Řád při bohoslužbě je nutný
1-16Jinak vás musím pochválit, že na mne nezapomínáte a držíte se toho, co jsem vás naučil. Nelíbí se mi však móda, jakou u vás některé ženy začínají pěstovat: když ve veřejných shromážděních vzývají Boha nebo o něm hovoří, nezahalují si hlavu. Vždyť je to stejný projev neúcty, jako když muž si nechá ve společnosti na hlavě pokrývku. Platí-li v důstojnosti pořadí Bůh – Kristus – muž – žena, pak si má žena hlavu zahalovat, jako si ji zahalují andělé před Bohem. Muž to nedělá proto, že má nezakrytě zrcadlit Boží slávu, a žena to má dělat proto, že tím uznává vyšší autoritu muže. Takový je aspoň všeobecný zvyk. Jinak jsou si ovšem obě pohlaví rovna v tom, že jako žena pochází z muže, tak se muž zase rodí z ženy; oba stejně vděčí za svůj život Bohu.
17-21Když už jsem v tom napomínání, ještě jedna věc mě rmoutí. Vidím, že vaše shromáždění začínají být spíš ke škodě než k užitku. Slyšel jsem – a něco pravdy na tom zřejmě je, že do vašich shromáždění pronikají různice. Na tom je dobré snad jedině to, že se aspoň jasně odliší zdravé od nezdravého mezi vámi. Výsledkem však je, že se ani nedá společně zasednout ke stolu Páně, protože každý honem spěchá sníst to, co si přinesl, a pak už často nemůže pozřít sousto s těmi, kdo přišli hladoví. 22Copak se nemůžete najíst už doma? Nebo se snad chcete vychloubat svou kuchyní před méně zámožnými bratry a zlehčovat tak Boží církev? Za to tedy ode mne pochvalu nečekejte.
Správný přístup k Večeři Páně
23Učil jsem vás přece, co mi Kristus svěřil: v tu noc, kdy byl zrazen, 24vzal chléb, poděkoval za něj Bohu, rozlámal ho a řekl: „Toto je moje tělo, které se za vás obětuje. Čiňte to na mou památku.“ 25Po večeři pak pozvedl kalich se slovy: „Hle, nová smlouva, kterou zpečetím svou krví. Ten kalich vám ji připomene, kdykoliv z něho budete pít.“ 26Jedením toho chleba a společným pitím z kalicha tedy hlásáte Kristovu smrt až do jeho příchodu.
27To ovšem znamená, že kdo bere ten chléb nebo to víno na lehkou váhu, znevažuje tím Kristovu smrt. 28-29Ať tedy každý nejdřív sám sebe zkoumá, než sáhne po chlebu a kalicha. Jinak na sebe přivolává odsouzení, protože pohrdá Kristovou obětí.
30Proto je vás tolik nemocných, slabých a umírajících. 31Nemuselo by to být, kdybychom byli sami na sebe přísnější. 32Takto nás však musí trestat Pán, aby nás pak nemusel odsoudit s ostatním světem.
33Proto vás prosím, bratři, abyste při takových setkáních čekali, až se sejdete všichni. 34Kdo by nemohl vydržet hladem, ať se nají doma a nepřivolává Boží trest. Ostatní zařídím, až přijdu.
1Ku bi gurbina, kamar yadda ni nake bin gurbin Kiristi.
Ɗa’a cikin sujada
2Ina yabonku saboda kuna tunawa da ni a cikin kowane abu, kuna kuma riƙe da koyarwar,11.2 Ko kuwa al’adu yadda na ba ku. 3To, ina so ku gane cewa shugaban kowane namiji Kiristi ne, shugaban mace namiji ne, shugaban Kiristi kuma Allah ne. 4Kowane namijin da ya yi addu’a ko annabci da kansa a rufe ya jawo kunya wa kansa. 5Duk macen da ta yi addu’a ko annabci da kanta a buɗe kuwa ta rena kanta, ya zama kamar an aske kanta ke nan. 6In mace ba ta so tă rufe kanta, to, sai tă aske gashinta; in kuwa abin kunya ne mace tă yanke ko tă aske gashinta, to, sai tă rufe kanta.
