2 Corintios 9 – NVI & HCB

Nueva Versión Internacional

2 Corintios 9:1-15

1No hace falta que les escriba acerca de esta ayuda para los creyentes, 2porque conozco la buena disposición que ustedes tienen. Esto lo he comentado con orgullo entre los macedonios, les dije que desde el año pasado ustedes, los de Acaya, estaban preparados para dar. El entusiasmo de ustedes ha servido de estímulo a la mayoría de ellos. 3Con todo, les envío a estos hermanos para que en este asunto no resulte vano nuestro orgullo por ustedes, sino que estén preparados, como ya he dicho que lo estarían, 4no sea que algunos macedonios vayan conmigo y los encuentren desprevenidos. En ese caso nosotros —por no decir nada de ustedes—, nos avergonzaríamos por haber estado tan seguros. 5Así que me pareció necesario rogar a estos hermanos que se adelantaran a visitarlos y completaran los preparativos para esa ofrenda generosa que ustedes habían prometido. Entonces estará lista como un acto de generosidad9:5 un acto de generosidad. Lit. una bendición. y no como una imposición nuestra.

Sembrar con generosidad

6Recuerden esto: El que siembra escasamente, escasamente cosechará, y el que siembra en abundancia, en abundancia cosechará.9:6 siembra … cosechará. Lit. siembra en bendición, en bendición cosechará. 7Cada uno debe dar según lo que haya decidido en su corazón, no de mala gana ni por obligación, porque Dios ama al que da con alegría. 8Y Dios puede hacer que toda gracia abunde para ustedes, de manera que siempre, en toda circunstancia, tengan todo lo necesario y toda buena obra abunde en ustedes. 9Como está escrito:

«Repartió sus bienes entre los pobres;

su justicia permanece para siempre».9:9 Sal 112:9.

10El que le suple semilla al que siembra también le suplirá pan para que coma, aumentará los cultivos y hará que ustedes produzcan una abundante cosecha de justicia. 11Ustedes serán enriquecidos en todo sentido para que en toda ocasión puedan ser generosos, y para que por medio de nosotros la generosidad de ustedes resulte en acciones de gracias a Dios.

12Esta ayuda, que es un servicio sagrado, no solo suple las necesidades de los creyentes, sino que también redunda en abundantes acciones de gracias a Dios. 13En efecto, al recibir esta demostración de servicio, ellos alabarán a Dios por la obediencia con que ustedes acompañan la confesión del evangelio de Cristo y por su generosa solidaridad con ellos y con todos. 14Además, en las oraciones de ellos por ustedes, expresarán el afecto que les tienen por la sobreabundante gracia que ustedes han recibido de Dios. 15¡Gracias a Dios por su don indescriptible!

Hausa Contemporary Bible

2 Korintiyawa 9:1-15

1Babu wata bukata in rubuta muku game da hidiman nan ga tsarkaka. 2Gama na san aniyarku na yin taimako, ina kuma taƙama a kan wannan ga Makidoniyawa, ina faɗin musu cewa tun bara, ku da kuke a Akayya a shirye kuke ku bayar. Ƙoƙarinku kuwa ya zuga yawancinsu ga aiki. 3Amma ina aika ’yan’uwan nan don kada taƙamar da muke yi da ku, a kan wannan al’amari ta zama a banza, sai dai domin yă zama kuna nan a shirye, kamar yadda na faɗa za ku kasance. 4Gama in waɗansu mutanen Makidoniya sun zo tare da ni, suka tarar ba a shirye kuke ba, kunya ta ishe mu, balle fa ku, saboda amincewa da muke yi da ku. 5Saboda haka, na ga ya dace in roƙi ’yan’uwan nan su ziyarce ku kafin lokacin, su kuma gama shirye-shirye saboda bayarwa ta yardar ran da kuka yi alkawari. Ta haka bayarwar za tă zama a shirye, ta yardar rai ba ta dole ba.

Shukin yardar rai

6Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace. 7Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai. 8Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki. 9Kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Ya ba gajiyayyu hannu sake,

ayyukansa na alheri madawwama ne.”9.9 Zab 112.9

10To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa. 11Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.

12Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah. 13Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na’am da bisharar Kiristi, saboda kuma gudummawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake. 14A cikin addu’arsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku. 15Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!