se projevuje spravedlivý Boží soud: těm, kteří vás nyní trápí, odplatí trápením, zatímco vás, kteří nyní trpíte, vysvobodí spolu s námi. To bude tehdy, až Ježíš, náš Pán, v ohnivém plameni sestoupí se svými anděly z nebe, aby potrestal ty, kdo Boha nectí a odmítají jeho poselství o Ježíši, našem Pánu. 9Za trest budou navždy vzdáleni od Pána a jeho moci a slávy. 10V ten den Kristus přijde sklidit chválu a vděčnost za všechno, co pro své vyvolené učinil. I vy patříte mezi ně, protože jste uvěřili našemu svědectví.

11Neúnavně se za vás modlíme, aby vás Bůh proměňoval a pomáhal vám dosáhnout cíl, k němuž vás povolal. Prosíme ho, aby svou mocí podepřel všechna vaše dobrá předsevzetí v životě víry. 12Tak mu každý bude moci vzdát čest a chválu za výsledky jeho díla ve vás; vaší slávou pak bude, že patříte jemu. To vše vám umožnila jeho milost a moc.

Hausa Contemporary Bible

2 Tessalonikawa 1:1-12

1Bulus, da Sila, da Timoti,

Zuwa ga ikkilisiya ta Tessalonikawa ta Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi.

2Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

Godiya da addu’a

3Dole kullum mu gode wa Allah saboda ku, ’yan’uwa, haka kuwa ya dace, domin bangaskiyarku tana girma gaba-gaba, ƙaunar da kowannenku yake yi wa juna kuwa tana ƙaruwa. 4Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da daurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha.

5Dukan wannan yana tabbatar cewa hukuncin Allah daidai ne, saboda haka kuma za a lissafta ku a kan kun cancanci mulkin Allah, wanda dominsa ne kuke shan wahala. 6Allah mai adalci ne, Zai sāka wa masu ba ku wahala da wahala 7yă kuma sauƙaƙa muku ku da kuke wahala, har ma da mu. Wannan zai faru sa’ad da aka bayyana Ubangiji Yesu daga sama cikin wuta mai ci tare da mala’ikunsa masu iko. 8Zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba da kuma waɗanda ba su yi biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu ba. 9Za a hukunta su da madawwamiyar hallaka a kuma kau da su daga gaban Ubangiji da kuma daga ɗaukakar ikonsa 10a ranar da zai dawo don a ɗaukaka shi a cikin mutanensa masu tsarki, yă kuma zama abin banmamaki ga dukan waɗanda suka gaskata. Wannan ya haɗa har da ku, domin kun gaskata shaidar da muka yi muku.

11Sane da wannan, kullum muna addu’a saboda ku, don Allahnmu yă sa ku cancanci kiransa, ta wurin ikonsa kuma yă cika kowace manufarku mai kyau da kuma kowane aikin da bangaskiyarku ta iza. 12Muna wannan addu’a don sunan Ubangijinmu Yesu yă sami ɗaukaka a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu da na Ubangiji Yesu Kiristi.1.12 Ko kuwa Allah da Ubangiji, Yesu Kiristi