7Namiji kuwa bai kamata ya rufe kansa ba,11.4-7 Ko kuwa 4 Duk namijin da ya yi addu’a ko annabci da dogon gashin kai, ya rena kansa. 5 Duk macen da ta yi addu’a ko annabci ba tare da ta rufe gashin kanta ba kuwa ta rena kanta, ta yi kama da ɗaya a cikin “matan da aka yi wa aski.” 6 In mace ba ta da abin rufuwa, sai tă kasance mai aski kwal a kanta, amma da yake abin kunya ne mace tă yanke ko tă aske kanta, ya kamata tă sa yă yi girma kuma. 7 Bai kamata namiji yă kasance da dogon gashin kai ba da yake shi kamannin Allah ne, da kuma darajar Allah, amma mace dai, darajar namiji ne. 8Gama namiji bai fito daga mace ba, sai dai mace ce ta fito daga namiji. 9Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji. 10Don haka, saboda wannan, da kuma saboda mala’iku, dole mace ta ɗaura wani abu a kanta. 11Duk da haka a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, namiji kuma ba a rabe yake da mace ba. 12Kamar yadda mace ta fito daga namiji, haka kuma aka haifi namiji ta wurin mace. Sai dai kowane abu daga Allah yake.
13Ku kanku duba mana. Ya yi kyau mace tă yi addu’a ga Allah da kanta a buɗe? 14Kai, yadda halitta take ma, ai, ta koya muku cewa in namiji yana da dogon gashi, abin kunya ne a gare shi, 15amma in mace tana da dogon gashi, ai, daraja ce a gare ta. Gama an ba ta dogon gashi saboda rufe kanta ne. 16In akwai mai gardama da wannan, to, mu dai ba mu da wata al’ada, haka ma ikkilisiyoyin Allah.
Cimar Ubangiji
17Game da umarnan nan dai, ban yaba muku ba, domin taruwarku ba ta kirki ba ce, ɓarna ce. 18Da farko dai, na ji cewa sa’ad da kuka taru a matsayin ikkilisiya, akwai tsattsaguwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen. 19Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku. 20Sa’ad da kuka taru, ba Cimar Ubangiji kuke ci ba, 21gama yayinda kuke ci, kowa yakan ci gaba ba tare da jiran wani ba. Wani yă zauna da yunwa, wani kuma yă bugu. 22Kai, ba ku da gidajen da za ku ci ku sha ne? Ko dai kun rena ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma wulaƙanta waɗanda ba su da kome? Me zan ce muku? In yabe ku ne game da wannan? A’a, ko kaɗan!
Cimar Ubangiji
23Gama abin da na karɓa daga wurin Ubangiji shi ne nake ba ku. Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki burodi, 24bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake dominku, ku yi wannan don tunawa da ni.” 25Haka kuma bayan cimar, ya ɗauki kwaf, yana cewa, “Wannan kwaf ne sabon alkawari a jinina; ku yi wannan, a duk sa’ad da kuke sha, don tunawa da ni.” 26Gama a duk sa’ad da kuke cin wannan burodi, kuke kuma sha daga wannan kwaf, kuna shelar mutuwar Ubangiji ne har yă dawo.
27Saboda haka, duk wanda ya ci burodin ko ya sha daga kwaf na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulaƙanta jiki da jinin Ubangiji ke nan. 28Dole kowa yă bincike kansa kafin yă ci burodin yă kuma sha daga kwaf ɗin. 29Gama duk wanda ya ci ya kuma sha ba tare da fahimtar jikin Ubangiji ba, ya ci ya kuma sha wa kansa hukunci ne. 30Shi ya sa da yawa a cikinku ba su da ƙarfi, suna kuma da rashin lafiya, waɗansunku kuma sun riga sun yi barci. 31Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za mu shiga irin hukuncin nan ba. 32Duk da haka sa’ad da Ubangiji ya hukunta mu, ana yin mana horo ne don kada a ƙarshe a hallaka mu tare da duniya.
33Saboda haka ’yan’uwana, sa’ad da kuka taru don ci, ku jira juna. 34In wani yana jin yunwa, sai yă ci abinci a gida, saboda in kuka taru kada yă jawo hukunci.
Sa’ad da na zo kuma zan ba da ƙarin umarnai.